Kakakin Rundunar ‘IRGC’: Yakin Kwanaki 12 Ya Nuna Karfin Kariyar Makaman Masu Linzamin Iran
Published: 21st, November 2025 GMT
Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Yaƙin kwanaki 12 ya nuna ƙarfin kariyar makamai masu linzamin Iran
Kakakin Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya bayyana cewa: Yakin kwanaki 12 ya nuna ainihin ƙarfin makamai masu linzami na Iran, kuma Amurkawa sun fahimci cewa, fuskantar makamai masu linzami na ballistic na Iran ba aiki ne mai sauƙi ba.
Da yake jawabi a taron “Masu Zaman Lafiya Don ‘Yantar da Kai”, Brigadier Janar Na’ini ya ƙara da cewa: “Wannan yaƙin shi ne mafi rikitarwa a duniya, kuma kuskuren lissafin makiya na ɓangarorin karfin Iran da dogaro da kayayyakin kariya da ta mallaka shine babban abin da ya jawo karyewar zuciyarsu a yakin.”
Ya ci gaba da cewa: “Maƙiya sun tabbatar da cewa: Wannan yaƙin zai samar da sakamako bisa ga kimantawarsu. Dabarun aiki na wannan yaƙin shine don kai hari mai sauri kan manyan jami’an kwamandan yaƙin Iran don hana Iran ikon daukan matakin mayar da martini a kan lokaci.” A cikin wadannan kwamandan yaƙin akwai manyan mutane huɗu: Brigadier Janar Rashid, Brigadier Janar Baqiri, Brigadier Janar Salami, da Brigadier Janar Hajizadeh. Maƙiya sun kiyasta cewa ta hanyar kai hari ga waɗannan mutane huɗu, sojojin ƙasar za su gurgunta kuma tsaronta zai ruguje, wanda zai jawo yaƙin cikin gida a Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Wasu Kasashe Bakwai Sun Mayar Da Martani Kan Hudurin IAEA Kan Kasar Iran November 21, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Kiran Da A Sanya Isra’ila Cikin Jerin Masu Aikata Abin Kunya Saboda Kashe Yara November 21, 2025 Tarayyar Turai Ta Kakaba Takunkumi Kan Dan Uwan Kwamandan Rapid Support Forces Ta Sudan November 21, 2025 Iran Tana Cikin kasashe 10 Na Farko Da Su Ka Fi Yawan Wuraren Tarihi November 20, 2025 Nigeria:Kotu Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada November 20, 2025 Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro November 20, 2025 Hizbullah: Ba Za Mu Taba Ajiye Makamanmu Ba November 20, 2025 Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla November 20, 2025 Hukumar Kula Da Jiragen Sama Ta Najeriya Ta ci Tarar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar November 20, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Kara Dagulewar Al’amura Bayan Harin Isra’ila A Gaza November 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Brigadier Janar
এছাড়াও পড়ুন:
Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF
Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a ta’asar da aka aikata a lokacin harin da aka kai a yankin Darfur na kasar Sudan.
An samu Kushayb da laifuka 27 da suka hada da laifukan yaki da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan kai, azabtarwa, fyade, da dai sauran manyan laifuka. Shari’ar dai ita ce shari’ar farko da aka shigar a gaban kotun ICC dangane da yakin Darfur.
A farkon wannan watan ne kotun ta ICC ta samu kara da ke da alaka da ta’addancin da aka yi a yankin Darfur a lokacin rikicin 2003-2004. An samu Kushayb da laifin bayar da umarnin kisa ga jama’a tare da kashe fursunoni biyu da gatari da kansa.
Lauya mai gabatar da kara Julian Nichols, yana magana a yayin zaman yanke hukunci na musamman, inda ya fallasa tare da kuma caccakar Kushayb a matsayin mai kisan kai da gatari. Ya ce Kushayb da kansa ya yi amfani da gatari ya kashe mutane biyu kuma ya kasance a sahun gaba wajen cin zarafin da aka yi a yankin Darfur fiye da shekaru 20 da suka gabata.
Mai gabatar da kara ya jaddada girman laifuffukan, yana mai nuni da irin rawar da Kushayb ya taka a ta’asar da aka aikata a farkon shekarun 2000 a matsayin shaida cewa ya kamata a yanke masa hukunci mafi tsanani a kotun.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci