Amurka ta cire tukuicin wanda ya bayar da bayani kan mataimakin shugaban Taliban
Published: 23rd, March 2025 GMT
Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida.
A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar da lada na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, tare da bayyana Haqqani a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka dangane da matakin.
Haqqani shi ne shugaban kungiyar Haqqani, wata kungiya mai karfi a cikin kungiyar Taliban wacce ta shahara wajen ayyukanta da makamai.
Duk da ayyana shi a baya a matsayin “dan ta’adda na duniya” da Amurka ta yi, Haqqani ya rike babban matsayi a cikin gwamnatin Taliban, inda aka dora masa alhakin kula da tsaron cikin gida na Afghanistan.
Kasancewar sa a cikin gwamnatin ya kasance wani batu ne da ake ta takun saka tsakanin ‘yan Taliban da gwamnatocin kasashen yammacin duniya, wadanda ke ci gaba da kakaba takunkumi tare da kin amincewa da mulkin kungiyar a hukumance.
Zargin cire ladan ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar Taliban ke kokarin ganin ta samu halacci a fagen kasa da kasa, a yayin da take kokarin kulla huldar diflomasiyya, da sakin kadarorin babban bankin Afganistan da Washington ta rike, da kuma rage takunkumin hana tafiye-tafiye a kan jami’ansu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: “Ba ma wasa game da batun inganta uranium, wanda hakkin al’ummar Iran ne”
Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba.
Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba.
Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani.
Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka.
Ministan ya jaddada cewa Iran na daukar tace sinadarin Uranium a matsayin wani hakki na kasa wanda ba za’a iya tauye mata ba, kamar yadda yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta tanada.