Aminiya:
2025-11-02@17:19:56 GMT

Gwamnatin Tinubu na amfani da talauci a matsayin makami — Atiku

Published: 31st, May 2025 GMT

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, da yin “amfani da talauci a matsayin makami” domin juya ’yan Najeriya.

Da yake jawabi a Abuja ranar Asabar a wajen lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, mai taken “Amfani da Talauci a Najeriya,” Atiku ya yi zargin cewa gwamnati tana amfani da matsalar tattalin arziki don sarrafa ’yan kasa.

Ya ce, “Abin da muke fuskanta a halin yanzu a Najeriya shi ne gwamnati tana amfani da talauci a matsayin makami.”

Atiku ya yi nuni da bambancin yanayin rayuwa a yanzu da lokacin ƙuruciyarsa, inda ya  ce a lokacin Kano tana cikin yalwar arziki, ba a saba ganin mutane marasa matsuguni ba.

Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba  ‘’Yan bindigar birni sun karɓe shugabancin Najeriya — El-Rufai

A cewarsa, yanzu lamarin ya canza, ta yadda talauci da rashin tsaro sun kai ga mutane suna barci a kan tituna da kuma karkashin gadoji a cikin birni Kano.

Har ma ya yi iƙirarin cewa an umarci wata hukumar jihar Kano da aka ɗora wa alhakin taimaka wa waɗannan mutane da ta dakatar da ayyukanta.

Atiku ya bayyana shigarsa cikin wata ‘gamayya siyasa’ don yaƙar wannan yanayi, yana mai cewa, “muna cikin wannan haɗin gwiwa don tabbatar da cewa ba za mu bari su ci gaba da amfani da talauci a matsayin makami ba.”

Da yake mai da martani ga kalaman Atiku, Rotimi Amaechi ya danganta ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar da yawaitar talauci.

“Yunwa ba ta san ƙabila da addini ba, kuma gwamnatin yanzu ta sa mutane sun ƙara talaucewa, wanda hakan ya ƙara yawan rashin tsaro da aikata laifuka,” in ji Amaechi.

Tsohon ministan sufurin ya tunatar da ’yan Najeriya cewa ikon ƙarshe yana hannunsu, yana mai kira gare su da su yi amfani da damarsu ta kaɗa ƙuri’a don tumbuke shugabanni idan ba su gamsu ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamnati Najeriya amfani da talauci a matsayin makami

এছাড়াও পড়ুন:

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe.

“Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano October 31, 2025 Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
  • Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai