Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi
Published: 23rd, March 2025 GMT
A kokarin Gwamnatin Jihar Jigawa na karfafa ayyukan noman rani tare da samar da wadataccen abinci da inganta rayuwa, ta kaddamar da shirin noman rani na Lallashi da ake amfani da rijiyoyin burtsatse a Karamar Hukumar Maigatari ta jihar.
Rahoton na nuna cewa, an yi aikin ne domin canza salon noman rani da sauran ayyukan noma a yankunan da galibi hamada ce.
A cewar rahoton, wannan shiri ana yin amfani da makamashin hasken rana da kuma amfani da na’urori masu rahusa tare da dabarun noman rani don samar da harkokin noman rani mai inganci cikin sauki.
Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a NijarDa yake jawabi a lokacin kaddamar da aikin, Gwamna Umar Namadi ya bayyana muhimmancin aikin, inda ya bayyana hakan a matsayin wata hanya ta jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin an samar da abinci mai yalwa da samar da hanyoyin rayuwa mai dorewa da rage radadin talauci a tsakanin al’umma.
Ya kuma bayyana cewa, babban abin da gwamnatinsa ta sanya a gaba shi ne na cimma manufofin kudirorinta 12 wajen amfani da hanyoyin noma na zamani a Jihar Jigawa, musamman ta hanyar gudanar da ayyukan noma a duk shekara.
Ya kara da cewa, gwamnatinsa na daukar matakai daban-daban don gyara da fadada wuraren noman rani a fadin jihar da suka hada da samar da madatsun ruwa da rijiyoyin burtsatse na yau da kullum.
Sai dai an bayyana cewa shirin noman na Lallashi da rijiyar burtdatse ya kunshi gonaki hekta 10 kuma yana samun tallafin manyan rijiyoyin burtsatse irin na masana’antu guda hudu, kuma ya zuwa yanzu, manoma sama da 80 ne ke cin gajiyar shirin kai-tsaye, wanda ake sa ran zai bunkasa noman sosai da kuma yaukaka tattalin arziki.
Da yake jawabi a madadin manoman yankin, malam Aliyu Musa ya bayyana cewa, abin da gwamnati ke yi wa al’ummomin da ke kewayen wurin noman rijiyoyin burtsatse tamkar jari ta bayar na rayuwa da ba za a iya tantance adadinsa ba.
A cewarsa, jama’a za su ci gaba da addu’o’in samun nasarar shirin tare da fadada shirin domin kara fadada shi a yankunan jihar gaba daya.
“Da farko mutanen wannan yanki suna yin noman rani ne da zarar lokacin damina ya kare, amma labarin ya canza a yanzu, wanda ke nufin ba za a bar kauye zuwa birni ba don ci-rani.
“Nan ba da dadewa ba birni zai zo gare mu, yayin da muka fara nazarin wannan dama mai albarka ta tashi a matsayin al’ummomin da ke da wuraren noman rani,” inji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Jigawa Malam Umar Namadi
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
Daga Usman Mohammed Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Injiniya (Dr.) Muhammad Uba, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da sabbin ayyukan gina hanyoyi a fadin jihar, ciki har da na Birnin Kudu.
Ya ce wannan mataki na cikin ajandar gwamnati 12, musamman wajen inganta ci gaban ababen more rayuwa.
A cewarsa, Birnin Kudu za ta amfana da gina hanyoyi masu tsawon kilomita 113, wanda ya hada da hanyoyin kauyuka da wadanda ke hada al’umma da sauran sassan jihar.
Dr. Uba ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen saukaka zirga-zirga, inganta harkokin tattalin arziki da samun sauki ga muhimman ayyuka ga jama’a.
Ya bayyana tabbacin cewa za a dade ana cin moriyar aikin hanyoyin, tare da hanzar ayyukan ci gaba da bunkasar karamar hukumar.
Shugaban ya yi addu’ar dorewar zaman lafiya da cigaba a Birnin Kudu tare da yin alkawarin ci gaba da hada kai da gwamnatin jiha domin tabbatar da cewa jama’a suna amfana da fa’idodin dimokuraɗiyya.