Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Ondo Da Shugaban Masu Rinjaye Sun Yi Murabus
Published: 3rd, June 2025 GMT
Wasu kuma sun ce akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan da mahaifinsa, Oba Akinruntan.
Bayan saukar Akinruntan, an zaɓi Ololade Gbegudu daga Okitipupa a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.
Gbegudu, mai shekara 42, ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin tsaro da ci gaban al’umma a majalisar kafin wannan sabon muƙamin.
Oluwatoyin James daga Akoko ta Arewa Maso Gabas ne, ya ayyana sunansa, yayin da Chris Aiyebusiwa daga Okitipupa I ya mara masa baya.
Haka kuma, tsohon jagoran majalisar, Ogunmolasuyi daga Owo I, ya sauya wajen aiki da Olatunji Oshati daga mazaɓar Ose, wanda yanzu shi ne sabon shugaban masu rinjaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Murabus
এছাড়াও পড়ুন:
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027.
Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar na da alaƙa da burinsa na ganin an samu shugabanci na gaskiya da riƙon amana a Najeriya.
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wutaA wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ziyararsa ta musamman zuwa Ibadan na da nufin girmama Rashidi Ladoja, wanda aka naɗa a matsayin Olubadan, da kuma jaddada muhimmancin Ibadan a siyasa, zamantakewa, da tattalin arzikin ƙasar.
“Na kai ziyara don girmama sabon Olubadan, Rashidi Ladoja, wanda ƙwarewarsa a matsayin tsohon sanata, gwamna, kuma attajiri za ta taimaka wajen ɗaga martabar Ibadan,” in ji Obi.
Ya ƙara da cewa tattaunawarsa da Obasanjo da Ladoja na da nasaba da ci gaban Najeriya da kuma shugabanci da ke da burin sauya al’umma ta fuskar gaskiya da adalci.
Ziyarar Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ake hasashen zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.