2025-12-13@14:00:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2887

«Sansanin yan gudun hijira»:

    Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Hamas ta fadi cewa fashewar bama-bama da rushewar gidaje da mutuwar mutane da dama a daidai lokacin da ake tsananin ruwan sama da sanyi a yankin gaza ya kara tabbatar da kisan kiyashi isra’ila kan alummar Gaza, kuma ya kara tabbatar da gazawar tsarin duniya na daukar mataki don dakatar...
    Allah Ya yi wa Farfesa Adamu Baikie, wanda ya kasance Farfesa na farko a fannin Ilimi daga Arewacin Najeriya, rasuwa. Farfesa Adamu Bakie ya rasu yana da shekaru 94 ne a daren Jumma’a a gidansa da ke Zariya, Jihar Kaduna. Babban ɗansa, Manjo Muhammad Adamu (Ritaya), ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a sanar...
    Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga Fabrairu, 2026 domin yanke hukunci a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta shigar kan DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar. NDLEA na tuhumar Abba Kyari, tsohon Shugaban Rundunar ’Yan Sanda Masu Yaƙi da Garkuwa d a Mutane (IRT),...
    Tauraro kumafitaccen mai shirya fina-finan HausaAli Huhu, ya bayyana Iran a matsayin misali wajen haskaka Musulinci a matsayin adinin zaman lafiya ta hanyar fina-finai. A wata hira ta musamman da da kamfanin dillancin labarai na Iran Press, Ali Nuhu, wanda shi ne babban Manajan Kamfanin Fina-finai a arewacin Najeriya, ya yaba wa Iran saboda kokarin...
    Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani daftarin kuduri da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agajin jin kai ba tare da wani sharadi ba zuwa Zirin Gaza. Kudurin da aka zartar a ranar Juma’a, ya yi kira ga Isra’ila da ta kare cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya tare da bin dokokin kasa da...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 2.6 domin gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnati...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Ma’aikatar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta ce za ta kashe fiye da naira miliyan dubu 18 domin gudanar da harkokinta a sabuwar shekara. Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Lawal Yunusa Danzomo ne ya bayyana haka lokacin da yake kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu 3 domin gudanar da aikace-aikacenta a lokacin aikin Hajjin 2026. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara a gaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin...
    Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya ce za su gana da bangarorin da ke rikici da juna a Sudan a birnin Geneva, sai dai shugaban bai bayyana  ranar da za a yi wannan tattaunawar ba. Guterres ya bayyana hakan ne a lokacin zantawarsa da kafar talabijin ta Al Arabiya da ke Saudiyya...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya jaddada game da mihummanci sanya hannun jari da kuma hadin guiwa a iyakoki, a matsayin abubuwan da ya fi mayar da hanakli akai a lokacin ganawarsa da shugaban kasar iraki Abdul latif rashid a gefen taron kasa da kasa na zaman lafiya a kasar Turkmenistan...
    Dakarun Sojin Rundunar Operation Haɗin Kai, sun kashe ’yan ta’adda biyu a wani samame da suka kai yankin Shettimari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga, a Jihar Borno. Majiyoyi sun shaida cewa rundunar ta kai harin ne ƙarƙashin Operation Desert Sanity V da safiyar ranar Alhamis. Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya...
    Ɗan wasan gaban Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Galatasaray ɗan asalin Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na bana, a bikin bayar da kyaututtuka ta GQ Türkiye na maza na 2025. Ɗan wasan mai shekara 26 ya sami kyautar mafi girma a bikin da aka gudanar mai ban sha’awa. Matatar man Dangote ta...
    Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu. A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pazeshkian, a ganawarsa da tokwaransa na kasar Turkmenietan Gurbanguly Berdimuhammedow a birnin Ashg’abat ya ce, a halin yanzu, fiye da duk wani lokaci – tana bukatar amintaccen madogara, zaman lafiya da kuma hadin kai. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana yabawa kasar Turkmenistan kan shirinta karban...
    Shugaban hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa, kasar zata ci gaba a fannonin ilmi guda 6 na fasahar nukliya wato Fission, Fussion, Lasers, fasahar Quantum, da kuma Plasma duk tare da barazanar yaki, ko na siyasa ko kuma yakin kwakwalwan da makiya suke wa kasar. Yace, matsayin  JMI a bayyana...
      A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000.   Jihar Delta A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar...
    Masana’antun kirar motoci na kasar Sin, sun samar tare da sayar da motocin da suka haura miliyan 31 cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, wanda hakan ke shaida irin ci gaban da suka samu ta fuskar fitar da hajoji. A cewar wasu alkaluma daga kungiyar kamfanonin kirar motoci na kasar Sin, tsakanin watan Janairu...
    Jam’iyyar PDP a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo. Jam’iyyar ta tabbatar da rasuwar ce a cikin wata sanarwa da sakatarenta yada labaranta na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya fitar. Rahotanni sun ce Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa da ke gidan gwamnati, Yenagoa, a ranar...
    Wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari gidan babban Jami’in kula da ofishin ‘yan sandan na Tattaɓa, ASP Mohammed Modu, da ke yankin Bara a ƙaramar hukumar Gulani, Jihar Yobe. Kamar yadda rahoton Jami’an tsaro ke nunawa cewa, da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar daren ranar 9 ga Disamba, maharan...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Hukumar bunkasa ilimin manya ta jihar Jigawa tace za ta kashe naira milyan 400 wajen gudanar da harkokin ta a sabuwar shekara ta 2026. Shugaban hukumar. Dr. Abbas Abubakar Abbas, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin hukumar a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa. Dr...
    Suleiman-Jibia ya ƙara sanar da cewa, majalisar ta amince da kafa Cibiyoyin Horar da Malamai a Katsina, Daura, da Funtua.   “Cibiyoyin za su taimaka wajen haɓaka tsarin koyarwar malaman domin samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai a faɗin jihar,” in ji shi ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra...
    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta lalata kayayyaki marasa inganci da suka kai sama da Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa. Kayayyakin da aka ƙwato daga jihohin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da Nasarawa, Benuwe da Kogi da Filato, an lalata su ne a wurin zuba shara a Angwan...
    Shugaban kasar Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa kasarsa ta zama abin misali a duniya, saboda sauyin da jama’a suka bukata tun lokacin da ya hau mulki a 2022. “Domin cimma cikakken ‘yancin kai, ya zama dole a bi juyin juya halin inji shi a wani jwabi ta gidan talabijin a jajaribin cika...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Nijeriya Ta Himmatu Wajen Inganta Tsarin Karatun Allo December 11, 2025 Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja December 11, 2025 Labarai Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 11, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato December 11, 2025
    Ghana ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin cin mutuncin ‘yan kasarta a filin jirgin sama na Ben Gurion na Isra’ila, bayan da aka tsare wasu fasinjoji ko kuma aka yi musu korar kare, ta kuma ce tana tunanin daukar irin wannan matakin na ramuwar gayya. Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana...
    Hukumar ICPC ta ce da ana aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da kusan kashi 80 na ’yan Najeriya na ɗaure a gidan yari. Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi. Kisan...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025. Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya...
    Jakadan kasar iran na din din din a majalisar dinkin duniya Amir saeid iravani ya jaddada matsayin Tehran na ganin ta hana kisan kare dangi, kuma tayi tir da kisan kare dangi da HKI ta yi a yankin Gaza, kuma ya fadi hakan ne a wajen taron koli karo na 10 na majalisar dinkin duniya...
    Daga Aliyu Lawal  Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa,...
    Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko. Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar. EFCC ta tsare Malami kan binciken...
    Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu. A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar...
    Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe. Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne...
    A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya. Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi. Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki. Yara ƙasa da...
    Tehran tana daukar bakwancin taron kwamitin bincike da ci gaban na kungiyar BRICS karo na 7Th wanda ya nuna irin yadda kasar Iran take ci gaba a cikin ilmin bincike da kuma na ci gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu taron na fadar cewa kasar Iran ta na samun ci...
    Taron kasa da kasa na musamman wanda aka gudanar a wata Jami’a a nan Tehran dangane da nasarar da JMI ta samu kan HKI da Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan yulin da ya gabata ya jawo hankalin kasashen duniya da dama, sannan ya sauya yadda ake daukar HKI a yankin, musaman a...
    Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar. Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar. Gwamnan Jihar Ribas...
    Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin. Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda...
    Ana taro kan yadda manzon Allah mohammad dan Abdullahi (a) ya zauna da wadanda ba musulmi ba a rayuwarsa a Madina. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto hukuma mai kula da al-adu da kuma al-amuran addinin Musulunci a nan Iran tana cewa ana gudanar da wannan taron ne a dai dai lokacinda...
    Matsalar rashin tsaro ce ta sa na yi waqar “Arewa”-SKD Arewa Muhsin Umar Chiroma wanda aka fi sani suna SKD Arewa, xaya ne daga cikin matasan mawaqan zamani da ludayinsu ke kan dawo wajen tashe, musamman a shafukan sada zaumunta. A hirarsa da Aminiya, saurayin mawaqin ya bayyana abin da ya xauki hankalinsa har ya...
    Ministan ilimi da kere-kere na Iran Husain Simayi, wanda ya gana da jakadan kasar  Turkiya  anan Iran Hijabi Kalanjik ya bayyana azamar kasashen biyu domin yin aiki a wannan fagen. Ministan ilimin da kuma fasahar kere-kere na Iran ya kuma ya kuma ce; Iran tana bayar da muhimmanci ga jami’o’in Turkiya wadanda a bisa ma’aunin...
    Daga Nasir Malali An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a...
    Wakiliyar musamman ta majalisar dinkin duniya kan yankin falasdinu da aka mamaye  Francesca Albanese ya bayyana irin halin da ake ciki a yankunan falasdinu da isra’ila ta mamaye a matsayin babban bala’I, ta ce kuma shi ne kisan kare dangi na farko da ya tada hankali duniya sosai. Da take bayani wajen rufe taron da...
    Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a wurin bikin fina-finai na Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu...
    An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja. Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata. ’Yan bindiga sun...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa har yanzu Amurka ba ta nuna sha’awarta ta shiga “tattaunawa mai ma’ana ba,” yana mai sake nanata cewa dole ne Washington ta fara amincewa da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya a karkashin Yarjejeniyar hana yaduwar Makaman Nukiliya ta (NPT). A...
    Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a...
    Kungiyar ‘yan wasan  ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda...
    Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin...
    Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa  dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada...