Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Yankunan Kasar Siriya Tare Da Kafa Wuraren Bincike
Published: 1st, June 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake yi kutse cikin garin Al-Qunaitra na kasar Siriya tare da kafa wurin bincike lamarin da ya fusata al’ummar yankin
Sojojin mamayar Isra’ila da suka sake yin Kutse cikin yankunan kasar Siriya sun gudanar da sintiri a yankunan tare da kafa shingen binciken ababan hawa tsakanin Khan Arnabeh da kauyen Jaba da ke lardin Quneitra.
A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya, sojojin mamayar Isra’ila biyu kuma sun kutsa kai a tsakanin garuruwan Jaba da Khan Arnabeh, kusa da tsohon wurin binciken ababan hawa na Al-Saqri. Sun samu rakiyar motocin sojoji dauke masu rakiya kusan 20.
Sojojin suna gudanar da binciken motocin ne domin neman makaman da ke iya zama barazana ga tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila, lamarin da ya janyo cece-ku-ce tsakanin jama’a da bullar fargabar cewa: Wannan mummunan ci zarafi kan kasar Siriya zai iya ci gaba da janyo tada zaune tsaye.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Siriya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.