Aminiya:
2025-09-24@08:32:50 GMT

Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi

Published: 21st, September 2025 GMT

’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum.

Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja.

Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina

Maharan, sun kai harin ne a kan babur, inda suka buɗe wa ’yan sandan da ke bakin aiki wuce.

Wani matashi da ya zo wucewa ta wajen ya rasa ransa.

Bayan haka, maharan sun kwashe bindigogin jami’an sannan suka tsere.

Daga baya, da misalin ƙarfe 11 na safe, suka sake kai wani hari a shingen da ke kan hanyar Ilafin, Isanlu a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, inda suka kashe wasu ’yan sanda biyu na rundunar MOPOL 70.

Mutanen yankin sun ce wannan hari ya jefa su cikin tsoro, suna ganin cewa maharan na neman bindigogi ne domin su ci gaba da kai hare-hare.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, Dokta Joshua Dare, ya yi Allah-wadai da hare-haren.

Ya bayyana harin a matsayin barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

Ba wannan ne karo na farko da irin wannan hari ya auku ba.

A ranar 9 ga watan Satumba, an kashe jami’an tsaro guda biyar; ciki har da ’yan sanda uku da ’yan banga biyu, a wani hari  kwanton ɓauna da aka kai musu a yankin Egbe da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma.

Gwamnatin Jihar Kogi, a baya-bayan nan ta zargi wasu matasa da taimaka wa ’yan bindiga a yankin, inda ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP William Aya, bai ce komai game da sabon harin ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda hari Ƙaramar Hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Gwagwarmaya  Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza

Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan rundunar “Folcan”.

Kakakin sojan HKI ya bayyana cewa wanda aka kashe din shi ne Manjo Shahir Natna’il, sai kuma Midgal Haimik a wani fada da aka yi a arewacin Gaza.

 Wasu kafafen watsa labarun HKI sun ambata cewa mayakan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas sun yi wa sojoji kwanton bauna a wasu wurare biyu mabanbanta.

 A bisa kididdigar sojojin HKI adadin wadanda aka kashe zuwa yanzu a yakin Gaza, sun kai 911.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Yin Kiran A Bai Wa Falasdinawa Kasarsu September 23, 2025  HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi September 23, 2025   Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A  Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga  MDD” September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Kogi Na Cikin Fargaba Yayin Da Kogin Neja Da Benuwe Suka Tumfatsa
  • Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
  • ‘Yan Gwagwarmaya  Sun Kashe Sojojin Mamaya Biyu A Wani Kwanton Bauna A Arewacin Gaza
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • ’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi
  • NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda
  • Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
  • An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
  • Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja