Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
Published: 21st, November 2025 GMT
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja.
Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya.
DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna KebbiShugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba.
Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba.
Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya ce: “Arewa na fama da ƙalubalen ilimi kuma ba za mu bari miyagu su lalata ci gaban da ake samu ba.”
Ya bayyana damuwa kan yadda hare-hare ke ƙaruwa a makarantu yayin da gwamnatocin Arewa ke ƙoƙarin samar da ingantattun tsare-tsaren tsaro ga ɗalibai.
Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro da al’umma don ƙarfafa tsaro a unguwanni da makarantu, da kuma tattara bayanai masu muhimmanci.
A madadin gwamnonin, Gwamna Yahaya ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda aka sace da Gwamnatin Jihar Neja.
Ƙungiyar ta buƙaci a ɗauki matakin gaggawa don ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya da kuma hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Haka kuma, ta yaba wa jami’an tsaro da ke aikin ceto ɗaliban da malamai, inda ya roƙe su da su ƙara himma, tare da roƙon jama’a su ba da haɗin kai don samun nasarar ceto waɗanda lamarin ya shafa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamna Yahaya Gwamnonin Arewa Save Ɗalibai
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi.
Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa.
Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a KebbiAminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin shugaban makarantar da wani maigadi kana suka jikkatar da dama.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana tsananin damuwa kan harin, inda ta ce ta bai wa jami’an tsaro umarnin gano da ceto ɗaliban cikin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Muhammad Idris ya fitar, ya ce gwamnati za ta tabbata an kamo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.
Ya ƙara da cewa gwamnati na tare da iyaye da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa, tare da jaddada cewa za a yi duk wani abu mai yiyuwa domin ganin yaran sun koma gida cikin aminci.
Ita ma ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International, ta yi kakkausar suka kan sabon harin, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici wanda ta ce ya tabbatar da gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga.