Mutumin da girgizar ƙasa ta razana ya shekara 2 yana zaune a cikin kogo
Published: 23rd, March 2025 GMT
Wani ɗan ƙasar Turkiyya da ya rasa gidansa sakamakon wata gagarumar girgizar ƙasa a shekarar 2023, ya shafe shekara biyu yana zaune shi kadai a cikin wani ƙaramin kogo saboda yana ganin ya fi kowane gini da mutum zai yi karko.
A watan Fabrairun 2023, Kudancin Turkiyya ya fuskanci ibtila’in girgizar kasa mai karfin 7.
Ali Bozoğlan, mahaifin ‘ya’ya uku daga lardin Hatay da ke kudancin kasar, ya rasa gidansa sakamakon girgizar kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu 2023.
Duk da cewa shi da iyalinsa sun tsira ba tare da wata matsala ba, Ali ya firgita da girgizar kasar har ya yanke shawarar ba ya son zama a ginin da mutum ya yi.
Maimakon haka, sai ya sami wani karamin kogo da zai iya zama lafiya a wajen birnin, inda ya mayar da shi gida.
Kodayake ya kasa shawo kan iyalinsa su hadu da shi don zama a cikin kogon da ba a saba gani ba, sai dai ya yi ikirarin cewa yana farin ciki kuma yana cikin kwanciyar hankali a inda yake.
Ali Bozoğlan ya shaida wa kafar yada labarai ta TGRT Haber cewa, “Na shafe shekara 2 ina zaune a nan bayan girgizar kasar kuma na sami kwanciyar hankali a cikin wannan kogon.
“Wannan kogon ya wanzu tsawon dubban shekaru kuma bai rushe ba.”
Bayan da an samu labarin yadda mutumin yake rayuwa, sai Hakimin Defne ya ba shi wata kwantenar gida mai kyau a wani wuri kusa da birnin, amma Ali ya so ya nisantar da kansa da birni mai cike da cunkoson jama’a, domin ya saba da rayuwar kwanciyar hankali a cikin karamin kogon nasa.
“Ina wanke kwanukan abincina da yin wanki da kuma yin abincin da zan ci. Ina yin kyakkyawar rayuwa a cikin kogon,” in ji Ali.
“Ba ni da kowa kuma ina hulda da yanayi. Mutanen da ba su da ilimi suna yin munanan maganganu game da rayuwata a cikin kogon.
“Domin ba sa zama da ni, suna magana da ni, kuma ba su san ni ba, suna yin kalamai daban-daban.”
Ali ya yarda cewa zama shi kadai a cikin kogo bai dace ba. Domin wuri ne mai zafi sosai a lokacin hunturu da sanyi da rani, yana jawo macizai da beraye, amma duk da haka ya saba da shi.
Haka kuma ya so ya sami ya rika shiga bandaki da samun ruwan sha, amma ba zai yiwu ba.
Yanzu ya shirya saka na’urorin samar da lantarki ta hasken rana domin ya iya sarrafa injin wanki da firinjinsa, amma ko da mafarkinsa bai zama gaskiya ba, ba zai yi watsi jin dadin kogon nasa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Girgizar kasa Turkiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani
Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba suna cewa ba za su gudanar da tattaunawa ba ne, amma tattaunawar dole ta kasance ta gaskiya
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rashin gindaya sharaɗi ba.
Da yake jawabi a wani taron masana ilimin bil’adama a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ‘yan kwanaki da suka gabata, Larijani ya bayyana cewa: “Hanya madaidaiciya ta gyara halayen makiyansu tana cikin ƙarfafa haɗin kan ƙasa, kuma tushenta shine gyare-gyaren tattalin arziki da dawo da kwanciyar hankali ga rayuwar mutane.”
Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rangwame kan hakki ba gami da rashin gindaya sharaɗi ba, yana mai ƙarawa da cewa: “Mutanen da suka amince kan wajabcin inganta sinadarin Uranium, yanzu suna cewa bai kamata Iran ta yi ba; su masu neman duk wata dama ce kan cimma munanan manufofinsu.”
Larijani ya nuna cewa: Babu ƙarshen buƙatun Amurka, kamar yadda suke cewa: “Bayan hana inganta Uranium, zasu bukaci rage karfin makaman kasar Iran tare da bukatar yin ayyukan kasa kamar yadda suka Sanya ake yi a yankin.” Ya bayyana: “Yana ganin akwai buƙatar juriyar ƙasa kan waɗannan buƙatun, kuma Iran da al’ummar kasarta dole ne su tsaya su kalubalanci duk wata mummunar manufa kansu.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci