Leadership News Hausa:
2025-06-03@03:02:06 GMT

‘Yan Wasan Da Tauraruwar Ronaldo Da Messi Ta Hana Su Haskawa

Published: 1st, June 2025 GMT

‘Yan Wasan Da Tauraruwar Ronaldo Da Messi Ta Hana Su Haskawa

Haka kuma an yi zaratan ‘‘yan kwallo irin su Johan Cruyff da Eusébio da Gerd Müller mahaifin Muller na yanzu da Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil da sauransu amma tabbas ba a samu zazzafar muhawara ba saboda bbau kafafen sadarwa na zamani wadanda yanzu kusan su ne suka hura wutar zazzafar muhawarar a sassa daban-daban na duniya da ake Kallon kwallon kafa.

A yanzu dai Messi ne ya fi lashe Ballon d’Or, inda yake da guda takwas: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021 da 2023, sai Cristiano Ronaldo mai guda biyar: 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017. Sannan Messi ya zo na biyu sau biyar, shi kuma Cristiano Ronaldo ya zo na biyu sau shida, sannan dukkansu sun zo na uku sau daya. Hakan ya sa ake ganin kamar ‘yan wasan biyu sun hana wasu fitattun ‘yan wasan yin rawar gaban hantsinsu.

Andrés Iniesta

Andrés Iniesta dan wasan kasar Spain ne da ya yi tashe tare da Dabi da Messi a Barcelona, inda suka lashe kofuna da dama. A lokacin da yake tashe tare da Dabi da Boskuets, sai da ya zama ana ganin babu kungiyar da take da ‘yan wasan tsakiya kamar Barcelona kuma sun taimaka wajen lashe kofuna da dama a Spaniya da Barcelona. Tsohon dan wasan mai

shekara 40 a yanzu, bayan Barcelona ya koma kungiyar Vissel Kobe ta Japan daga shekarar 2018 zuwa 2023, sannan ya koma Emirates ta Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya yi shekara daya kafin ya yi ritaya.

Sannan ya lashe kofuna da dama ciki har da zakarun turai ta kofin duniya da ya lashe a shekarar 2010 a kasar Afirka Ta Kudu. A shekarar 2010 ce aka yi tunanin Iniesta zai lashe kambun bayan Spain ta lashe gasar cin kofin duniya amma bai samu nasara ba, sannan a shekarar 2012 da Spain ta lashe gasar cin kofin Nahiyar Turai ta biyu a jere aka sake yin tunanin zai lashe, amma nan ma bai samu nasara ba. Duk da haka an yi amannar Iniesta gwani ne musamman wajen rarraba kwallo da murza ta yadda yake so.

Zlatan Ibrahimobić

Zlatan Ibrahimobić, wanda aka haifa a ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 1981, fitaccen dan wasan kasar Sweden ne, wanda ya yi shekaru yana jan zarensa wajen zura kwallaye a raga. Yana cikin ‘yan wasan gaban da ake ganin sun kware a duniyar kwallo, inda ya lashe kofuna guda 34 a zamaninsa kuma ya zura kwallaye guda 570, ciki har da sama da kwallaye guda 50 a kungiyoyin da ya bugawa wasa.

A shekarar 2022, Zlatan ya ce bai lashe kambun ba ne saboda yana bayyana ra’ayinsa a kan komai daidai da yadda ya fahimta, inda ya bayyana a wata tattaunawarsa da Bild da kafar Goal.com [1] ta ruwaito cewa, “akwai siyasa a wajen bayar da kyautar nan. Matukar kana bayyana ra’ayinka, ba za ka samu ba.”

Neymar Jnr

Neymar da Silba Santos Júnior dan wasan kasar Brazil ne da aka haifa a ranar 5 ga watan Fabrairun 1992. Lokacin da tauraron dan wasan ya fara haskakawa, musamman wajen iya buga kwallo da zura kwallaye a raga, sai aka fara tunanin an samu magajin Messi da Ronaldo kuma da farko an ga alamun hakan kafin daga baya abubuwa da dama su faru da suka sanya ya kwanta dama.

Yanzu haka shi ne dan kwallon da ya fi zura kwallaye a tarihin kasar Brazil, duk da zaratan ‘‘yan kwallon da asar ta fitar a baya. Sau tara dan wasan yana shiga cikin sahun ‘yan takarar lashe kyautar amma bai samu nasara ba, sannan a shekarar 2015 da 2017 da aka fi tunanin zai lashe, sai duk ya kare a na uku.

Hazard

Eden Michael Walter Hazard dan kwallon kasar Belgium ne da aka haifa a ranar 7 ga watan Janairun 1991. Dan wasan ya yi tashe matuka musamman a lokacin da yake kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ma tawagar kasarsa ta Belgium saboda a lokacin ana masa kallon daya daga cikin zaratan ‘‘yan kwallon da aka yi a zamanin nan saboda kwarewarsa wajen iya buga kwallo.

Sai dai tauraronsa bai haska ba bayan ya koma kungiyar Real Madrid, wanda aka yi zaton shi ne zai maye gurbin Cristiano Ronaldo. Ya lashe kyaututtuka da dama ciki har da gwarzon matashin dan kwallo sau biyu da gwarzon dan kwallon gasar Premier League, sannan ya lashe gasar ta Premier da sauran kofuna a lokacin zamansa a kungiyar Chelsea da ke kasar Ingila.

Wesley Sneijder

Shima dan wasa Wesley Sneijder dan wasan tsakiya ne na kasar Netherlands, wanda ya yi fice wajen iya rarraba kwallo da zura kwallon a raga daga tsakiyar filin wasa. Ya buga kwallo a kungiyoyin Ajad da Real Madrid da Inter Milan da Galatasary. A shekarar 2010 ce ya kasance cikin ‘yan wasan da suka fi nuna bajinta wajen jagorantar kungiyar Inter Milan ta lashe gasar Zakarun Turai, sannan kasarsa ta Holland ta zo ta biyu a gasar kofin duniya, wanda hakan ya sa aka yi tunanin zai iya lashe kambun Ballon d’ Or amma a karshe sai ya kare a na hudu, inda Messi ya lashe kambun a shekarar.

Dabi Hernández

Gogaggen dan wasa Dabi Hernández, tsohon dan wasan tsakiya ne na kasar Spain, wanda ya fi yin fice a zamanin da yake buga wasa a kungiyar Barcelona, kungiyar da daga bisani ya horar da ‘yan wasanta. Duk wata nasara da Messi ya samu, tare suka samu da Messi da Iniesta, inda suka yi kusan shekara bakwai suna kaka-gida a harkar kwallon kafa ta kungiyoyi a duniya. Dabi ya lashe gasar La Liga biyar da Copa del Rey uku da zakarun turai biyu da sauransu a Barcelona. Sannan ya lashe gasar cin kofin nahiyar turai sau biyu a jere da kofin duniya da kasar Spaniya.

A shekarar 2009 ya shiga ‘yan takarar kyautar su uku, inda Messi ya doke su da shi da Cristiano, sannan a shekarar 2010 da 2011 ma ya shiga cikin mutum uku na karshe, amma bai samu nasara ba.

Robert Lewandowski

Dattijon dan wasa Robert Lewandowski, dan wasan kasar Poland ne da a yanzu yake buga wasa a kungiyar Barcelona ta Spain. Dan wasan gaba ne da ya kware wajen zura kwallo a raga. Zuwa yanzu ya zura kwallo sama da guda 700 a wasannin da ya buga wa kasarsa da kungiyoyin da ya wakilta, kuma har yanzu yana ci gaba da jefa kwallaye.

A shekarar 2020 ce aka yi tunanin dan kwallon zai lashe kyautar, amma annobar Cobid-19 ta hana shirya bikin.

Amma duk da haka ya ci gaba da nuna bajinta bayan an dawo daga kullen annobar, amma sai Messi ya doke shi waje lashe kyautar a shekarar 2021, inda aka ba shi kyautar wanda ya fi zura kwallaye, lamarin da ya matukar haifar da muharawa a tsakanin masu kallo saboda ana ganin ya kamata a bashi saboda shekara ta 2020 ba a gudanar da bikin ba saboda annobar Korona.

Griezmann

Dan wasa Antoine Griezmann wani fitaccen dan kwallon kafa ne da ya yi tashe sosai, amma bai taba lashe kambun na gwarzon dan kwallon ba. Dan wasan gaba ne na tawagar kasar Faransa da a yanzu yake kungiyar Atletico Madrid ta kasar Spaniya. Ya lashe kofuna da dama, ciki har da kofin duniya da wasu kofuna da daman gaske da ya lashe a kungiyoyin da ya wakilta da kasar Faransa. A shekarar 2016 ce aka fi yin tunanin zai lashe kambun, amma ya zo na uku bayan Messi da ya lashe, da Cristiano Ronaldo da ke biye masa.

Franck Ribéry

Gwarzon dan wasan duniya Franck Henry Pierre Ribéry tsohon dan wasan kasar Faransa, sannan ya buga kwallo a kungiyoyi da dama, amma ya yi fice a zamaninsa a Bayern Munich.

A kyautar ta shekarar 2013 ce aka yi zaton dan wasan zai lashe, amma sai ya zo na uku, inda Cristiano Ronaldo ya lashe, Messi ya zo na biyu. Amma ya lashe kyaututtuka da kofuna da

dama, ciki har da gasar Bundesliga da ya lashe guda tara da sauransu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: bai samu nasara ba dan wasan kasar a shekarar 2010 A shekarar 2010 ya buga kwallo zura kwallaye kwallon kafa kofin duniya ciki har da lashe gasar dan kwallon da ya lashe

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Wasan Kano Sun Rasu Sanadiyar Hadarin Mota Yayin Dawowa Daga Gasar Wasanni Ta Kasa

Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata,  sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta.

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa motar da ke ɗauke da ‘yan wasan, wadda ke ɗauke da mutane 30, ta faɗa gadar ta Dakatsalle da ke jihar ta Kano.

“Yayin da nake magana da ku yanzu, mun kirga gawarwaki 19,” ya fada cikin tashin hankali.

Ado Salisu, tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida da ke kula da lamuran Wasanni ta Najeriya (SWAN), ya ce an kai waɗanda suka jikkata babban asibitin gwamnati da ke Kura.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai ɗan Salisu Jegu, ɗan jarida a fannin wasanni na gidan rediyon Express Radio.

Daga Khadijah Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sanatocin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar ‘Yan Wasan Kano
  • Nijeriya Ta Lashe Gasar Unity Cup Bayan Doke Jamaica A Bugun Fenarati
  • Gwamnonin Najeriya Sun Bayyana Alhininsu Bisa Rasuwar ‘Yan Wasan Kano
  • Ƙungiyar Gwamnoni Sun Yi Ta’aziya Kan Rasuwar Ƴan Wasan Kano 21
  • Mutane 20 sun rasu a hatsari motar ’yan wasan Jihar Kano
  • ‘Yan Wasan Kano Sun Rasu Sanadiyar Hadarin Mota Yayin Dawowa Daga Gasar Wasanni Ta Kasa
  • Ahmed Musa Ya Angwance Da Matarsa Ta 4 A Kano
  • Unity Cup: Yau Nijeriya Za Ta Buga Wasan Ƙarshe Da Ƙasar Jamaica
  • Jami’ar Jos Ta Samu Lambobin Zinare 14 A Gasar NUSSA, Yayin Da FUT Daura Ta Lashe Kofin Kwallon Kafa