Aminiya:
2025-09-20@19:26:16 GMT

Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Published: 20th, September 2025 GMT

Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato.

Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar mota ta yanke sakamakon ambaliya.

Wata mata ta haifi ’ya’ya huɗu a Bauchi Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi

Yayin da yake tafiya, jirgin ya bugi wata ƙaramar gada ta nutse a ruwa, lamarin da ya jawo mutuwar mutum tara, yayin da wasu suka samu rauni.

Rahotanni sun ce ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba saboda ya ɗauki mutane fiye da kima.

Har yanzu hukumomin agajin gaggawa ba su fitar da wata sanarwa ba kan hatsarin.

A nasa martanin, Sanata Ibrahim Lamiɗo, Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga al’ummar yankin tare da kiran gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro da gyaran hanya tsakanin Sabon Birni da Goronyo.

Ya ce rashin tsaro da matsalar tituna na jefa mutanen yankin cikin hatsari, tare da jaddada cewa gwamnati na da alhakin kare rayukan jama’a da kuma inganta rayuwarsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hatsarin Jirgin Ruwa Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar mutuwar mutane 58 sanadiyyar kamuwa da cutar amai da gudawa (kwalara) inda ta gano sabbin masu dauke da cutar mutane 258, wanda aka samu a kananan hukumomi 14 cikin 20 na jihar.

Duk shugaban da bai yi aiki ba bai kamata a sake zaɓarsa ba — Jonathan An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Auwal Jatau ne ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da cutar kwalara na jiha, da kuma kwamitin kwararru kan yaki da cutar.

Jatau ya bukaci mambobin kwamitocin da su tunkari ayyukan da aka dora musu cikin kishi da kwarewa da kuma hanzari.

Mataimakin Gwamnan wanda shi ne shugaban kwamitin ya koka kan yadda cutar kwalara da ta sake barkewa, kuma tana ci gaba da janyo asarar rayuka, da kuma kawo cikas ga harkokin rayuwa da kuma kawo kalubalen ga tsarin kiwon lafiyar jihar.

Ya ce, cutar kwalara na daya daga cikin manyan cututtuka da ke barazana ga lafiyar al’umma, duk da kokarin da gwamnatin jihar da takwarorinta ke yi na shawo kan cutar.

Jatau ya bayyana cewa, kafa kwamitoci yana da mahimmanci wajen cimma manufofin da ake so.

“Ana iya yin rigakafin wadannan bullar cutar tare da daukar matakan da suka dace,, da kuma ci gaba da inganta tsaftar ruwan sha tsaftar muhalli, da tsaftar jiki.”

A kan haka ne ake sa ran kwamitin zai yi aiki tare da kungiyoyin hadin gwiwa don shawo kan matsalar.

Ya ce, Jihar Bauchi ta mayar da hankali kan barkewar cutar kwalara da kuma fitar da dabarun rigakafin cutar kwalara na dogon lokaci tare da tsare-tsare da tsare-tsare na kasa da kasa kan tsare-tsaren dakile cutar kwalara a Najeriya da yin rigakafi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi
  • ’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato
  • Ajali: Wasu Ƴan Ƙauye Sun Gujewa Ƴan Bindiga Sun Nutse A Ruwa
  • Miyetti Allah ta roki Gwamntin Kwara da ta sa baki kan rufe Kasuwar Kara da Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi
  • An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe
  • Fubara ya sauka a filin jirgin saman Fatakwal
  • Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi
  • Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato