Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci da aka kai a wani masallaci a kudu maso yammacin Nijar
Published: 23rd, March 2025 GMT
Iran, ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a wani masallaci a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa masallata.
Akalla mutane 44 ne suka mutu yayin da 13 suka jikkata a harin da aka kai a kauyen Fonbita da ke cikin kauyan Kokorou dake jihar Tillabery wanda ya faru a lokacin da wasu ‘yan ta’addan na kungiyar Da’ish a yankin Sahara (ISGS) suka far wa masallacin, inda suka auka wa masu ibada dake sallar Juma’a.
Baghaei ya bayyana cewa, wannan ta’addancin da aka aikata a lokacin sallar Juma’a ya saba wa ka’idar Musulunci, kuma ya saba wa dukkanin ka’idojin shari’a da hakkin dan Adam na kasa da kasa.
Kakakin na Iran ya jaddada muhimmancin kara inganta hadin gwiwa a matakai daban-daban na shiyya-shiyya da na kasa da kasa don dakile da yaki da ta’addanci.
Ya zama dole a gurfanar da masu hannu a harin ta’addanci da kuma hukunta su.
Baghaei ya nuna juyayi ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su da gwamnati da kuma al’ummar Nijar kan harin ta’addanci.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harin ta addanci
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu.
Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara.
A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata.
A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama.
Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.