Leadership News Hausa:
2025-08-01@05:02:26 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]

Published: 23rd, March 2025 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [15]

● Ta biyu, yana nuna rashin ladabi ga Allah, domin ainihin hassada ita ce jin haushin yadda Allah Ya ba wa wani ni’ima, kuma hakan yana nufin yana sukar hukuncin Allah.

● Ta uku, zuciyarsa tana shan wahala saboda yawan damuwa da baƙin ciki.”

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [14] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [13]

Fashin Baƙi:

Ibn Juzai Allah Ya ji ƙan sa, ya yi cikakken bayani kan illolin hassada ga mai hassada ta hanyoyi guda uku: samun zunubi, da rashin ladabi ga Allah, da wahalar da zuciya.

Zan ɗan yi bayani a kan waɗan gaɓoɓi guda uku da malam ya ambata, tare da hujjoji daga Alƙur’ani, da Hadisi, da mahangar masana ilimi. Ga maganar kamar haka:

Hassada Zunubi Ce Kuma Haramun Ce a Shari’a:

A Musulunci, hassada tana daga cikin manyan zunubai. Dalili kuwa shi ne cewa tana ƙunshe da ƙiyayya da kishi mara dalili. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:” Shin yanzu za su riƙa yi wa mutane hassada ne a kan abin da Allah Ya ba su na falalarsa?” Suratun Nisã’i aya ta 54. Ma’anar wannan aya ita ce: idan mutum yana jin haushin wani saboda wata ni’ima da Allah Ya ba shi, to yana fuskantar hukuncin Allah da kishi maras tushe. Haka nan Annabi (SAW) ya fadi a cikin hadisi cewa: “Kada ku yi hassada“ Bukhari da Muslim ne ya ruwaito.

Me Yasa Hassada Take Zama Zunubi?

Hassada ta zama zunubi ne ta fuskoki masu yawa.

• Akwai saɓa wa Allah da Manzonsa (S.A.W) na hani a kan hassada.
• Hassada tana sa mutum ya yi mummunan zato ga Allah, yana ganin kamar bai dace Allah Ya ba wani wata ni’ima ba.
• Hassada tana iya sa mutum ya aikata mugun aiki, kamar cutar da wanda yake yi wa hassada.
• Hassada tana hana mutum mai da hankali kan nasararsa, tare da an giza shi yana riƙa jin haushin wasu maimakon yin aikin da zai amfane shi.
• Hassada tana hana mutum gode wa Allah da abin da yake da shi.

Mafita:
Maimakon haka, Musulunci ya na koyar da yin gibḍa (kishi mai kyau), wato yin burin yin abin da wani yake yi ba tare da fatan sharri gare shi ba. Misali, idan mutum yana ganin wani ya fi shi ilimi, maimakon yin hassada, yana da kyau ya yi addu’a Allah Ya ba shi ilimi kamar nasa.

Hassada Rashin Ladabi Ce Ga Allah:

Idan mutum yana jin haushin yadda wani ya samu wata ni’ima, hakan yana nufin yana ƙin hukuncin Allah ne. Wannan kuwa yana iya jefa mutum cikin shakka ko rashin yarda da Allah. Allah Ta’ala Ya ce a cikin Alƙur’ani: ”Kuma Allah Yana bayar da mulkinsa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai Yalwa ne, Masani” Suratul Baƙara aya ta 247.

A ma’anar wannan aya ita ce, Allah ne yake rarraba arziki, da ilimi, da kyau, da sauran ni’imomi ga wanda Ya ga dama. Idan mutum yana jin haushin wannan, to yana sukar hukuncin Allah ne. Misali a rayuwa, Idan mutum yana jin haushin wani saboda yana da dukiya, wannan yana nuna cewa bai gamsu da yadda Allah ke bayar da arziki ba. Idan mutum yana jin haushin wani saboda yana da kyau ko hikima, yana nufin yana ƙin tsarin Allah ne. Hassada tana sa mutum ya yi tambayoyi marasa amfani, kamar:

○ Me yasa Allah Ya ba wane, amma ni bai ba ni ba?”
○ Me yasa ni ban samu kaza ba alhali na fi shi ƙoƙari?
Waɗannan tunani suna iya jefa mutum cikin gaba da ƙaddara, wanda hakan yana daga cikin munanan al’amura a Musulunci da suke taɓa imanin bawa.

Hassada Tana Jefa Mai Yi Cikin Wahalar Zuciya da Damuwa:

Baya ga kasancewar hassada zunubi, hassada tana cutar da zuciyar mai yi. Wannan yana da nasaba da ilimin halayyar dan ɗan’adam (wato psychology), wanda ya tabbatar da cewa hassada tana jefa mutum cikin damuwa da ciwon zuciya.

Yadda Hassada Take Hana Jin Daɗi:

Hassada tana hana mai hassada jin daɗi ta fuskoki masu yawa da suka haɗa da:

● Mai hassada yana rayuwa cikin baƙin ciki, saboda yana kallon wasu yana jin haushinsu.
Yana cike da damuwa, saboda yana son a cire wa wani wata ni’ima a maimakon ya mai da hankali kan kansa.
● Mai hassada yana ƙin farin cikin wasu, idan wani ya yi nasara, sai ya ji haushi a maimakon ya taya su murna.

Ga Wa su Misali a Rayuwa:
1. Idan mutum yana jin haushin wani saboda ya sami aiki, yana iya shafe kwanaki yana tunanin hakan a maimakon neman na kansa.
2. Idan mutum yana jin haushin abokin karatunsa saboda ya fi shi kyau, yana iya jin ƙunci da matsin lamba a maimakon ƙoƙarin kyautata halinsa. Allah Ya tsare mu daga hassada, Ya sa mu kasance cikin masu gode Masa da kyawawan halaye! Amin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan Idan mutum yana jin haushin wani saboda a Allah Ya ba saboda yana wata ni ima

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa.

Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne.

Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres

Lamarin ya faru ne da ranar yammacin Lahadi, 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwalen ya taso daga ƙauyen Digawa a Ƙaramar Hukumar Jahun zuwa ƙauyen Zangon Maje da ke Ƙaramar Hukumar Taura.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.

Ofishin NEMA na Kano, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin.

Wasu mazauna yankin sun ceto mutum takwas da ransu, sai dai an yi rashin sa’a mutum tara sun riga mu gidan gaskiya.

NEMA tare da haɗin gwiwar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (JSEMA), Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIWA), da jami’an Ƙaramar Hukumar sun wayar da kan al’umma kan muhimmancin bin ƙa’idojin tsaro yayin tafiya a ruwa.

NIWA, ta kuma raba wa mutanen yankin rigunan kariya na ruwa don kare kansu daga irin wannan hatsari.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kare Ya Ciji Tsohon Ɗan Wasan Barcelona A Mazakuta
  • Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
  • Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya
  • Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Wani mutum ya mutu yayin raba faɗar ma’aurata