Aminiya:
2025-11-21@12:28:58 GMT

Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta

Published: 21st, November 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Saint Mary da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar.

Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a.

’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su

Shugaban Sashen bayar da Agaji na Ƙaramar Hukumar, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula, amma bai bayar da cikakkun bayani ba.

Sai dai a cikin wata sanarwa, Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Abubakar Usman, ya ce bayan samun bayanan sirri tun da farko, gwamnati ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a yankin.

Sai dai ya  ce makarantar da abin ya shafa ta ƙi bin umarnin ta kuma buɗe makarantar.

“Gwamnatin Jihar Neja ta yi matuƙar bakin ciki da labarin sace ɗaliban makarantar St. Mary da ke Ƙaramar Hukumar Agwara. Har yanzu ba a tabbatar da adadin ɗaliban da aka sace ba yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tantance lamarin.

“Jihar ta samu bayanan sirri tun da farko da ya nuna ƙaruwa barazanar tsaro a wasu sassan yankin arewa.”

“A kan haka ne Gwamnatin jiha ta bayar da umarnin dakatar da dukkan ayyukan gine-gine tare da rufe dukkan makarantun kwana a yankin da abin ya shafa a matsayin kandagarki

“Sai dai makarantar St. Mary ta ci gaba da zama a buɗe da ci gaba da karatu ba tare da sanarwa ko neman izini daga gwamnati ba.”

“Jami’an tsaro sun riga sun fara cikakken bincike da aikin ceto domin tabbatar da an dawo da ɗaliban gida lafiya.”

“Gwamnatin Jihar Neja tana aiki kai tsaye da dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa kuma za ta ci gaba da bayar da rahotanni yayin da bayani kara fitowa.”

“Gwamnati na kira ga masu makarantu, shugabannin al’umma, da duk masu ruwa da tsaki da su bi ƙa’idojin tsaro da aka bayar domin kare rayukan jama’a. Kariya ga rayuka, musamman na ’ya’yanmu, ita ce babban abin da wannan gwamnatin ta sa a gaba,” in ji shi.

A Jihar Kwara makwabciyar Nejan, gwamnatin jihar ta sanar da rufe makarantu fiye da 50 a kananan hukumomi hudu sakamakon sake ƙaruwar hare-hare a yankunansu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnatin Jihar Neja tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru

Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba.

Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu.

Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana

An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci.

Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS.

Haka kuma, ya nemi a mayar da waɗanda ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali domin suke samun damar ganawa da lauyoyinsu cikin sauƙi.

Lauyan DSS, David Kaswe, ya ƙi aminta da wannan buƙata.

Ya ce lauyoyin dole ne su rubuta wa DSS buƙatunsu kafin su ziyarci waɗanda ake tuhuma.

Alƙalin kotu, Emeka Nwite, ya yanke shawarar bai wa lauyoyin waɗanda ake tuhuma ƙarin lokaci domin shirya wa shari’ar.

Ya ce wannan zai tabbatar da adalci, sannan ya sanya ranar shari’a 15 ga watan Janairun 2026, domin fara sauraren shari’ar.

DSS, tana zargi waɗanda ake tuhuma da jagorantar kai harin gidan yarin Kuje da ke Abuja a 2022, inda fursunoni sama da 600 suka tsere.

Hakazalika, ta zarge su da kai hari wajen haƙar ‘uranium’ a Jihar Neja, tare da sace mutane da dama, ciki har da injiniyan ƙasar Faransa, Francis Collomp, a shekarar 2013.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade
  • ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Kiran Da A Sanya Isra’ila Cikin Jerin Masu Aikata Abin Kunya Saboda Kashe Yara
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
  • Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru
  • Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya
  • ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi