Nijeriya Ta Lashe Gasar Unity Cup Bayan Doke Jamaica A Bugun Fenarati
Published: 1st, June 2025 GMT
Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup ta bana da ta kunshi kasashen Ghana, Trinidad And Tobago, Jamaica da Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta sanar da cewa a ’yan kwanakin nan za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a wasu jihohi da ke sassa daban-daban na ƙasar.
Hakan na kunshe cikin hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025 da hukumar ta fitar.
Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’a An nada ’yar Najeriya a Kwamitin Nukiliya na Majalisar Dinkin DuniyaNiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa.
A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama.
Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, an samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sakkwato da Kaduna.
Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar kasar kamar Abuja da Neja da Filato da Nasarawa da Benuwe da Kogi su ma za su samu ruwan sama daga rana zuwa yamma.
Ranar Talata da safe kuma ana sa ran ruwan sama da tsakar rana a Abuja da Kwara da Neja da Filato.
A ranar Laraba da safe kuma, za a samu iska mai ƙarfi da ruwa a Katsina da Kano da Bauchi da Sakkwato da Taraba sannan daga baya za a samu a Yobe da Jigawa da Kaduna da Borno da kuma Kebbi.