An kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na Tabar Wiwi
Published: 19th, November 2025 GMT
Rahotanni na cewa an kama wani mutum, Onun Ikoli, tare da matarsa, Itam Onun, bisa zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi a Jihar Kuros Riba.
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ce ta cafke ma’auratan a ranar Talata a ƙaramar hukumar Yakurr a jihar ta Kuros Riba.
Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a JigawaKwamandan NDLEA na jihar, John Anteyi, yayin zantawarsa da Aminiya a Kalaba, ya ce ababen zargin sun yi iƙirarin cewa tabar wiwin wadda nauyinta ya kai tan 4.
Ma’auratan sun shaida wa ’yan sandan cewa ba su da masaniyar harkar da mutumin yake yi wanda ba a samu nasarar cafke shi ba a gidan.
Itam Onun, mai kimanin shekara 52, ta musanta cewa tabar wiwin ta su ce, inda ta ce: “Ba mu san komai ba. Shi ne mai gidan.
“Mu dai haya muka karɓa a wurinsa kan naira dubu 50, ba mu san irin wannan harkar yake yi ba. Shi ya kawo kayansa ya ajiye amma ga shi an kama mu kan wannan zargin.”
Kwamandan ya ce kawo yanzu dai hukumar tana ci gaba da bincike domin gano ainihin mallakin kayan.
Kazalika, Anteyi ya jaddada cewa wannan samame na cikin yunƙurin da shugaban hukumar NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ke jagoranta na yaƙar miyagun ƙwayoyi da masu safarar su a fadin ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tabar wiwi
এছাড়াও পড়ুন:
An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa.
Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a NajeriyaDSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012.
Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan sanda na Unguwa Uku, da wasu wurare.
Mutane da dama sun jikkata a yayin kai waɗannan hare-hare.
An kama Ismaila ne a ranar 31 ga watan Agustan 2017, a ƙauyen Tsamiyya Babba da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa, a Jihar Kano.
Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa dokar hana aikata ta’addanci ta 2013.
Shari’ar ta ɗauki lokaci saboda ɗaukaka ƙara da kuma tabbatar da bayanan da ya bayar da farko ba tursasa shi aka yi ba.
A ƙarshe, lauyoyin gwamnati sun kira shaidu biyar, ciki har da jami’an DSS da mutanen da harin ya shafa.
Da farko Ismaila, ya ƙi amincewa da laifin da ake tuhumarsa amma bayan gabatar da shaida na biyar, ya sauya maganarsa ya amsa laifin.
Lauyansa daga Hukumar LAC, P. B. Onijah, ya roƙi kotu ta yi masa sassauci, inda bayyana cewa Ismaila ya nuna nadama kuma bai son ɓata wa kotu lokaci.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Nwite ya yanke masa shekar 15 kan tuhumar farko da kuma shekaru 20 kan sauran kowace tuhuma uku.
Dukkanin hukuncin za su tafi a lokaci guda, kuma za su fara aiki tun daga ranar da aka kama shi a shekarar 2017.
Alƙalin ya umarci Hukumar Gyaran Hali ta tsare shi a gidan yari da Babban Kwamandan Hukumar ya zaɓa.
Bayan ya kammala zaman gidan yari, dole a yi masa horon gyaran hali da kawar da ra’ayin ƙiyayya kafin a sake mayar da shi cikin al’umma.