Sojojin Iran: Gwagwarmaya Ce Kadai Hanyar Warware Matsalar Falasdinu
Published: 27th, March 2025 GMT
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya.
Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi ne ci gaba da gwgawarmaya, sannan kuma da samun goyon bayan al’ummar duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa; A wannan lokacin na jajiberin ranar Kudus,al’ummar Falasdinu suna cikin mawuyacin yanayi na cin zali da nuna karfi akansu da ‘yan sahayoniya suke yi ta hanya mafi muni, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar dubban Falasdinawa da kuma jikkatar wasu dubu dubatar, daga cikinsu da akwai kananan yara, mata da kuma fararen hula.”
Bayanin sojojin na Iran ya yi kira ga dukkanin ‘yantattun mutane a duniya da su fito domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da ake cin zalinsu, tare da kara da cewa, al’ummar Iran ma’abota juyin juya hali za su fito a ranar Kudus ta duniya domin nuna kin jinin zalinci irin na ‘yan sahayoniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin, hukumomi masu kula da harkokin kasa da kasa, kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya, da Majalisar Dinkin Duniya dukkansu sun kasa tilasta musu sauya manufofinsu. Wannan tsarin kasa da kasa, idan mun bar shi haka ba tare da wani sauyi ba, to, wata rana za mu ga an koma tsarin zalunci na zamanin mulkin mallaka, wanda zai yi barazana ga hakkin rayuwa, da raya kai na al’ummar kasashe masu tasowa. Ta haka za mu san cewa gyara ya riga ya wajaba.
Saboda haka, shawarar inganta jagorancin duniya ta zama wani abun dake biyan bukatun dake akwai a duniyarmu. Wannan ya sa ta samun karbuwa a tsakanin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. Inda shahararren dan jarida a Najeriya Lawal Sale, ya rubuta a cikin wani sharhinsa cewa, “Wannan shawara za ta haifar da karin kwanciyar hankali, da tabbas a duniyarmu mai cike da tashin hankali, musamman ma a nahiyar Afirka.” Kana a nasa bangare, Paul Frimpong, wani shehun malami dan kasar Ghana, ya ce shawarar nan “tana tabbatar da cewa tsarin jagorancin duniya ba zai ci gaba da zama karkashin mallakar wasu kasashe masu karfi ba.” Kana dan jaridar kasar Lesotho, Silence Charumbira, ya ce shirin na baiwa kananan kasashe damar zama masu hakikanin ‘yancin kai.
Ta wannan shawara ta inganta jagorancin duniya, za mu iya kara fahimtar halayyar kasar ta Sin. Ko da yake wani yanayin da duniyarmu ke ciki shi ne dishewar tauraron kasashen yamma, amma duk da haka, kasar Sin ba ta neman yin koyi da kasashen yamma wajen yin babakere a duniya. Tana neman gyara, da inganta tsare-tsaren kula da harkokin duniya, ta yadda za ta tabbatar da moriyar dukkan kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, maimakon kafa wani sabon tsari da ya saba wa tsarin kasa da kasa na yanzu. Dalilin da ya sa haka shi ne babban burin kasar Sin ta fuskar diflomasiyya, shi ne kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil’adama, da kokarin tabbatar da ci gaban harkokinsu na bai daya.
Yayin da karin kasashe ke nuna goyon bayansu ga shawarar kula da al’amuran duniya da kasar Sin ta gabatar, tabbas za mu shaida hadin gwiwar karin mutane a duniya don neman wanzar da adalci, abin da zai haifar da damar tabbatar da daidaito da adalci a duniyarmu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp