Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara
Published: 20th, March 2025 GMT
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana.
A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ta kai ziyara ga jami’an NAMA a Filin Jirgin Sama na Hassan Usman Katsina da ke Kaduna.
A yayin ziyarar, Malam Salihu Abubakar ya yaba wa NAMA bisa gudunmuwar da take badawa wajen nasarar hajjojin da suka gabata, inda ya roƙi irin wannan haɗin gwiwa a bana.
Ya jaddada muhimmancin samun ingantattun hanyoyin sufuri tare da roƙon NAMA ta tabbatar da samar da duk wani kayan aiki da ake bukata domin kauce wa cikas yayin jigilar alhazai.
A nasa jawabin, Manajan Harkokin Zirga-zirgar Jiragen Sama na filin jirgin, Alhaji AbdulMajid Mohammed, ya tabbatar da aniyar NAMA na ci gaba da tallafa wa aikin jigilar alhazan Jihar Kaduna.
Ya bayyana cewar har yanzu akwai matsalar ginin sabon hasumiyar kula da zirga-zirga da ba a kammala ba, yana mai ƙarin bayani cewa yawan katsewar wutar lantarki na kawo cikas, wanda ya sa yanzu filin jirgin ke aiki ne kawai kafin ƙarfe 5 na yamma.
Duk da waɗannan ƙalubalen, Alhaji AbdulMajid ya tabbatar wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai cewa NAMA na da ƙudurinsa na ganin cewa aikin jigilar alhazan Kaduna zai kasance cikin tsari da kwanciyar hankali.
Ya tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin rage yiwuwar samun cikas da kuma tabbatar da nasarar tafiyar Hajjin bana.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Hukumar Jihar Nasara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.
An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”
Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.
“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”
Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.