Aminiya:
2025-11-20@14:25:59 GMT

Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanci

Published: 20th, November 2025 GMT

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa.

Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan su daga bangaren masu gabatar da ƙara.

Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas

Alkalin ya ce barazanar tashin hankali da Kanu ya yi a cikin jawabansa ta haifar da tsoro da damuwa a zukatan jama’a a yankin Kudu maso Gabas.

Justice Omotosho ya ƙara da cewa bisa hujjojin da masu gabatar da ƙara suka bayar, an tabbatar da abubuwan da suka hada da ta’addanci a cikin shaidun da aka gabatar a kan shi ta hanyar niyya da halayensa.

Alkalin ya lura cewa Kanu ya ki yak are kansa, yana mai cewa ya “gaza kuma da gangan ya ƙi bayar da wata hujja da za ta wanke shi” daga tuhumar da aka yi masa.

A halin yanzu dai kotun na ci gaba da yanke hukunci kan tuhumar ta’addanci da aka gabatar a kan Kanu.

Muna tafe da karin bayani…

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal

Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao.

Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu manyan gyare-gyare da ake yi wa filin, lamarin da ya tilasta wa Barcelona komawa wasu filayen waje domin buga wasanninta.

An kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na Tabar Wiwi Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba

Sai dai duk da cewa ba a kammala gyaran filin gaba ɗaya ba, an ba da damar komawa amfani da shi domin buga wasanni.

Yamal, mai shekara 18, ya buga wasa ɗaya ne kacal a Camp Nou kafin a rufe shi a watan Agusta 2023, inda a yanzu ya ce yana fatan farantawa dubban magoya baya kulob ɗin a sabon filin da aka sauyawa fasali.

A wani saƙo da ya wallafa a Instagram, Yamal ya saka hotonsa riƙe da bajon Barcelona tare da rubutun cewa Camp Nou shi ne wajen da za a rubuta tarihi.

A farkon watan Nuwamba an gudanar da gwajin farkon shigar tara a filin, inda aka bai wa magoya baya 23,000 damar shiga. Sai a yanzu da aka ƙara yawan kujeru domin ɗaukar ‘yan kallo har 45,401.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru
  • Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa kawai da kin jinin Iran
  • Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal
  • Kotu A Gabon Ta Yanke Hukuncin Dauri A Kurkuku Kan Jami’an Tsohuwar Gwamnatin Kasar
  • An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari
  • Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026
  • Gwamna Abba ya gabatar da kasafin 2026 na N1.36trn
  • Majalisa wakilai A Najeriya Ta Bukaci Gwamnati Ta Sake Dabarun Yaki Da Ta’addanci
  • Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS