Majalisar dokokin jihar Zamfara ta mayar da dan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar, Shamsudeen Hassan Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Arewa, bayan da ya nemi gafarar majalisar.

 

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran majalisar Bello Madaro ya raba wa manema labarai a Gusau.

 

A zaman da aka yi, Kakakin Majalisar, Alhaji Bilyaminu Ismail Moriki, ya karanta abin da ke cikin wasikar neman afuwar Basko, inda daga nan ne ya nemi shawarar majalisar ta gamayya inda ‘yan majalisar suka amince da dage dakatarwar.

 

Shugaban majalisar ya jaddada bude kofar majalisar na karbar irin wasikun neman afuwa daga sauran ‘yan majalisar bakwai da aka dakatar, inda ya ce irin wadannan matakai za su ba su damar dawo da su tare da samar da hadin kai a cikin majalisar.

 

Mambobin sun kuma yi masa maraba da komawa zauren majalisar, sannan sun bukaci sauran mambobin da aka dakatar da su yi koyi da ayyukansa domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban mazabarsu da jihar baki daya.

 

A takaitacciyar jawabinsa, Shamsudeen Hassan Basko ya bayyana matukar godiya ga majalisar bisa damar da ta samu ta mayardashi.

 

Basko ya yi alkawarin ci gaba da bin ka’ida, da’a na Majalisar, ya kuma sha alwashin nisantar da kansa daga duk wata kungiya ko yin tasiri da ke yunkurin bata mutunci da ikon majalisar.

 

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Fabrairun 2024 ne majalisar, bayan wani kudiri da shugaban masu rinjaye, Bello Mazawaje ya gabatar, ta dakatar da mambobinta takwas bisa saba wa kundin tsarin mulkin majalisar (Oda 10, Doka ta 9).

 

Matakin ladabtarwar dai ya samo asali ne daga zarge-zargen da ake yi masa, wanda ya hada da shigar karfi da yaji a ofishin magatakarda da zama ba bisa ka’ida ba, da dakile ayyukan majalisa, da kuma gudanar da ayyukan da ake ganin bai dace da ‘yan majalisar ba.

 

REL/AMINU DALHATU.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Zamfara da aka dakatar

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004.

 

Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara
  • Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya
  • Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35
  • Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati
  • Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya
  • Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan.
  • ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa
  • Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal
  • Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba