Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara a 2027 — NNPP
Published: 20th, November 2025 GMT
Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a Kano har ma da matakin ƙasa “ta rasa shugabanci da tsari”, wanda hakan, a cewarsa, ya sa suke yawan neman kusanci da Kwankwaso.
A cewarsa, “Wannan mutanen APC ba su da ƙarfi, kuma a halin yanzu sun shiga ruɗani. Sun san cewa idan babu Kwankwaso, ba za su iya cin zaɓe a 2027 ba.
“Shi ya sa kullum sai ka ji suna cewa wai suna tattaunawa da shi wanda hakan ya nuna su ne buƙatar sa, a yayin shi kuma nasa hankalin ya karkata kan jin daɗin ’yan Najeriya.”
‘Sulhu a siyasa ba sabon abu ba ne’Sai dai Dungurawa ya bayyana ce tattaunawa da sulhu a siyasa ba sabon abu ba ne, yana mai jaddada cewa haɗuwar Kwankwaso da wasu manyan ‘yan siyasa da ake yi a bayan nan “ba wai wata yarjejeniya ce ta siyasa ba, sai dai haɗuwa ta ba-zata da ba ta haɗi da sha’anin siyasa”.
‘Jama’a ba su waye da NNPP ba a Zaɓen 2023’Yayin da yake amsa tambayar dalilin da NNPP ta samu kusan ƙuri’u 500,000 kacal a Kano a zaɓen 2023 duk kuwa iƙirarin shaharar Kwankwaso, Dungurawa ya ce ai a lokacin jam’iyyar “dududu ba ta wuce watanni bakwai da kafuwa ba.”
Ya ce, “Ko a 2023 tambarin jam’iyyar [NNPP] bai fito ba sosai a takardar zaɓen ba, sannan kuma mutane da dama ba su waye da jam’iyyar ba kasancewarta sabuwa ce a lokacin.
“Amma duk da haka mun samu kujeru a Kano, Jigawa, Taraba da Bauchi. Don haka zaɓen 2027 zai bambanta kwarai da abin da kuka gani.”
Game da shirye-shiryen tarukan jam’iyya masu zuwa, Dungurawa ya ce tsarin jam’iyyar ya bayyana cewa yawancin shugabannin jam’iyyar na yanzu za su ci gaba da riƙe muƙamansu.
Ya ce, “Dokokin jam’iyyar sun yarda shugabanni su yi wa’adi biyu muddin ba su fice daga jam’iyya ba, ko suka mutu ko kuma aka same su da laifi.”
Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da zaɓen cike gurbi a watan gobe domin maye gurbin kansiloli uku da suka rasu a kananan hukumomin Garin Malam, Dala da Doguwa.
Ya yabi Gwamna Abba kan kasafin kuɗin Kano na 2026Shugaban na NNPP ya kuma yaba wa ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2026 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar, yana mai cewa fifikon da aka ba bangaren ilimi da noma “abin yabawa ne”, tare da jinjina wa gwamnati kan “gyare-gyaren da ake gani da ido” a faɗin Jihar Kano.
Ya kuma soki tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yana zarginsa da “barin ilimi a baya, rashin tallafin karatu, da ƙin biyan haƙƙoƙin fansho.”
‘Ba mu damu da masu ficewa daga jam’iyyar ba’Dangane da batun sauyin sheƙa, Dungurawa ya ce ɗan majalisar tarayya ɗaya kacal ne ya fice daga cikin jami’yyar da kansa, sauran kuwa an dakatar da su ne tun kafin su fice.
Ya ce, “Ba damuwar mu ba ce. Jam’iyyar ba ta buƙatar mutane masu wuyar sha’ani. NNPP kamar ɗakin otel ne — akwai masu barin ɗaki na alfarma ‘royal suite’ su koma na gama-gari wato ‘standard room’, daga baya sai su gane banbancin.”
Dungurawa ya buƙaci jama’ar NNPP su ci gaba da zama tsintsiya maɗauri ɗaya, su kuma fara shiri domin NNPP ta ci gaba da cin gajiyar mulki a 2027.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hashimu Sulaiman Dungurawa Rabi u Musa Kwankwaso Dungurawa ya ce
এছাড়াও পড়ুন:
Yanzu-yanzu: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP
An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.
Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata.
Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban taronta na kasa da ya gudana a karshen mako ya kira taron gaggawa a yau Talata a hedikwatar Jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.