Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
Published: 20th, November 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata.
Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba.
Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan AmurkaLamarin ya faru kasa da sa’o’i 24 bayan mummunan harin da aka kai coci a Eruku, Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar, inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutum 30.
Majiyoyin al’umma sun ce an fara yin garkuwa da mutane huɗu, ciki har da ɗan sa-kai, a cikin waɗannan hare-haren.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce maharan daga baya sun kashe manoman shinkafa biyu tare da jikkata wani mutum na uku wanda aka ce ɗan sa-kai ne.
A halin yanzu, gwamnati ta ce ta ɗauki matakan tsaro na musamman a makarantu, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinta na tabbatar da kariya ga ɗalibai.
Matakan dai sun shafi makarantu a ƙananan hukumomin Ifelodun, Ekiti, Irepodun, Isin, da Oke Ero.
Gwamnatin ta ce wannan mataki ya nuna ƙudurinta na dakile ayyukan masu garkuwa da mutane waɗanda za su iya amfani da ɗalibai a matsayin garkuwa daga matsin lambar da suke fuskanta.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi da Ci gaban Ɗan Adam na jihar, Dr Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce matakan sun shafi makarantun kwana a Irepodun.
Sanarwar ta ƙara da cewa matakin zai ci gaba da kasancewa a yankunan har sai an samu cikakken tabbacin tsaro kafin a dawo da harkokin yau da kullum.
A ranar Litinin, ’yan bindiga sun kai hari a makarantar GGCSS Maga, Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu ta Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da ɗalibai 25.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwara Rufe Makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
Harin Isra’ila ya kashe mutum 15 a sansanin ‘yan gugun hijira na Falasdinawa a Lebanon
Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon.
An kuma kwantar da adadi mai yawa na mutane a asibitoci a birnin Sidon bayan harin na Ain al-Hilweh da ke can ranar Talata, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon (NNA).
Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin, kan abin suka kira, membobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a sansanin.
Saidai kungiyar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne.
https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=falseShare
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: An Bayyana Taron Gundumomin Dake Gabar Ruwan ” Caspian” Da Cewa Yana Bunaksa Alakar Kasashen Yankin November 18, 2025 Nijar: An Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyin Agaji Da Dama November 18, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Sahayoniya A Garin Bint-Jubail November 18, 2025 Brazil: Al’ummun Yankunan Karkara Na Amazon Sun Yi Gangami A Wurin Taron MDD Akan Muhalli November 18, 2025 Sojojin Najeriya Sun Karyata Cewa “ISWAP” Ta Kashe Wani Babban Jami’i Mai Mukamin Birgediya Janar November 18, 2025 Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi November 18, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza November 18, 2025 Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza November 18, 2025 Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza November 18, 2025 Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci