2025-07-09@17:03:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 636

«yi aiki a matsayin»:

    An gabatar da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin Shugaban Kwamitin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN). Wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da Ganduje ya yi daga shugabancin APC kwanan nan, inda ya bayyana cewa ya yi hakan saboda wasu muhimman dalilai na ƙashin kansa. 2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai Jam’iyyar ta maye gurbinsa da Ali Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya. Gbenga Saka, mai bai wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shawara kan harkokin dijital, ya wallafa bidiyon bikin rantsar da Ganduje a shafin X. Ganduje, wanda tsohon...
    Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan  sahayoniyya kan kasar Iran Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren. Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari. A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
    Shugaban Majalisar Kolin siyasar kasar Yemen ya jaddada ‘yancin kowa da kowa wajen gudanar da zirga-zirga a teku in banda makiya ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, Field Marshal Mahdi al-Mashat, ya jaddada aniyar kasar ta Yemen na ba da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ga kowa da kowa in banda makiya yahudawan sahayoniyya da kuma masu goya musu baya a lokacin da suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza. A cikin wata sanarwa da Al-Mashat ya fitar ya ce: Ba su da wani sha’awar kai hari ga duk wanda ba shi da alaka da goyon bayan makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai kira ga dukkanin kamfanonin jiragen ruwa da su...
    Kungiyar Kano Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (Kano-ACReSAL) ta kaddamar da yakin neman ilimin sauyin yanayi zuwa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ’Yan Mata da ke Kano a wani bangare na shirinta na “Catch Them Young”. Wato Ilmantar da Matasa.   Gangamin wayar da kan jama’a wani bangare ne na kashi na biyu na yunkurin aikin na jawo dalibai, malamai, da kwararrun muhalli wajen tattaunawa kan sauyin yanayi da kuma shigar da matasa wajen magance shi.   Mukaddashin mai kula da ayyukan, Dr. Abdulhamid Bala, ya sanar da daliban cewa sauyin yanayi ya kasance babban kalubalen da ba za a yi watsi da shi ba.     “Sauyin yanayi ya kasance barazana mai dorewa ga dorewar duniya. Amsarmu dole ne...
    An kaddamar da jam’iyyar African Democratic Party, ADC a Gombe mako guda bayan wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun hada kai cikin jam’iyyar.   Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Gombe kuma tsohon ministan sufuri Alh. Idris Abdullahi, ya ce makasudin shiga jam’iyyar shi ne ceto kasar nan daga kangin tattalin arziki da dora ta kan turbar ci gaba.   A cewarsa gamayyar jam’iyyun adawa sun zabi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyya daya tilo da za ta samar da hanyar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.   Sanata Idris Abdullahi ya jaddada kudirin kungiyar a Gombe na ci gaba da kasancewa da hadin kai domin cimma burin ta.   Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Gombe Alh. Auwal Barde ya ce...
    Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa mai shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma yaudarar jama’ar duniya. Ko Lai ya manta da cewa, a ran 19 ga watan Mayun da ya shude, shekaru 9 a jere ne babban taron hukumar lafiya ta duniya WHO ya ki yarda da shirin da wasu kasashe tsirraru suka gabatar na halartar Taiwan taron. Yawancin kasashen duniya sun nanata matsayinsu kan kiyaye kudurin babban taron MDD mai lamba 2758, da nace wa ga bin ka’idar kasar Sin daya tak a duniya,...
    Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala Jebilet a Jihar Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya. Gwamnan jihar Tindouf Mustapha Dahou, da babban darektan CRCC Dai Hegen sun halarci bikin kammala aiki. A gun bikin, Dahou ya ce, CRCC da jiharsa, sun yi hadin gwiwar daga matsayin layin dogon zuwa masana’antu, matakin da ya ingiza bunkasar tattalin arzikin wuri zuwa mataki na gaba. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su kara hada...
    Ahmed Musa ya ce zai buƙaci haɗin kai daga duk masu ruwa da tsaki domin ciyar da ƙungiyar gaba. Ya kuma ce zai taimaka wajen samar da kayan aiki da tallafin da ƙungiyar ke buƙata domin ta yi fice a sabuwar kakar wasa mai zuwa. Ya ce: “Ina tabbatar wa kowa cewa da goyon bayanku da na mambobin hukumar, zan yi iya ƙoƙarina don dawo da Kano Pillars matsayin ya kamata a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi ba kawai a Afirka ba, har ma a duniya.” Ƙungiyar Kano Pillars, wacce ta taɓa lashe kofin NPFL sau huɗu, ta fara shirin tunkarar kakar wasa ta shekarar 2025/2026. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Kakakin hafsan hafsoshin sojojin Iran ya ce; Iran tana dora wa Amurka  alhakin duk wani hari da za a kai mata Kakakin hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Birgediya Janar Abul-fazl Shekarchi ya jaddada cewa: Iran tana dorawa Amurka alhakin duk wani harin wuce gona da iri da za a kaddamar kan kasarta. A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Shekarchi ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran ba su ne suka kaddamar da harin kan wata kasa ba, amma sun mayar da martani cikin kwanaki 12 na arangama da munanan hare-hare da suka fuskanta daga mabartan ‘yan sahayoniyya makiya. Ya kara da cewa, “An sanya wa makiya tsagaita bude wuta ne bayan da suka fuskanci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana kuma ya zanta da wani babban malamin yahudawa mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron kasashen BRICS a kasar Brazil. Rabbi Yisrael Dovid Weiss, wanda ya je Brazil domin ganawa a gefen taron BRICS, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, inda suka yi musayar ra’ayi da shi. Wani abin lura shi ne cewa a baya malamin ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Brazil bayan bude littafin ta’aziyya ga shahidan da yahudawan sahayoniyya da suke kai wa hari a                                                                    kasar hari. A...
    Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin  gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen. Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa...
    A ƙarshe, Farfesa Pate ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gina sabbin gine-gine a jami’ar kamar ginin Majalisar Jami’a, katangar jami’a, da ɗakunan kwana. Ya bayyana cewa dalibai 6,870 ne suka kammala karatu, ciki har da 91 da suka samu First Class da kuma 16 da suka kammala karatun digiri na PhD. Haka kuma, jami’ar ta karrama mutane biyar da digirin girmamawa saboda gudummawarsu ga ci gaban kasa da ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomin gwamnati.” “Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori kara mai kyau ta fashin zabe.” Ya bayyana. Ya ce irin wannan matsalar na samar da mutanen da ba su ko iya cin zabe a cikin dangin su ko al’ummar su amma sune ke tinkahon lashe zabe. A cewarsa a matsayinsa na dan majalisar dattawa suna kokarin gabatar da dokokin da za su shawo kan wadannan matsalolin, ya ce sun san hukumar zabe ba za...
    Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar shiga filayen kiwo ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ƙara tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma. Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka “Duk wanda aka kama yana da hannu a wannan aika-aikar, za mu hukunta shi bisa doka,” in ji Gwamna. Ya kuma roƙi makiyaya da su guji shiga gonaki domin...
    Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa idan har Barcelonan za ta iya biyan kudin da aka yi masa farashi. Kungiya ta kwana-kwanan nan da ta nemi Rashford ita ce kungiyar Bayern Munchen ta Jamus, bayan da Liberpool ta ce ba za ta sayar mata da Luiz Diaz ba, ana ganin yanzu kungiyar za ta karkata akalarta zuwa neman Rashford. Kungiyoyi irinsu Newcastle United da Tottenham da kungiyoyi daga Saudiyya duka sun...
    Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada zumunta. Matakin ‘yan adawar na shiga ADC, na zuwa ne bayan kasa cimma bukatarsu ta yi wa sabuwar kungiyar mai suna ‘All Democratic Alliance’ (ADA), rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, sakamakon jan kafa da suka rika samu daga babbar hukmar zabe ta kasa (INEC). Haka zalika, Atiku Abubakar da wasu manyan jam’iyar PDP, sun nemi ‘yan jam’iyyar da su hada hannu da su wajen shiga...
    Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa karkashin tsarin hadakar BRICS, ya zamo wani muhimman karfi na ingiza nasarar samar da duniya mai mabanbantan tasiri, wadda za ta wanzu bisa daidaito da adalci, da kuma tsari mai game dukkanin sassa, da tattalin arziki da dukkanin duniya za ta ci gajiyarsa. Kasashe mambobin BRICS, sun yi aiki tukuru wajen ingiza tsarin cinikayya da kudaden juna, da gina tsarin hada-hadar kudade mai zaman kansa,...
    Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce gona da iri, zai gaggauta zuwa karshensu ne.” Sanarwar ta kuma ce: Muna tunawa ne da zagayowar cikar shekaru 42 daga wancan aikin ta’addanci, da a yanzu kwanaki kadan ne su ka wuce na kawo karshen yakin da HKI da Amurka su ka kallafa mana na tsawon kwanaki 12. Yaki ne wanda martani mai karfi da jamhuriyar musulunci ta Iran ta mayar yake kara fito...
    A wani rahoton musamman da jaridar ” Telegraph” ta Birtaniya ta buga,  ta amabci cewa; makamai masu linzami da Iran ta harba wa Isra’ila sun sauka kai tsaye akan wasu muhimman cibiyoyin soja. Jaridar ta kara da cewa; Mahukuntan Isra’ila ba su bayyana wa duniya wadannan wuraren da makamai masu linzamin su ka fadawa ba, saboda aiki da dokar soja ta Sakaye labaran wuraren da aka kai wa hare-hare. Rahoton jaridar ya ce, ya sami bayanai ne daga hotunan tauraron dan’adam na jamiar Jahar Oregon da suka saba yin aiki da irin wadannan bayana da suke tarawa domin gano barnar da aka yi a wuraren yaki. Rahoton ya ci gaba da cewa cibiyoyin sojan da Iran ta kai wa harin,...
    Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano: Gani suke ai in su nuna suna samu kamar matan nasu za su dora musu hidima da yawa, sun gwamma ce su bar matansu da wahala. Wani ma dan rashin imani kokari yake ita matar ta ciyar da shi alhalin yana da damar sa, shi ya sa ko yaran wani lokaci in suka taso komai na mahaifiyarsu sai daga baya ya zo ana da-na-sani mara amfani a lokaci da ba shi da amfani. Rashi tausayi ne kawai kuma kusan yanzu ma kaso casain na maza haka suke, ka so daya ne suke kyautatawa iyalansu. Kalubale babba ma kuwa shi ya sa sam! yanzu auren ma ba ya karko, karshe a jefa...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da cewa: Ta gabatar da martani mai kyau ga shawarar dakatar da bude wuta tsakaninta da gwamnatin mamayar Isra’ila Kungiyar Hamas ta sanar da kammala tuntubarta tare da gabatar da kyakkyawar amsa ga sabuwar shawarar neman dakatar da bude wuta, inda ta bayyana shirinta na nan take na yin shawarwari kan tsarin aiwatarwa. Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Falastinu ta Hamas ta sanar a yammacin jiya Juma’a cewa ta kammala shawarwarin cikin gida da kuma tuntubar wasu bangarori da dakarun Falasdinawa dangane da sabuwar shawara da masu shiga tsakani suka gabatar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza. Kungiyar ta yi nuni da cewa ta mika martanin...
    A bana ake bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ana kuma daf da gudanar da sabon zagayen taron jagororin Sin da EU. Sakamakon hakan, jerin ayyukan cudanya a matsayin koli tsakanin sassan biyu na kara jan hankali. A baya-bayan nan, an gudanar da dandalin tattaunawa na manyan jami’ai tsakanin Sin da EU karo na 13 a birnin Brussels na kasar Belgium. Kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da shugabannin EU, tare da ziyartar kasashen Jamus da Faransa. Bangaren Sin ya jaddada cewa, bunkasar tafarkin ci gaban alaka tsakanin Sin da EU ya nuna kyakkyawar dangantakar sassan biyu maimakon adawa da juna, kuma hadin gwiwarsu shi ne...
    Har ila yau, da yake jawabi, mai gudanar da taron, Bonabenture Melah, ya ce makasudin tattaunawar shi ne, inganta dabarun sadarwa, da inganta fassarar bayanai, da samar da hadin gwiwa tsakanin kwararru a NiMet da ‘yan jarida, ta yadda ‘yan jarida za su yi aiki yadda ya kamata. Har ila yau, darektan Sabis na Hasashen Yanayi (DWFS) a NiMET, Farfesa Bincent Weli, ya lura cewa, “sauyin yanayi na da tasiri kai tsaye a rayuwarmu ta yau da kullum.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin wasu sabbin hadimai 19 da za su yi aiki a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman domin ƙara inganta aikin gwamnati a jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a. Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu Yanzu adadin hadiman da ke aiki da Gwamna Abba sun zarce mutum 300. Hadiman sun haɗa da Masu Ba da Shawara na Musamman, Manyan Mataimaka na Musamman, Mataimaka na Musamman da kuma Masu Taimaka Masa. Gwamnan ya fara naɗa hadimansa ne a ranar 16...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya shugabancin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars. Ya naɗa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin sabon Babban Manajan ƙungiyar. An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno “ADC za ta fuskanci matsala wajen zaɓen wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa” Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake gina ƙungiyar kafin tunkarar kakar wasa ta 2025-2026 a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL). A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, an yanke hukuncin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon ƙafa. Gwamnatin ta rushe tawagar hukumar wasanni ta jihar tare...
    Ministan Babban Birninn Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta labarin cewa ya yanka wa ’ya’yansa manyan filaye a Abuja, inda ya ce in ma haka ne suna da hakki a matsayinsu na ’yan Najeriya. Ana dai zargin Wike da ba biyu daga cikin ’ya’yansa fili mai fadin murabba’in hekta 2,082, dayan kuma mai fadin hekta 1,740, wanda aka kiyasta darajarsu ta haura Naira tiriliyan tara. Da yake zantawa da ’yan jarida a Abuja ranar Alhamis, Wike ya karyata labarin na cewa ya ba ’ya’yan nasa filayen a unguwannin Maitama da Asokoro. Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC Filato: Mahara sun cire hannun matashi a kan hanyar komawa gida daga jana’iza To sai dai duk da haka, ya kare...
    Daga safiyar yau juma’a, Falasdinawa 17 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren da HKI ta kai wa Falasdinawa ‘yan hijira a yankin Mawasi dake Kudancin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a gabashin birnin Gaza, haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki nau’in Code Copter ” wajen bude wuta akan wannan yankin. A cikin unguwar Shuja’iyya kuwa, sojojin sahayoniyar sun tarwatsa da rusa gidajen Falasdinawa. A sansanin ‘yan hijira na Jabaliya dake arewacin Gaza ma dai jiragen yakin HKI sun kai jerin hare-hare masu tsanani da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu. A daren jiya Alhamis ‘yan sahayoniyar sun yi kisan kiyashi akan Falasdinawan...
    Ya bayyana cewa, kungiyar na ci gaba da nazartar na rabar da man kai tsare, na shirin na matatar man ta Dangote, wanda daga baya, kungiyar za ta shiga cikin shirin gadan-gadan. Clement, ya sanar da cewa, kafin kungiyar ta shiga cikin shirin kai tsaye, yana da kyau a fara tattaunawa da Dangoten da kuma sauran da hukumomi. A cewarsa, ta hanyar tattaunawar ce, za ta sanya kungiyar ta shiga cikin shirin, domin a yanzu, muna ci gaba da yin nazari ne, kan shirin na Matatar ta Dangote. Sakataren ya ci gaba da cewa shirin da matar ta Dangote ta bullo dashi na rabar da man kai tsaye, musamman iskar Gas, abu ne da kungiyar take gani ya dace. “Shirin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran cin amanar diflomasiyya ce Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana harin da sojojin Amurka suka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya a matsayin cin amanar diflomasiyya da kuma cewa wani mataki ne da ba a taba ganin irinsa ba ga tsarin doka da hakkin kasa da kasa da kuma tsarin hana yaduwar makaman nukiliya. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da Ronald Lamola, ministan hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa na Jamhuriyar Afirka ta Kudu, sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya bayan dakatar da hare-haren soji da yahudawan sahayoniyya...
    Rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai ban tsoro ya bayyana cewa: Manyan kamfanoni suna da hannu wajen aiwatar da kisan kare dangi a Gaza Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana sunayen wasu manyan kamfanoni na duniya sama da 60 da ke da hannu a tallafawa wajen gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a yankunan gabar yammacin kogin Jordan da kuma hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza. Rahoton wanda wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ta wallafa ya samo asali ne daga bayanai sama da 200 daga kasashe, kungiyoyin kare hakkin bil adama, masana ilimi da kamfanoni. Ta...
    Rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai ban tsoro ya bayyana cewa: Manyan kamfanoni suna da hannu wajen aiwatar da kisan kare dangi a Gaza Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya bayyana sunayen wasu manyan kamfanoni na duniya sama da 60 da ke da hannu a tallafawa wajen gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida a yankunan gabar yammacin kogin Jordan da kuma hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza. Rahoton wanda wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ta wallafa ya samo asali ne daga bayanai sama da 200 daga kasashe, kungiyoyin kare hakkin bil adama, masana ilimi da kamfanoni. Ta...
    Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
    Ƙungiyar Hamas ta sanar da karɓar tayin tsagaita wuta a yaƙin Gaza kuma tuni ta soma nazarin sabuwar yarjejeniyar aka gabatar mata. Hamas wadda ta nuna alamun samun masalaha ta bayyana cewa manufar yarjejeniyar ita ce kawo ƙarshen hare-hare Isra’ila da janye dakarunta daga yankin. Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC Ƙungiyar ta ce tana tuntuɓar abokan shawararta, sannan ta jinjina wa ƙoƙarin masu shiga tsakanin. Shugaban Amurka ne ya gabatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 60, wadda ya ce tuni gwamnatin Isra’ila ta amince da ita. To sai dai rahotonni na cewa da dama cikin ministoci masu ra’ayin riƙau ba...
    A kakar da ta wuce, Arsenal ta karɓi Neto a aro daga Bournemouth domin taimaka wa Raya, amma yanzu ta yanke shawarar dawo da shi domin ɗaukar Kepa daga Chelsea. Kepa ya buga wasanni 163 a Chelsea, kuma yana cikin tawagar da ta lashe kofin zakarun Turai, Europa League da kuma kofin ƙungiyoyin duniya (Club World Cup). Haka kuma, ya shafe shekara guda a aro a Real Madrid, inda ya taimaka musu suka lashe Laliga da Champions League a kakar 2023-24. Chelsea ta ɗauki Kepa ne a 2018 bayan kasa ɗaukar Thibaut Courtois daga Atletico Madrid da Alisson Becker wanda ya koma Liverpool. Daga baya kuma ta gane cewa bai cancanci kuɗin da aka kashe a kansa ba, ciki har...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare.   A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin hali. NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan makon zai yi...
    A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wakilan kasashen duniya a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna girmamawa ga wadanda suka yi shahada a harin wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Iran Masu fafutukar wanzar da zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka da wakilan kasashe daban-daban a Majalisar Dinkin Duniya sun gabatar da bayanai kan mutanen da suka yi shahada a hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran ta hanyar halartar hedkwatar wakilan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya. Daruruwan masu fafutukar neman zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka ne suka hallara a hedkwatar tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin New York a ranar Litinin din wannan mako don karrama shahidan...
    Magajin garin birnin Tehran ya bayyana cewa: Karyar ‘yan sahayoniyya ya tonu na cewa ba su kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran ba Magajin garin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ali-Ridha Zakani ya tabbatar da cewa: Karairayi da ‘yan sahayoniyya suke yadawa dangane da rashin kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran a fili yake karara. Yana mai nuni da cewa akwai kwarararn dalilai da ake da su wadanda suke fallasa karyar wadannan ikirari. A cikin bayanansa, Zakani ya ce: Dalilai kan wadannan karairayi su ne kaburbura gawawwaki da suka hada da fili mai lamba ta 42 a makabartar Al-Jannar – Zahra da ke babban birnin Tehran. Ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka za su mayar da martani mai tsanani akan sabon wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya.  Kakakin sojojin na Iran ya kuma ce; Dama ko kadan jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta taba amfani da Kalmar ‘dakatar da fada ba” a mastayin zabi.  Haka nan kuma ya ce; ‘Yan sahayoniya ba wadanda za a amince da su ba ne, balle gaskatawa, ba a cikin Iran ba, balle kuma a kowane wuri a duniya.”  Shikarci ya kuma yi ishara da cewa; sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwan fiye da kowane lokaci a baya, don haka duk...
      Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka.   Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar Kano suke yi masa na gadon alkairai da ya bari kuma a matsayinsa na dattijon jihar.   Ana sa ran jana’izar da za a yi a birnin Madina, za ta samu halartar wakilan jiha da na tarayya, da ‘yan uwa, ‘yan kasuwa, malaman addinin Islama, da masoya daga sassan duniya baki daya, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu. Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.” Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara...
    Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan. Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma kula da zaben kananan hukumomin, za a kuma gabatar da ita ga ‘yan Nijeriya don yin nazari a taron sauraron jin ra’ayoyin. Wadansu batutuwa da aka fitar a cikin sanarwar da suka hada da kudirin dokoki guda biyu kan tsaro da manufar samar da ‘yansandan jihohi da majalisar tsaro na jihohi don tsara manufofin tsaro na cikin gida a matakin yankuna. “A bangaren gyaran manufifin...
    Majalisar dokokin tsibirin Corsica a yankin Mediterranean, wacce ta kasance jiha ce a kasar Faransa, ta amince da kasar Falasdinunu a matsayin cikakken kasa mai zaman kanta a MDD. Tsirin dai tana neman samun yanci daga kasar faransa, ta amince da samuwar kasar Falasdinu da kuma yin watsi da HKI a matsayin yar mamaya. Kissan kiyashi mai ban tsoro wanda HKI take yi a zirin Gaza ya tada hankalin mutane da dama a duniya kuma ya shara fagen amincwa da kasar Falasdinu mai zaman kanta. Labarin ya kara da cewa Marie-Antoinette Maupertuis shugaban majalisar dokokin kasar ta Corsican ne ya gabatar da bukatar amincewa da kasar Falasdini a majalisar. Ya ce bisa wasu dokokin MDD kasar Falasdinu kasace mai zaman...
    Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka yi kan cibiyoyin makamashin nukiliya, da kafofin yada labarai, da cibiyoyin kiwon lafiya na Iran, da kuma wuraren zama, gidajen yari da birane da kauyuka, a matsayin misali karara na keta dokokin kasa da kasa da hakkokin bil’adama. A cikin wata wasika da ya aike wa kwamishinan kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk Nasser Seraj mataimakin shugaban hukumar...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi zai shaida cewa Iraniyawa sun zubar da jininsu tare da kin ba da kasarsu da mutuncinsu. Araqchi ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa: “Duk da zafi da rashi na shahidansu kwatsam, amma tunaninsu yana nan a cikin zukatan masu hankali, da kuma zukatan al’ummomi masu zuwa, kuma suna sane da yin riko da Imani da hanyarsu, kuma za su ci gaba da bin tafarkinsu.”...
    Duk ana dora alhakin yadda lamarin cinikin Bayi ya bunkasa kan wani mutum dan asalin kasar Birtaniyya da ake kira da suna,John Hawkins. Hawkins  shi ne mutumin da ya kara daukaka, bunkasa,da zamanan har da lamarin cinikin Bayi”manufa anan yayi  gyare- gyare daga yadda Turawan kasar Fotugal suka fara da barinsa,ya yi masa kwaskwarima,zuwa lamarin kasuwanci mai daraja”. Jiragen ruwa suna tasowa daga Kasar Birtaniya ko kuma Ingila  da Bindigogi, Madubi,da kuma Giya,Jiragen na zuwa wani wurin da ake kira da suna inda ake daukar Bayi a kai su  kasar ko kasashen da suka saye su, yanzu wurin ana kiransa da suna yankin Neja Delta inda daga can ne kuma za ‘a fara tafiya, har sai sun kai inda zasu...
    An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano. An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi. Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau  Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar. Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane. Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina...
    Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau  ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi. Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa...
    Ana neman tono gawar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, marigayi Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala, domin yin gwajin jini (DNA) da nufin tantance halastattun ’ya’yansa da za su ci gadon dukiyar da ya bari. Batun tono gawar ta kunno kai ne bayan taƙaddama ta yi tsami a tsakanin ’ya’yan tsohon gwamnan a kan rabon gadonsa. Babbar ’yar marigayin mai suna Uwargida Oluwatoyin Alao-Aderinto ce ta shigar da ƙara a gaban Mai Shari’a Taiwo na Babbar Kotun Jihar Oyo ta hannun lauyanta, Oladipo Olasope (SAN), inda ta roƙi kotun ta bayar da umarnin tono gawar mahaifin nasu daga kabarinsa domin yin gwajin ƙwayar halittarsa ga wasu mutane bakwai da ke iƙirarin cewa su ne halastattun ’ya’yan marigayin. Uwargida Aderinto ta shigar da ƙarar...
    Wasan farko da Leicester za ta buga a gasar Championship zai kasance a gida, inda za ta kara da Sheffield Wednesday ranar Laraba, 10 ga watan Agusta mai zuwa. A baya, Van Nistelrooy ya taɓa riƙe matsayin kocin riƙon ƙwarya na Manchester United, bayan da suka sallami Eric Ten Hag kafin su ɗauki Ruben Amorim daga Sporting CP ta ƙasar Portugal. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasan farko da Leicester za ta buga a gasar Championship zai kasance a gida, inda za ta kara da Sheffield Wednesday ranar Laraba, 10 ga watan Agusta mai zuwa. A baya, Van Nistelrooy ya taɓa riƙe matsayin kocin riƙon ƙwarya na Manchester United, bayan da suka sallami Eric Ten Hag kafin su ɗauki Ruben Amorim daga Sporting CP ta ƙasar Portugal. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kara da cewa, babban makasudin kafa cibiyoyin da kudaden jama’a shi ne bunkasa masana’antu, da rage bukatar musayar kudaden waje, da samar da fa’idoji masu yawa ga kasar nan. Idu ya ce IDCs, musamman Cibiyoyin shiyyoyi hudu, sun cika da manyan injina don yada ilimin fasahar masana’antu da fasahar da za su yi tasiri matuka kan yunkurin kasar na samar da masana’antu. Ya bayyana damuwarsa cewa, “A tsawon shekaru, kusan dukkanin IDCs, ma’aikata da kayan aiki a yi asarar su kuma wasu kayan aikin sun daina aiki. “Duk da cewa gwamnatin tarayya ta mika wadannan cibiyoyi ga hukumar kula da masu kananan sana’o’i ta kasa (SMEDAN) tsawon wasu shekaru a yanzu, babu wani abin da aka yi gaba daya...
    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta  kafa karamar cibiyar kula da muggan kwayoyi a Damaturu babban birnin jihar Yobe. Kwamandan hukumar a Jihar, Abdulazeez Ogunboye  ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu a wani bangare na bikin ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta shekarar 2025. Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin dokokin haraji Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya Ogungboye ya kara da cewa cibiyar wacce tun daga lokacin da ta fara aiki na daya daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a jihar. “An shigar da mutane tara da suke ta’ammali da muggan kwayoyi a cibiyar, daga cikin su...
    Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu. Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa wasu shaguna da ke a wata kasuwa, da ka mayar a matsayin wajen kwanan, ‘yan gudun hijira, wuta. Duk da kokarin da wasu matasa da kuma kokrin jami’an tsaro na dakile maharani, hakan ya faskare su, hatta wani daya daga cikin jami’in tsaro da aka tura wanzar da tsaro, ya rasa ransa. Duk a 2025, a watan Afiiru an kai hare-hare a Logo da Ukum,...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Cristiano Ronaldo ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwatiraginsa da shekara biyu a ƙungiyar Al Nassr  da ke buga gasar Saudi Pro League. Wannan dai na nufin kyaftin din na tawagar Portugal zai ci gaba da zama a ƙungiyar har 2027, lokacin da zai kai shekara 42 a duniya. Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya Gwamnatin Katsina ta amince da ƙidayar almajirai, makarantun Islamiyya Al-Nassr ta bai wa Ronaldo kwantiragi mafi tsada a tarihin wasanni, inda ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fam miliyan 24.5 ($33.7m), lamarin da zai ba shi damar samun albashin da zai rika karbar sama da fam miliyan a duk kwana biyu. Ɗan wasan mai shekara 40 ya je Al Nassr ne a...
    A ƙoƙarinta na bunƙasa noma da samar da isasshen abinci, Gwamnatin Jihar Gombe ta amince ta sayi tan 10,000 na taki, wanda ya yi daidai da buhu 200,000 domin shirin noman daminar bana. Kwamishinan Harkokin Noma na Jihar, Dokta Barnabas Musa Malle, ya ce za a kashe Naira biliyan 8.8 wajen sayen takin. 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau Ya ce hakan na nuna yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tallafa wa manoma da kuma ƙara samar da abinci a jihar. Dokta Malle ya ce, “Gwamnati ta fito da sabbin hanyoyin aiki sama da yadda aka yi a baya, kuma za a raba...
    Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja. Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano Damagum ya kuma bayyana cewa an soke taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100 da aka shirya yi, saboda wasu matsaloli. Maimakon haka, jam’iyyar za ta gudanar da wani taro a ranar 30 ga...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya nesanta kansa daga wata kungiya da take fafutukar ganin Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a 2027. Mai magana da yawun Sanatan, Isma’il Mudashir ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, inda ya ce a maimakon haka, kamata ya yi kungiyar ta fi mayar da hankali wajen mara wa Tinubu baya ya samu nasarar yunkurinsa na bunkasa Najeriya. A kwanan nan ne dai wata kungiya mai suna Zauren Matasan APC na Arewacin Najeriya (NNPYA) ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu ya dauki Sanatan a matsayin wanda za su yi takara tare. Gwamnatin Nijeriya ta yi wa Amurka martani kan barazanar tsaro a Abuja Mali...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya. Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris...
    Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), inda ya karɓi ragamar shugabancin daga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. An sanar da hakan ne a taron shugabannin ECOWAS karo na 67 da aka gudanar a Abuja. An kashe matar aure, manomi ya jikkata a wani sabon hari a Kaduna ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa  Shugaba Tinubu, wanda ya yi wa’adin shugabancin ƙungiyar sau biyu tun daga shekarar 2023, ya bayyana cewa shugabancin ECOWAS babban abu ne a rayuwarsa. Ya ce: “Yayin da nake miƙa ragamar shugabanci ga abokina kuma ɗan uwana, Shugaba Julius Maada Bio, ina mai gamsuwa da fatan alheri ga makomar Yammacin Afirka.” Ya ƙara...
    Yanzu haka ana shirye-shiryen gudanar da taron kasa da kasa na tattauna batutuwan raya tattalin arziki na Davos na yanayin zafi karo na 16, taron da aka fi sani da dandalin Davos. A bana za a gudanar da taron ne tsakanin ranakun Talata 24 zuwa Alhamis 26 ga watan nan na Yuni, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, bisa taken “sana’o’i a sabon zamani.” A bana taron zai mayar da hankali ne ga muhimman fannoni biyar, wadanda suka hada da warware batu game da tattalin arzikin duniya, da hange game da kasar Sin, da halin da masana’antun duniya suka fuskanta na taka musu birki, da zuba jari kan al’umma da duniyar bil’adama da batun sabbin makamashi da hajoji. Game...
    Wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Alƙalin Babbar Kotun Jihar Bayelsa, Ebiyerin Omukoro. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Asabar a unguwar Ekeki, kusa da babban titin Melford Okilo a Yenagoa, babban birnin jihar. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a Filato Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen sun isa a cikin mota ƙirar Hilux, sanye da baƙaƙen kaya. Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, maharsn sun kutsa kai gidan cin abincin da alƙalin ke ciki kuma suka tilasta masa shiga motarsu. Har zuwa yanzu, ba a san inda suka kai shi ba, kuma babu...
    Ƙasar Iran ta bayyana shirinta na shiga tattaunawar sasantawa “idan aka tsagaita hare-hare”, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar ya bayyana bayan ganawa da takwarorinsa daga Faransa, Burtaniya da Jamus.   Yayin da ministocin Turai suka nuna sha’awar ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna shakku kan yiwuwar nasara, yana mai cewa Iran tana son magana kai tsaye da Amurka. Hakan ya faru ne a lokacin da rikici tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba, inda Isra’ila ta kai hari kan wasu wurare a Tehran, kuma Iran ta mayar da martani da harin makamai. Fadar White House ta bayyana cewa Trump zai yanke shawara cikin makonni biyu kan ko Amurka za ta ɗauki mataki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar tantance fina-finai ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta ce za ta ci gaba da sa ido tare da ɗaukar matakin shari’a kan duk wani da ya yi amfani da sunan barkwanci don yada abin da ya kira da “nishadi mai tada zaune tsaye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A cewarsa, shaye-shayen miyagun kwayoyi, shi ne musabbabin da ke haifar da aikata laifuka da dama, wanda galibi ke zama sanadin tashin hankali da rikice-rikice a cikin al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar, Adamu Muhammad ya sanya wa hannu, ta ce an lalata barasa a Damaturu, a wani mataki na aiwatar da dokar hana sha da kayan rarraba barasa a jihar. Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Dokta Yahuza Hamza Abubakar ne ya bayyana cewa aikin ya...
    Ayatollah ya yi gargaɗi cewa, idan Amurka ta shiga cikin rikicin kai-tsaye don taimaka wa Isra’ila, wannan zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin matsala babba. Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya shafe kwanaki shida yanzu, inda mutane da dama suka mutu a ɓangarori biyun, baya ga asarar dukiyoyi da gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yanzu haka fargaba ta karaɗe yankin, yayin da jama’a ke roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye domin kawo ƙarshen wannan matsala da ta dabaibaye rayuwarsu da amfanin gonarsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu, ya kaddamar da aikin samar da ruwan sha mai tsafta wanda kamfanin CGCOC na kasar Sin ya tallafa wajen gudanar da shi a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa, ta yin aiki tukuru a fannin samar da ababen more rayuwa, da kai tsaye za su inganta rayuwar al’ummun kasar. Shugaba Tinubu ya bayyana aikin a matsayin muhimmin mataki na tabbatar da al’ummun birnin sun samu ruwa mai tsafta, mai dorewa kuma isasshen a gidaje da hukumomi, da dukkanin sassan birnin. Ya kuma godewa gwamnatin kasar Sin da kamfanin CGCOC, bisa hadin gwiwarsu wajen tabbatar da nasarar aikin. Yayin da yake nasa tsokaci kuwa a bikin kaddamar da aikin, mukaddashin jakadan Sin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev gabanin taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na biyu. Kazalika, daga bisani duk dai a yau shugabannin biyu za su halarci bikin musayar rubutaccen daftarin hadin gwiwa tsakanin Sin da Kazakhstan. Xi ya isa Astana, babban birnin Kazakhstan yau Litinin, domin halartar taron koli karo na biyu tsakanin kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Wannan ya nuna ragin hauhawar farashi a faɗin ƙasar nan. Masana na ganin wannan ragi a matsayin alamar ci gaba ga tattalin arziƙi, sai dai har yanzu ‘yan Nijeriya da dama na fama da tsadar rayuwa, musamman wajen samun kayan abinci da wasu muhimman abubuwan buƙara na yau da kullum. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri. Mahukunta a bangaren shari’ar sun ce an kama Esmail Fekri a shekarar 2023 yana ƙoƙarin miƙa wa Isra’ila bayanan sirri ne don samun kuɗi. KADSEMA da IOM sun fara tantance ɓarnar da ambaliya ta yi a Kaduna Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila Wannan ne karo na uku a baya-baya nan da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa saboda zargin leƙen asiri ga Isra’ila. A ranar Lahadi, Isra’ila ta ce ta kama wasu ’yan ƙasa biyu da ake zargin suna aiki da hukumar leƙen asirin Iran. Babban alƙalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya bayyana...
      Dan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye 20 sannan ya taimaka wajen zura bakwai daga wasanni 40 da ya buga a duk wasannin da ya buga a kakar wasan data gabata, Lookman ya ci kwallaye 17 kuma ya taimaka wajen zura 10 a kakar wasanni ta shekarar 2023/24. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun kai hare-hare har sau uku kan cibiyoyin leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ma’aikatar hulda da jama’a ta dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta bayyana harin da aka kai kan cibiyoyin leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila a mataki na uku na hare-haren daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na Uku”. Sanarwar ta kuma bayyana cewa: Hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suke kaiwa kan kasar Iran da jijjifin safiyar yau sun nufi yankunan gidajen jama’a ne. Sannan maharan yahudawan sahayoniyyan sun kashe jami’an leken asirin dakarun kare juyin juya hali uku, shahid Mohammad Kazimi, Hassan Mohaqeq, da Mohsin Baqiri. A ci gaba da mayar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi  Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe...
    Iran ta zartar da hukuncin kisa kan jami’an leken asirin Hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya “Mossad” a safiyar yau Litinin A wani gagarumin farmaki da aka kai kan cibiyar leken asirin yahudawan sahayoniyya a cikin kasar Iran, an kama wani mutum tare da yi masa shari’a bisa zargin hadin kai da hukumar leken asirin ‘yan sahayoniyya, bisa tuhumarsa a matsayin maci amana da gudanar da barna a kan doron kasa. An zartar da hukuncin ne bayan kammala shari’ar laifuka da kuma tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke. A cikin wani hadadden aikin fasaha da leken asiri a cikin kasar, an kama Isma’il Fakri a watan Disamban shekara ta 2023 yayin da yake da alaka da hukumar leken asiri...
    A cikin wata wasika mai kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, mai lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wacce aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, na cewa, IGP ya bukaci a mika Bature zuwa gaban wani jami’i, SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis 29 ga Mayu, 2025, domin amsa tambayoyi.   In ba a manta ba, IGP a watan Disamba, 2024 ya ba da irin wannan umarni tare da tura jami’an sa ido na IGP domin su kamo mai magana da yawun Gwamnan Kano tare da kai shi hedikwatar rundunar da ke Abuja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Mahaifin Xi Jinping, Xi Zhongxun, ya taba shaida masa cewa, “Duk irin kololon matsayin da ka kai, kada ka manta da yi wa jama’a aiki tukuru, ka yi tunani game da jama’a, ka yi cudanya da jama’a, kuma ka zama wanda za a iya kusantarsu.” A sakamakon haka, Xi Jinping ya mayar da shawarar mahaifinsa a matsayin alkiblar neman tabbatar da “cikar burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Martanin Iran game da ta’addancin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba a rana ta biyu Ana ci gaba da mayar da martani mai girma na Iran game da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila take kaiwa da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki. ‘Yan mintoci da suka gabata a zaman wani bangare na biyu na “Alkawarin Gaskiya Na 3”, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka kan haramtacciyar kasar Isra’ila. An harba wadannan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki da kuma jiragen sama masu saukar ungulu daga Tehran da sauran garuruwan kasar Iran a matsayin wani mataki na murkushe laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan...
    Iyaye su ne ke ginawa yara dabi’un farko, shi ne ma ya sa a ke so su rika kiyaye irin maganganun da za su rika yi a gaban yaransu, sannan su tsaftace mu’amalolinsu ta yadda yaran ba za su rika kwaikwayon abubuwan da ba su dace ba. hatta da yin dakuwa da nufin zagi, a wurin iyaye yara ke fara koyo. Shi ne ya sa za ka ga wani ya zama gwani a zagi, kwararren gaske. Ba a sama ya samo dabi’ar ba, abin da ya taso ya ga a na yi a gidansu kenan. Wasu kuwa gidansu mutanen kirki ne, don haka ba su iya samun daman kwaikwayon zagi a gida. Daga gida, lokacin da yaro ya fara wayo,...
    Ministan harkokin wajen Omani Badr Albusaidi ya sanar da cewa, ba za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka ba. Yau Lahadi ne aka shirya gudanar da zagaye na gaba na shawarwari a Muscat babban birnin kasar Oman. A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X (tsohon Twitter), Albusaidi ya tabbatar da sokewar, yayin da ya jaddada cewa “diflomasiyya da tattaunawa sun kasance hanya daya tilo ta samun zaman lafiya mai dorewa.” “Tattaunawar Iran da Amurka, wadda aka shirya gudanar da ita a birnin Muscat ranar Lahadin nan, ba za ta gudana a yanzu ba. Tattaunawar diflomasiyyar da aka faro kan shirin nukiliyar Iran, a watan Afrilu a shiga tsakanin masarautar Oman,...
    Yayin da taro na biyu na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya ke kara matsowa, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, sun nuna gamsuwa da hadin gwiwa bisa matsayin koli dake tsakanin Sin da kasashen nan biyar na yankin tsakiyar Asiya, a matsayin wata hadaka ta al’umma mai kyakkyawar makomar bil’Adama, wadda ke kara shigar da sabon kuzari, na daidaito cikin yanayin duniya dake kara shiga yanayin tangal-tangal. Tun dai taro na farko na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen biyar ya shiga wani sabon zango na ci gaba. Har ma kuri’un na jin ra’ayin jama’a suka nuna yadda kaso 90.4...
    A yau Asabar ne kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na lura da yanayin bala’u a doron kasa, wanda ake sa ran zai rika samar da bayanai ga kasar Sin dangane da aukuwar bala’u daga indallahi, ta aikewa da sakwanni tsakanin sararin samaniya zuwa doron duniya. An harba tauraron dan Adam din mai suna Zhangheng 1-02, ta amfani da rokar Long March-2D, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, da karfe 4 saura mintuna 4 agogon Beijing, ya kuma shiga da’irarsa ba tare da wata matsala ba, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta tabbatar. Kazalika, CNSA ta ce, wannan aiki muhimmin mataki ne...
    Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda za’a kubuta daga irin cin fuskar da ake yi kowace rana. Kafin dai a tsunduma sosai cikin lamarin cinikin Bayi, yana da matukar kyau a fara yin bayani kan yadda abin ya fara:Lamarin cinikin Bayi ba manufa bace ta Yammacin Turai.Duk lamarin ya zarce wani hasashen da za’a iya yi ko wani rubutun,da aka yi aka aje.Idan kuma aka duba ta bangaren nahiyar Afirka ita...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike da sako ga al’ummar Iran bayan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar A yammacin jiya ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da sakon ta gidan talabijin ga al’ummar Iran bayan harin ta’addanci na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana a cikin wani sakon da ya aike ta gidan talabijin ga al’ummar Iran cewa: Sojojin Iran za su yi aiki da dukkanin karfinsu, kuma za su mayar da martani kan wannan mugunyar aniya ta ‘yan sahayoniyya kaskantattu marasa tunani da basira. Jagoran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba za su fita cikin wannan aika-aika ba,...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bude kofofin wuta a kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar mayar da martani kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasarta Iran ta bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya a matsayin mayar da martani ga mummunan zaluncin da suka kaddamar kan lardunan Iran da dama, wanda ya yi sanadiyyar shahadan mutane da dama da jikkata. Bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Wajibi ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta jira mummunan hukunci mai tsanani da kuma makoma mai daci kan abin da aikata, kuma bayan da sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran za su bude kofofin...
    Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra. Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya zargi Isra’ila da yin zagon kasa ga diflomasiyya ta hanyar tsallaka jajayen layukan kasar Iran, da kuma ta’azzara rikici da kasashen yammacin duniya, yana mai bayyana cewa, ba za a iya yin shawarwari a halin da ake ciki ba. Sanarwar dai na nuni da koma baya sosai a yunkurin diflomasiyya na Iran da kasashen Yamma, musamman yadda tashe-tashen hankula ke kara ta’azzara bayan matakin sojin Isra’ila. Matakin na Isra’ila da hadin kai tare da Amurka na a matsayin kokari na kawar da duk wata dama ta cimma sakamakon shawarwari. “Ba za a iya shawarwarin ba yayin da a lokaci guda ake barin gwamnatin kisan kare dangi ta kai hari kan Iran.” “Ba...
    Jagoran juyin musulunci na Iran wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojan kasar Iran, ya nada sabbin kwamandoji da maye gurbinsu da wadanda su ka yi shahada. Bayan shahadar kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci Shahid Hussain Salami, da kuma  babban hshahid Muhammad Hussain Bakiri, sai Shahid Gulam Ali Rashid wanda shi ne kwamandan Bakirin soja na “Khatamul-Anbiya, jagoran juyin ya sanar da sunayen wadanda su ka maye gurbinsu. Birgediya Muhammad Pakphur shi ne wanda jagoran ya sanar a matsayin sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci, sai kuma  Manjo Janar Musawi a mastayin sabon kwamandan rundunar sojan kasar, yayin da aka nada janar Ali Shadmani a matsayin kwamandan Barikin soja na Khatamul-Anbiya.
    Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fitar da bayani a yau juma’a da a ciki ya yi wa ‘yan sahayoniya alkawalin fuskantar ukuba mai tsanani. Bayanin na jagora ya kunshi cewa: Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Ya Ku Al’ummar Iran Masu Girma Da safiyar yau, ‘yan sahayoniya sun miko hannuwansu da suke jike da jini, domin tafka laifuka a cikin kasarmu.  Sun kuma sake bayyana hakikanin dabi’arsu mummuna fiye da kowane lokaci a baya,  su ka kai wa  gidajen fararen hula hari. A dalilin haka, wannan haramtacciyar kasar ta saurari sakamako mai tsanani. Su kuma  sani cewa; Sojojin Jamhuriyar musulunci masu karfi ba za su kyale su ba da yardar Allah....
    Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matsayin cin ribar cikakkiyar dimokuraɗiyya ba, duk da cewa an dawo mulkin farar hula shekaru 26 da suka gabata. Yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, Fayemi ya bayyana cewa duk da cewa ana gudanar da zaɓe a kai a kai a ƙasar, har yanzu an rasa muhimman abubuwan da suka kamata su kasance a tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna “Bai kamata mu rikita gudanar da zaɓe da aiwatar da dimokuraɗiyya ba,” in ji shi. “Abin da muka...