Leadership News Hausa:
2025-10-13@17:54:15 GMT

Ya Kamata Karancin Malamai A Duniya Ya Zama Darasi Ga Nijeriya

Published: 26th, September 2025 GMT

Ya Kamata Karancin Malamai A Duniya Ya Zama Darasi Ga Nijeriya

Alkaluma sun nuna cewa, a yankin Arewa Maso Gabas, kalubalen rashin tsaro ya dakatar da akalla yara miliyan 20, daga zuwa Makarantar Boko tare tare da kuma yadda hare-haren, suka lalata Makarantun Boko da dama da ke a yankin, wanda hakan ya janyo gagarumar tazara a tsakain yankin da kuma Kudancin kasar, tare da kuma wasu lamuran da suka shafi al’ada a fadin kasar, wanda ya kai kaso 15.

Misali, yankin Arewa Maso Gabas, kacal irin wadannan hare-haren babu kakkautawa da mahara ke kai wa ya dakatar da yara miliyan biyu daga zuwa Makaranta inda hare-haren suka lalata gine-genen Makarantu da dama hakan kuma ya kara haifar da karancin Malaman.

Malamai 915,913 kacal ne a matakin karatun Firamare ke koyar da dalibai miliyan 31.7 wanda hakan ke ci gaba haifarwa da bangaren koyarwa, nakasu.

A nan za a iya cewa, matakan Makarantun Firamare, ba fuskanta karancin Makamai sama da 165,000 wanda musamman lamarin, ya fi yin kamari a yankunan Karkara tare da kuma janyo babban gibi a bangaren samar da ingantaccen ilimi.

Kazalika, a cikin kasafin kudi na shekara-shekara, Gwamnati na kebewa fannin ilimi kaso biyar zuwa kaso tara ne, wanda wannan kaso, ya gaza da shawarar da UNESCO ta bayar na a warewa fannin kaso daga 15 zuwa 20, inda hakan ya haifar da samun gazawar kara daukar Malaman aiki.

Wannan karancin na daukar Malaman, ya nuna karara na irin gadawar Gwamnatin, inda a gefe daya kuma ake biyan Malaman can Albashi kalilan da jinkirin biyansu da rashin samar masu da kyakyawan yanayi na koyarwa, wanda hakan ke tilasata su, yin kaura zuwa wasu kasashen duniya inda za a biya su da gwabi.

A kwanukan baya, an samar da wasu shirye-shiye misali, a jihohi kamar irinsu, Anambra da Enugu, ba daukar Malamai 5,000 aiki tare da kuma ware kaso 33 a cikin kasafin kudi na 2025, amma batun wanzar da lamarin a nan ne, natsalar ta ke.

A gefe daya kuma Arewacin kasar na ci gaba da fuskantsr kalubalen tsarin Almajiri da ke da watan gaririya a kwararo-kwararo, ba bu ilimin Boko.

Da farko a nan, muna bayar da shawara da a kaddamar da daukar Malamai a daukacin fadin kasar, musamman kwararru.

Za a iya ci gaba da fuskantar jahilci a kasar inda hakan kuma zai safi fannin tattalin arziki tare da rashin samun daidaito, matkar, ba a dauki matakan gaggawa na magance wadannan matsalolin ba.

Ya zama wajibi jihohin kasar nan su yi hadaka da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta rungumar tsarin zamani irin na kasar Rwanda na magance matsalar da kasar ta Rwanda ta fukasta na karancin Malamai a baya wanda hakan ya bai wa kasar damar kai wa kso 98.

Irin wannan tsarin zai bai wa Nijeriya damar ciki gibin da ake da shi na dalibai guda 165,000, tare da kuma ingnata alawus-alawsu din Malaman da ke koyarwa a yankunan karkara.

Kazalika, ya kamata a kara inganta jin dadi da walwalar Malaman tare da kuma basu dauki, ga bangaren kula da lafiyarsu.

Hukumar ta UNESCO, ta kuma bayar da shawara da a rinka bai wa Malaman horo da samar masu da kayan aiki, domin a rage yawan yadda suke fita ketare, neman aikin yi.

Hakazalika, Hukumar da ke Kula da Yiwa Malaman Makaranta Rijista ta Kasa wato TRCN, ta mayar da hankali wajen ganin ana daukar kwararrun Malamai aiki.

Akwai bukatar a samar da sauye-sauye tare da kara zuba kudade a fannin ilimi wanda zai kai ga akalla an zuba kaso 15 a cikin kasafin kudi na kasa, kamar yadda Gwamnati ta yi alkawri a 2021, sai dai, duk ba a cika wannan alkawarin ba.

Ya kamata a samar da shirye-shiyen magance matsalar yaran da ba sa zuwa Makaranta kamar yadda Bankin Dniya yak ebe kudi har dala miliyan 700, domin tallafawa karatun ‘ya’ya mata

Bugu da kari, ya kamata a yi koyi da tsarin Malamai irin na kasar Finland ko kuma na kasar Singapore wanda ake daukar Malaman bisa cancanta.

Wannan Jaridar ta mayar da hankali wajen ganin ana gudanar da shugabanci na gari, inda take shawartar Gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamnatocin jihohi da kuma ‘Yan Majalisar Kasar da su dauki matakan gaggawa, domin magance barazanar karancin Malamai a kasar.

Matsalar ta karancin Malaman da duniya ke fuskanta, ta zama tamkar wata izina ce, ga kasar nan, domin kasar ta shi tsaye, ta magance wannan barazanar.

Baya ga kula da Malaman ya kuma kamata a mayar da hankali a kan makomar daliban, musamman domin kar batun na cimma muradun karni na SDG 4, ya zama tamkar tatsuniya.

Batun kawo uzuri kan wannan barazanar abu ne wanda za a iya cewa, bai ma wani taso ba, domin dole ne a fara daukar matakai na gaba, idan kuma bah aka ba, yaran masu tasowa, za su kasance, a cikin duhun jahilici.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: tare da kuma wanda hakan

এছাড়াও পড়ুন:

Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta

Jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, kuma rahotanni masu karo da juna suna cewa an kashe shugaban Taliban na Pakistan

Kafofin yada labaran Afghanistan sun yi ikirarin cewa: Sojojin Pakistan ne ke da alhakin harin da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a yammacin ranar Alhamis.

Tashar Talabijin ta Tolo News da Khabar Online Afganistan sun ruwaito cewa: Sojojin Pakistan sun dauki alhakin hare-haren da aka kai cikin daren jiya a Kabul.

Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya rubuta a dandalin X a yammacin ranar Alhamis cewa: An ji karar fashewar wani abu a birnin Kabul.

Ya kara da cewa: “Babu wata damuwa, lamarin dai kamar yadda aka saba, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kawo yanzu ba a samu hasarar rayuka ba.”

Majiyar leken asirin Afganistan ta shaidawa Al-Araby Al-Jadeed cewa: Shugaban Taliban na Pakistan kuma wani babban kwamandan kungiyar ya tsallake rijiya da baya a harin da Pakistan ta kai kan Kabul.

A halin da ake ciki, wasu kafafen yada labaran Afghanistan sun sanar a cikin wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba, y ace: An kashe Mufti Noor Wali Mehsud shugaban Taliban na Pakistan a wani hari da aka kai ta sama a Kabul a daren yau.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka  Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Mohajirani: Iran na goyon bayan shawarar Falastinawa kan batun dakatar da bude wuta October 10, 2025 Khalil al-Hayya: Mun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta  dindindin October 10, 2025 Ministan mai na Nijar ya gana da Jakadan Iran  a Yamai October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana
  • Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
  • Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
  • Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida