Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya
Published: 27th, March 2025 GMT
A yayin da ake tunkarar bikin ƙaramar sallah, hankalin Musulmi a ko ina a duniya, ya karkata zuwa ga hidimar wannan rana ta musamman, musamman a fannin ado da sabbin kaya.
A wata ziyarar da Aminiya ta kai babbar kasuwar tufafi da kayan ado ta Kwari da ke Kano, ta tarar da kasuwa cike maƙil da mata da maza, kowanne na ƙoƙarin sayen sabbin kaya.
Kayayyakin da aka fi saya sun haɗa da atamfofi, mayafai, adire, dogayen riguna, leshi, sarƙoƙi, yadi, da sauran kayan ado.
Kasuwanni sun cika maƙil da masu sayayya
A yayin da ya rage saura kwanaki kaɗan a yi sallah, kasuwanni sun cika maƙil, inda jama’a ke shirin sayan sabbin tufafi da za su yi ƙawa da su a ranar.
A kasuwar Kwari da ke Kano, dandazon mata da maza ne suke sayen kayan ado da tufafi da sauransu.
Wasu na sayen atamfofi da mayafai, wasu kuma sun fi mayar da hankali kan dogayen riguna, leshi, sarƙoƙi, da yadi, sai dai tsadar kaya a gefe guda ta sauya shirin da dama daga cikinsu.
Aisha Idris, uwa ce da ta fito domin yi wa iyalinta sayayyar kayan sallah. Ta shirya saya wa kanta sabon kaya guda ɗaya da kuma guda biyu-biyu ga ’ya’yanta mata da maza.
Amma kuma tana shiga kasuwa sai ta tarar da farashin kaya ya yi tsada fiye da yadda ta yi tsammani.
Ta ce: “Da na shiga kasuwa sai na tarar kayan da za a yi yayi ne suka fi yawa. Amma kowanne idan za a saye shi sai an daure.”
A cewarta, yanzu haka dogayen riguna na yara sun kai Naira 19,000 zuwa Naira 20,000, na manya kuma daga Naira 40,000 zuwa Naira 50,000, har ma akwai wasu da suka haura Naira 50,000.
Hijabin da ake kira ‘Matar Gwamna’ shi ma ana sayar da yadinsa kan Naira 2,500, yayin da na ɗinkakke ya kai Naira 15,000.
Takalmin da ake kira ‘Gidan Sarauta’ mai manyan duwatsu kuwa yana tsakanin Naura 14,000 zuwa Naira 15,000.
Aisha Idris ta ce: “Ban iya siya wa kaina komai ba. Sai dai na saya wa ’ya’yana atamfa mai kyau a kan kuɗi Naira 11,000.”
Yadda mata ke shirin caɓa ado da sallahAmina Yakubu, wata matashiya da Aminiya ta tattauna da ita, ta ce tana shirin yin ado da sabbin kaya a sallar bana.
“Sallar bana ta zo da yayi kala-kala daidai da ajin da kike da shi da kuma aljihunki. Ni dai na yi ɗinki, na kuma sayi doguwar riga.”
Ta bayyana cewa ɗinkin da ake yi yayi a bana shi ne ɗinkin ‘Kufta’, wanda ake yi masa ado da duwatsu masu walwali.
Ana fara ɗinkin daga Naira 20,000 zuwa sama, ko da yake akwai wasu da ba su da adon sosai da ake iya samun su a ƙasa da haka.
“Ranar idi kuma yayin hijabi za a yi, don haka na sayi ‘Matar Gwamna’ na adana ina jiran ranar.”
Teloli na cin karensu ba babbakaDuk da koke-koken tsadar kaya, teloli na cin alfanun kasuwar bana, domin suna samun ɗinki sosai fiye da na bara.
Mujahid Sallari, wani tela da muka tattauna da shi, ya ce: “Bana ana ɗinki sosai fiye da bara. Ɗinkin manya kuma ya fi yawa fiye da na yara, musamman ’yan mata.”
Ya ce akwai mata da suke bayar da ɗinki har guda uku zuwa biyar, wanda a shekarar bara ba haka abin yake ba.
Ɗinkin da aka fi yayi a banaMujahid ya bayyana cewa ɗinkin da aka fi yi a bana sun haɗa da Buba, Kaftan da kuma Abaya.
Wasu mata sun fi sayen rigunan Abaya na ƙasashen Larabawa, yayin da wasu ke siyan yadi su ɗinka na gida saboda farashin doguwar riga ya yi tsada.
Me ya sa teloli suka ƙara kuɗin ɗinki?Dangane da koken da aka yi cewar teloli sun ƙara farashi, Mujahid ya bayyana cewa matsalar ba daga wajensu take ba.
“Gaskiya ba ma za a kwatanta farashin kayan ɗinkin bara da bana ba. Tun da azumi ya zo, aka ƙara kuɗin ɗinki.
“Yayin da azumi ya zo sai kuma abin ya ƙara tashi, har zuwa bikin Sallah.”
Ya ƙara da cewa tsadar kayan ɗinkin ita ce ta sa su ma dole suka ƙara farashin aikinsu.
Yadda ake yayin lalle da ƙunshi a sallar banaKwalliyar sallah ba ta cika a wajen mata, idan aka ce babu lalle ko ƙunshi. Kamar kowace shekara wannan sallar ma mata na yi wa gidajen masu ƙunshi da lalle ƙawanya domin kece raini.
A bana, matan sun bayyana cewa lallen ‘salatif’ da fulawa baƙa ne ake yi yayi.
“Ko dai samari sun bayar da kuɗin lalle, ko ba su bayar ba, dole a yi.”
A taƙaice, sallar bana ta zo da sabbin ɗinkuna, hijabai, takalma da adon lalle, duk da cewa farashi ya tashi sosai.
Yayin da mutane ke shirye-shiryen Sallah, kasuwanni sun cika, kayan ado sun mamaye kasuwanni, teloli na warkajaminsu, amma kuma tsadar kaya ta sauya tsarin sayayya.
Waɗanda suka saba sayan kaya masu yawa, yanzu sun taƙaita; wasu kuma sun mayar da hankali kan hijabai da dogayen riguna. Duk da haka, ana sa ran za a gudanar da bikin Smsallah cikin farin ciki da jin daɗi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: abaya Kasuwar Kwari kwalliya Rahoto dogayen riguna bayyana cewa sallar bana tsadar kaya
এছাড়াও পড়ুন:
Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya.
Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar.
Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya“Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar da ‘yan ta’addan Musulmai da ke aikata wannan ta’asar,” in ji Hegseth.
Trump dai ya yi wannan barazanar ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, inda ya ce Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma tana iya “shiga ƙasar da ƙarfin soji domin share ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci.”
“Idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wata tallafi, kuma mai yiwuwa ta shiga wannan ƙasar, ta cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’addan Musulmai masu zafin kishin addini,” in ji Trump.
Ya kuma gargaɗi gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ɗaukar mataki, yana cewa idan Amurka ta kai farmaki “za ta yi shi cikin sauri, da tsananin ƙarfi, da gamsuwa.”
Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya mayar da Nijeriya cikin jerin ƙasashen da za a sanyawa ido, yana zargin cewa “ana yi wa Kiristoci kisan gilla” a hannun ƙungiyoyin Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.
Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.
A cewar mai ba wa Tinubun shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, za a yi ganawa tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Trump “a cikin kwanaki kaɗan masu zuwa” domin tattaunawa da warware wannan saɓanin fahimta.