An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade
Published: 21st, November 2025 GMT
Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku.
Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Bright Edafe, ya ce ’yan sanda sun samu ƙorafi a kan faston bisa zargin lalata, fyade da cin zarafi.
Ya ce a ranar 17 ga watan Nuwamba, an kama wanda ake zargi a harabar cocinsa.
Edafe ya ce bincike ya nuna faston ya yi amfani da mu’ujiza ta karya wajen jawo mambobin cocin masu rangwamen gata zuwa ofishin cocinsa, yana tilasta musu su yi imani cewa idan bai yi jima’i da su ba, ba za su sami ’yanci ba.
Ya ƙara da cewa bincike ya tabbatar da cewa faston ya yi lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne, inda ya ce wacce ake zargin ya yi wa fyadeb ta ƙarshe shekararta 17.
Edafe ya ce wanda ake zargi yana tsare a hannun ’yan sanda yayin da bincike ke ci gaba da gudana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fyade
এছাড়াও পড়ুন:
Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba
Tsohon zakaran damben duniya a ajin masu nauyi, Anthony Joshua, zai fafata da tauraron YouTube, Jake Paul, a wani damben ƙwararru da za a yi a watan Disamba mai zuwa.
Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 36, wanda ya lashe kambun duniya ajin masu nauyi sau biyu, zai kara da Paul a cibiyar Kaseya Center da ke Miami.
’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar NajeriyaAna sa ran za a watsa damben kai tsaye a tashar Netflix a ranar 19 ga Disamba. Wadda za ta kasance fafatawa mai turmi takwas, kowanne na mintuna uku.
Joshua, wanda ya yi fafatawa uku a baya da nauyin sama da kilogram 113, yanzu dole ne ya rage nauyinsa zuwa ƙasa da kilogram 111.
Sannan dukkan abokan karawar za su saka safar hannu matsakaita, kamar yadda hukumar shirya gasar ta tanada.
Yanzu haka dai ana jiran samun tabbacin Joshua kan amincewa da wannan damben ko akasin haka, sai dai wasu rahotannin daga jaridar Sky Sports na nuna alamun tuni ya amince da tayin.