Aminiya:
2025-11-21@05:47:59 GMT

Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi

Published: 21st, November 2025 GMT

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar.

Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace.

Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara

’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin.

A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda ya bayyana umarnin a cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis, ana sa ran Matawalle zai isa Birnin Kebbi da safiyar Juma’a.

“Yana da ƙwarewa sosai wajen fuskantar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga 2019 zuwa 2023,” in ji sanarwar.

“A ranar 26 ga watan Fabrairu, 2021, ’yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata 279 masu shekaru tsakanin 10 da 17 a makarantar kwana ta GGSSS Jangebe, Jihar Zamfara. ’Yan bindigar sun saki dukkan waɗanda suka yi garkuwar da su a ranar 2 ga watan Maris, 2021.”

Idan za a iya tunawa, Shugaba Tinubu ya dage tafiyarsa da aka tsara zuwa Johannesburg, Afirka ta Kudu, da Luanda a kasar Angola, domin ya jira ƙarin rahotannin tsaro kan satar daliban na Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a cocin Eruku da ke jihar Kwara.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi

Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya.

Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin.

Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji.

Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin hana su tafiya da yaran.

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas

A yayin ziyarar jaje da Gwamna Idris ya kai makarantar, bayan yanke ziyarar aiki da ya kai Abuja, ya ba wa iyayen ɗalibai tabbacin cewa gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su yi dukkan abin da zai yiwu wajen ceto yaran.

Kana ya jaddada cewa za su ci ga da ƙoƙari wajen ganin bayan ayyukan ta’addanci a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai
  • Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya
  • DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
  • Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi
  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin
  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi