Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki a wat
Published: 25th, September 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025.
Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya.
Za a yi tantancewar ne ta hanyar tsarin amfani da kwamfuta mai suna Nigeria Education Repository and Databank (NERD), wanda aka ƙirƙiro domin adanawa da tabbatar da sahihancin takardun karatun ma’aikata.
A wannan tsari, babu wanda za a ɗauka aiki ko a tabbatar masa da muƙami sai an tabbatar da takardunsa ta hanyar National Credential Verification Service (NCVS).
Kowace takarda da aka tabbatar za a ba ta wata lamba ta musamman mai tsaro.
Jami’ai sun ce wannan mataki zai kare mutuncin ilimi a Najeriya, kodayake masana sun yi gargaɗin cewa wasu za su iya rasa ayyukansu.
A baya, an gano ’yan Najeriya da dama suna amfani da takardun bogi don samun aiki ko ƙarin matsayi a wajen aiki.
A shekarar 2024, gwamnati ta soke takardun shaidar kammala karatu sama da 22,000 daga jami’o’in bogi na Jamhuriyar Benin da Togo.
Haka kuma, gwamnati ta umarci cibiyoyi su riƙa gabatar da rahoton bin doka duk shekara domin tabbatar da tsauraran matakai.
Wannan zai sa ya zama da wuya a riƙa yin amfani da takardun ƙarya ba tare da an gano su ba.
Masana ilimi sun ce idan aka aiwatar da tsarin yadda ya kamata, zai dawo da mutuncin takardun shaidar kammala karatu na Najeriya a idon duniya, tare da bai wa ɗalibai na gari damar samun aiki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Takardun bogi Takardun Shaidar Kammala Karatu Tantancewa da takardun
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroYa ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.
ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.
A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.
Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.
Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.
Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.