Kungiyar Hamas Ta Yi Kiran Da A Sanya Isra’ila Cikin Jerin Masu Aikata Abin Kunya Saboda Kashe Yara
Published: 21st, November 2025 GMT
Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira da a saka gwamnatin mamayar Isra’ila cikin jerin ‘masu aikata abin kunya’ saboda take hakkin yara
Majalisar Dinkin Duniya ta yi bikin Ranar Yara ta Duniya a ranar 20 ga Nuwamba, yayin da yaran Falasdinawa ke fuskantar mummunan yanayi sakamakon laifukan Yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, wanda ya lalata tushen rayuwa, gami da abinci, magani, ruwa mai tsafta, kiwon lafiya, ilimi, da tallafin tunani.
A Ranar Yara ta Duniya, Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: Bikin na wannan shekarar ya zo ne yayin da yakin shekaru biyu na kisan kare dangi da yunwa a yankin Gaza ya bar yara sama da 20,000 suka mutu, dubbai kuma suka bata a karkashin baraguzan gine-gine, da kuma yara sama da 30,000 wadanda suka rasa iyaye. Dubban mutane sun ji rauni kuma suna rashin lafiya, suna bukatar jinyar gaggawa a kasashen waje.
A yankin yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, wahalar da yara ke sha ta ci gaba saboda kisan gilla da gangan, wariyar al’umma, rushe gidaje, rufe hanyoyi da makarantu, tilastawa mutane yin gudun hijira, hana ilimi, kai hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa. Adadin yara da suka yi shahada a Yammacin Kogin Jordan kadai ya wuce 300 a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tarayyar Turai Ta Kakaba Takunkumi Kan Dan Uwan Kwamandan Rapid Support Forces Ta Sudan November 21, 2025 Iran Tana Cikin kasashe 10 Na Farko Da Su Ka Fi Yawan Wuraren Tarihi November 20, 2025 Nigeria:Kotu Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada November 20, 2025 Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro November 20, 2025 Hizbullah: Ba Za Mu Taba Ajiye Makamanmu Ba November 20, 2025 Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla November 20, 2025 Hukumar Kula Da Jiragen Sama Ta Najeriya Ta ci Tarar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar November 20, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Kara Dagulewar Al’amura Bayan Harin Isra’ila A Gaza November 20, 2025 Labanon Ta Bukaci Gudanar Da Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Cikin Gaggawa November 20, 2025 Achraf Hakimi Ya Zama Gwarzon Wasan Kwallon Kafar Afirka Na Shekara Ta 2025 November 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.
Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba.
NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’ummaWannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan