Aminiya:
2025-11-21@21:21:30 GMT

Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya

Published: 22nd, November 2025 GMT

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya.

Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja.

Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 

Maharan sun sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar St.

Mary’s Catholic.

Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.

Harin ya auku ne bayan sace ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka a Ƙaramar Hukumar Maga, a Jihar Kebbi, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa, musamman a Arewa.

A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya nuna damuwarsa.

“Abin takaici ne sosai. Har yaushe za a ci gaba da rasa rayuka ba tare da an ɗauki matakin gaggawa ba?”

Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta ɗauki tsauraran matakai.

Ya kuma buƙaci ƙarin tsaro a makarantu domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ɗalibai hari yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama.

A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da aka kai musu mummunan hari suna tsaka da ibada a cocin.

Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai

Majiyoyi daga iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwar sun fara kiran ’yan uwan waɗanda aka sace ta hanyar amfani da wayoyinsu.

Sakataren cocin, Josiah Agbabiaka, ya ce tuni aka fara tuntubar wasu daga cikin dangin wadanda aka sace din.

Ya ce, “Gaskiya ne cewa ’yan bindigar sun fara kiran ’yan uwa ta amfani da wayoyin waɗanda aka sace don neman kudin fansa,” in ji Agbabiaka.
“Abin da aka shaida mana shi ne sun raba waɗanda aka sace gida-gida. Rukunin farko na mutane 11 an nemi su biya Naira miliyan 100 kowanne.”

Basaraken gargajiya na yankin, Olori Eta, Cif Olusegun Olukotun, wanda ’yan uwansa huɗu na cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa masu garkuwar suna kiran dangin wadanda aka sace daya bayan daya.

“’Yan bindigar sun fara kiran wasu suna neman Naira miliyan 100 kan kowanne mutum. Sun ce sun raba waɗanda aka sace gida-gida, kuma suna kiran danginsu,” in ji shi.

Olukotun ya ce yana cikin cocin tare da ’yan uwansa biyar lokacin harin, inda ya ce ya tsere ta taga yayin da sauran aka tafi da su.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sanda ta Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce rundunar ba ta samu wani rahoto a hukumance ba kan neman kudin fansar.

“Ba mu da masaniya kan wani neman kudin fansa ko tuntubar iyalan waɗanda aka sace,” in ji ta a ranar Alhamis.
“Dakarunmu na musamman tare da sojoji da sauran jami’an tsaro suna kan aiki don ceto waɗanda aka yi garkuwar da su.”

Ejire-Adeyemi ta ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adekimi Ojo, ya roƙi al’umma da iyalan waɗanda aka sace da su bayar da bayanan da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen aikin ceto mutanen kuma a kan lokaci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
  • Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 
  • ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja
  • ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • ’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Dalibai Mata 25 a Jihar Kebbi 
  • Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya