Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma
Published: 21st, November 2025 GMT
Shugaban Cocin Katolika na Duniya, Fafaroma Leo XIV, ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Babban limamin, ya bayyana cewa duk da cewa akwai damuwa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, amma babu wani mabiyi na kowanne addini da matsalar ta ƙyale.
Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara a 2027 — NNPP Za a aurar da marayu 200 a Zamfara“Matsalar tsaron da ake fuskanta a Nijeriya ba Kiristoci kaɗai ta shafa ba, domin ta shafi Musulmi da sauran al’ummomi baki ɗaya,” in ji shi.
Fafaroman ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a lokacin da yake barin gidansa na Castel Gandolfo a Vatican, inda aka tambaye shi game da tsaron Kiristocin Najeriya, musamman yadda kasashen Yamma ke nuna damuwa.
Ya ce tashin hankalin kasar ya samo asali ne daga ta’addanci, matsin tattalin arziki da kuma rikice-rikicen mallakar ƙasa, ba addini kaɗai ba.
“A wasu yankuna na Najeriya, lallai Kiristoci na cikin haɗari; amma haka lamarin yake ga kowa a ƙasar gaba ɗaya. Ana kashe Kiristoci da Musulmi,” in ji shi, a zantawa da EWTN News.
Sai dai ya akwai buƙatar gwamnatin Najeriya da sauran al’ummomin ƙasar su haɗa kai wajen inganta ’yancin addini na gaskiya, domin kawo ƙarshen tashin hankalin da ake fuskanta
Aminiya ta ruwaito cewa furucin Fafaroman na zuwa ne bayan matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka kwanan nan na sanya Najeriya cikin jerin Kasashe Masu Fuskantar Barazana saboda zargin take haƙƙin ’yancin addini.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan kiyashi, tana mai jaddada cewa irin wannan bayani ba ya nuna haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙasar.
Haka zalika, ko a watan Satumba da ya gabata, Sakataren Gwamnatin Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya bayyana matsalar tsaron Najeriya a matsayin rikici na zamantakewa, musamman tsakanin makiyaya da manoma, ba rikicin addini ba kamar yadda wasu suke ɗauka.
A ranar Laraba, Mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawaga zuwa Amurka domin musanta zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar.
Tawagar ta gana da Riley Moore, wakilin da Trump ya tura binciko lamarin, inda suka yi tattaunawa mai zurfi game da gaskiyar halin da ake ciki a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fafaroma Leo XIV Najeriya matsalar tsaron
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka
Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare.
Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano“Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son amfani da labaran ƙasashen waje kai hare-hare kan wuraren da ba su da kariya kaimi,” in ji Akume a ranar Laraba.
Yayin da yake magana kan yadda ta’addanci, hare-haren ’yan bindiga da matsalolin tsaro ke ci gaba da sauyawa a ƙasar, Sakataren Gwamnatin ya ƙara da cewa: “Kafin waɗannan kalaman, an riga an raunana ƙungiyoyin ta’addanci sosai, kuma sun rage kai kananan hare-haren daji. Wannan dawowa ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa, ba wai Magana kawai ba, tsakanin Najeriya da Amurka.”
Trump, a jerin sakonnin da ya wallafa a shafin X tsakanin 30 ga watan Oktoba da 1 ga Nuwamba, 2025, ya ayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa mai Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Shugaban Amurka ya yi gargadin cewa zai iya tura sojojin Amurka zuwa Najeriya idan kisan da ake zargin bai tsaya ba.
Ya ce tuni ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta kasar da ta fara shirin yiwuwar daukar matakin soja idan tashin hankali ya ci gaba.
Trump ya kuma yi barazanar dakatar da dukkan taimakon Amurka ga Najeriya idan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kasa magance abin da ya kira zaluntar Kiristoci.
A cikin jawabin da SGF ya yi a ranar Laraba, ya ce an riga an raunana cibiyoyin ta’addanci sosai kuma sun rage zuwa kananan hare-haren daji kafin waɗannan kalaman.
“Wasu ƙungiyoyi yanzu suna ƙoƙarin amfani da waɗannan kalaman don samun suna,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa a cikin makon nan ne dai wasu ’yan bindiga suka sace dalibai 25 a makarantar sakandaren kwana ta GCGSS Maga da ke jihar Kebbi.
Kazalika, a cikin makon kuma ta wasu maharani sun farmaki wasu masu ibada a wani coci da ke Eruku a jihar Kwara.