Aminiya:
2025-09-20@23:28:27 GMT

NAF ta hallaka Boko Haram 32 a Borno

Published: 21st, September 2025 GMT

Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta kashe ’yan ta’addan Boko Haram 32, a wani farmaki da ta kai garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno.

Rahoton ya bayyana cewa farmakin ya auku ne a ranar 18 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10:15 na safe.

Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Wannan na zuwa ne bayan ’yan ta’addan sun kai hari hedikwatar ’yan sanda da ke Banki.

A lokacin kai farmaki , sojoji biyu sun rasa rayukansu, haka kuma wani ƙaramin yaro mai shekara tara, Ismail Abubakar, ya rasu.

Har ila yau, maharan sun ƙone motocin soja uku.

Bayan kai harin, sojin sama na Operation Had6in Kai sun tura jirgin A-29 Super Tucano wanda ya yi wa ’yan ta’addan ruwan wuta.

Wannan ya janyo mahara 32 sun mutu sakamakon ɓarin wuta da suka sha.

An kwashe gawar sojojin zuwa Maiduguri, yayin da aka miƙa wa iyayen yaron gawarsa domin yi masa sutura.

Daga ƙarshe, an ƙara tura jami’an tsaro zuwa Banki domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram Farmaki hari

এছাড়াও পড়ুন:

Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar

Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita.

An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta zuwa ƙetare.

’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa

Munduwar mai ɗauke da ado na musamman, na da matuƙar daraja tun zamanin Fir’aunan, yayin da ake danganta ta da tsofaffin gumakan da aka yi bautar su a can baya, sannan an ce tana da ƙarfin warkarwa.

Munduwar na cikin jerin kayayyakin tarihin da ake shirin zuwa da su wani gagarumin taron baje-kolin kayayyakin tarihi a Italiya da za a fara gudanarwa a watan gobe.

Tuni aka kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike kan sauran kayayyakin tarihin da ake da su a ƙasar domin tabbatar da cewa, suna nan daram.

Gidan tarihi na Masar shi ne mafi daɗewa a yanƙin Gabas ta Tsakiya, kuma yana ɗauke da kayayyaki daban-daban har guda dubu 170.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Ta’addan Lakurawa Sun Sake Zama Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Turmutsitsin Shiga Kwale-kwale
  • Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina
  • Bayan biyan N50m ma’aurata da ’yarsu su da aka yi garkuwa da su a Katsina
  • Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani
  • Wata mata ta ƙone fuskar ’yar mijinta da tafasasshen man girki a Borno
  • Benfica ta naɗa Jose Mourinho sabon kociyanta
  • Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar
  • Gwamnatin Kano Ta Aika Dalibai 588 Zuwa Jihohin Arewa 13 A Karkashin Shirin Musanya
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda