2025-11-11@07:53:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11405

«da aka dakatar»:

    ’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a. Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.” Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga. “Mun kai wani matsayi da ’yan...
    A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro. Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe a hannun shugabannin yau, za su lalata komai, kuma ba za ku samu gobe mai kyau ba. Ku duba ƙasar Kamaru, shugabanta Paul Biya yana da shekara 92, to me za a ce game da matasan ƙasar?” Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a...
    A kasar Lebanon an sanar da sakin dan tsohon shugaban kasar Libya, Hannibal bisa kudin fansa da sun kai dala 900,000. An tsare dan gidan Kaddafi din ne bisa tuhumarsa da boye bayanai masu alaka da bacewar Sayyid Musa As-Sadr da abokan tafiyarsa, wanda tsohon shugaban kasar ta Libya yake da hannu. Majiyar tsaro da kuma ta shari’a a kasar Lebanon ta bayyana cewa; An saki Hannibal ne bayan da aka kammala dukkanin matakan sharia,sannan aka bai wa gidan kurkukun da ake tsare da shi, umarnin su bude kofa ya fita. Tun a ranar 17 ga watan Oktoba ne dai wata kotu ta amince da a sake shi, bisa cewa zai bayar da dala miliyan 11, sai dai kuma daga...
    A Jiya Litinin an sake bude  gidajen sayar da man fetur  da aka rufe a cikin birnin Bamako saboda killace iyakokin kasar a kungiyar  masu dauke da makamai mai alaka da alka’ida ta yi ta hana shigar da makamashi. Har ila yau an bude wasu makarantun a cikin birnin na Bamako da safiyar jiya Litinin,kamar kamfanin dillancin labarun “AP” ya nakalto. Fiye da tankokin jigilar man fetur 100 ne masu dauke da makaman su ka kone kurmus, tare da kashe mutane da kuma kama matukansu da yin garkuwa da su. A ranar Lahadin da ta gabata ne dai kungiyar tarayyar Afirka ta fitar da bayani na yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki matakin fuskantar masu wuce...
    Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya samu rakiyar Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya miƙa kayan ne a hukumance a ranar Litinin ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, a Bulasa Warehouse da ke kusa da Birnin Kebbi. Sarkin Argungu, wanda ya yi jawabi a madadin Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa wannan kyauta na cikin manufofin Gidauniyar Sarkin Musulmi na inganta ilimi da...
    Shugaban kasar Amurka ya yi wa ma’aikatan filayen jiragen sama masu sa idanu akan sauka da tashin jirage, barazana. Ma’aikatan da suke sanya idanu a cikin hasumiyoyin dake filayen jiragen sama da dama ne a Najeriya su ka dakatar da ayyukansu saboda rufe ayyukan gwamnati da aka yi a kasar, domin ba za su sami albashi ba. Shugaba Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta  “Truth Social” cewa:, Ba ni jin dadin mutanen da ba su yin wani aiki sai korafi,alhali suna sane da cewa za a basu dukkanin hakkokinsu.” Trump ya kuma yi wa ma’aikatan da ba su dakatar da ayyukansu ba alkawalin ba su kyautar kudi Dala 10,000 kowanensu. Rufe ayyukan gwamnatin kasar ta Amurka wanda ake...
    Ƙungiyar Tsofaffin Sojoji ta Najeriya ta bukaci gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen inganta rayuwar mata zawarawan sojojin da suka mutu a bakin aiki tare da ba su goyon bayan da ya dace. Sabon shugaban ƙungiyar a Jihar Bayelsa, Mista Baratuaipre Allison-Alamini, ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan rantsar da shi. Ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari ganin cewa muryar zawarawan sojojin da suka rasu ta isa inda ya kamata, ta yadda za a inganta rayuwarsu da kuma tabbatar da samun tallafin da suka cancanta. Allison-Alamini ya kuma sha alwashin ba da muhimmanci ga walwalar tsoffin sojoji a jihar, tare da gode wa mambobin ƙungiyar bisa yadda suka ba shi amanar shugabanci. Wani mutum ya...
    Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba. Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike. Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da...
    Ganawa a tsakanin bangarorin biyu dai ta mayar da hankali ne akan batutuwan da su ka shafi dauke wa Syria takunkumi, shigar da kungiyar  Kurdawa a cikin sojojin kasar, da kuma alaka a tsakanin Damascuss da Haramtacciyar Kasar Isra’ila. A nashi gefen ministan harkokin wajen Syria As’ad Shaibani ya bayyana ganawar da cewa ta yi kyau, sannan ya kara da cewa an tattauna batutuwa da dama. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi. Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil. Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma  masu rajin kare muhallin na...
    An kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na takwas (CIIE) a yau Litinin, inda aka samu daddale kulla cinikin dalar Amurka biliyan 83.49 a cikin yarjejeniyoyi da aka cimma na shekara guda, wanda adadin da aka samu ya karu da kashi 4.4 cikin dari idan aka kwatanta da na baya kuma ya kai wani sabon matsayi, kamar yadda hukumar kula da bajen kolin na CIIE ta bayyana. Dandalin baje kolin ya kai fadin murabba’in mita 367,000, inda ya jawo hankulan kamfanoni 4,108 daga kasashe da yankuna 138, lamarin da ya karya tarihin yanayin girma da adadin mahalartan na baya da aka gudanar. Baje kolin na tsawon kwanaki shida ya kunshi sabbin kayayyaki, da...
    Zhang Lei, mataimakiyar shugaban sashen yada labaru na kamfanin BaySystems reshen Sin da yankin arewa maso gabashin Asiya, ta kara da cewa, “A cikin shekaru 140 da suka gabata, mu kasance a nan ba mu taba barin ba, ko a lokacin wahala ko a’a. Wannan yana nuna irin kauna da alkawarin da wannan tsohon kamfanin Jamus mai shekaru 100 ke da su ga kasar Sin.” A game da hakan, Frank Hammes, babban darektan kamfanin IQAir na kasar Switzerland ya bayyana cewa, bikin CIIE tamkar dakin gwaje-gwaje ne a gare mu, inda ban da baje kolin sabbin nasarorinmu, muna kuma iya samun martani daga masu sayayya. Shi kuma Mr. Yu Feng, babban darektan kamfanin Honeywell da ke kula da harkokin kasar...
    Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, ta rasu tana da shekaru 89 a duniya. Iyalai sun tabbatar da cewa ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Litinin, bayan fama da doguwar jinya. Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jallo Ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasa kuma Hakimin Shagari, Kyaftin Bala Shagari (mai ritaya), shi ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da aka fitar daga Sakkwato. Sanarwar ta ce: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna baƙin cikin sanar da rasuwar Hajiya Sutura Shehu Shagari, mata ɗaya tilo da da ta rage wa tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa November 10, 2025 Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo November 10, 2025
    Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan Adam da da’irarsu ke kusa da doron kasa, daga cibiyar harba kumbunan kasuwanci ta lardin Hainan dake kudancin kasar.   An harba rukunin taurarin wanda shi ne irinsa na 13, da ya kunshi jerin taurarin dan Adam masu samar da sadarwar intanet ne da misalin karfe 10:41 na safiyar yau Litinin agogon Beijing. An kuma yi amfani da rokar Long March-12 wajen harbawa, inda tuni suka shiga da’irarsu. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo November...
    Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta’annati a Nijeriya EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo mai ɗauke da hoton tsohon gwamnan da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin. Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP Hukumar ta ce tana neman Mista Sylva ne bisa zargin wata badaƙalar kuɗi da yawansu ya kai dala miliyan 14.8. EFCC ta ce tana zargin tsohon gwamnan da karkatar da kuɗin da aka yi niyyar amfani da su wajen gina matatar man fetur a ƙasar. Hukumar ta ce wata kotu ce a Jihar...
    Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da yadda aikin hajjin bana zai kasance dangane da abin da ya shafi kudin kujerar aikin da lokacin da za a rufe karbar kudin maniyyata. Wannan dai ya biyo bayan kulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta 2026 da hukumar ta yi a madadin Najeriya da hukumomin kasar Saudiyya, a lokacin wani biki da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya. Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar. Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da rage kudin kujerar aikin hajji ne, bisa umarnin shugaban ƙasa. Share 0 0 votes...
    Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya ta yi  tsananin gargadi game da kisan da ake yi a El-Fasher dake arewacin Darfur na kasar Sudan, ya bayyana birnin da cewar yana cikin mummunan yanayi da kuma karuwar hare-hare mafi muni  a kwanaki 10 da suka gabata, Yankin El-Fasher yana kasancewa daya daga cikin garuruwan dake fuskantar mummunan yanayi na zubda jinni a fadin kasar Sudan, da kuma rikice-rikicen kabilanci da kai harin kan fararen hula, kuma yana barazanar karuwar rarrabuwar kai a kasar da tsawaita yakin da jawo kashe dubban mutane da kuma raba miliyoyi da gidajensu, Tun a watan aprilun shekara ta 2023  sojojin Sudan da dakarun sa kai na kungiyar RSF suka...
    Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji da aka kai mata. Kakakin yayi suka mai tsananin ga kamalan da shugaban Amurka  yayi dake tabbatar da hujjoji dake nuna cewa yana da hannun dumu dumu wajen kai mata harin soji,  wannan yana daya daga cinkin bayyanannun hujoji  dake tabbata da taka rawar Amurka wajen kai mata hari. Haka zalika ya nuna cewa iran ta mikawa kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya wadannan kalaman...
    Rahotanni sun nuna cewa Afirka ta Kudu ta ce babu abin da zai sauya dangane da rashin zuwan wakilan Amurka taron G20 da take karbar bakuncinsa, bayan da shugaba Donald Trump a karshen makon jiya ya sanar da matakinsa bisa zargin cewa ana take hakkin dan adam a kasar. Sanarwar da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce, mataimakin shugaban kasa JD Vance, wanda ake sa ran zai halarci taron shugabannin kasashen G20 a Johannesburg tsakanin 22 zuwa 23 ga Nuwamba, an soke ta bisa dalilai masu karfi. Trump ya ce, abin kunya ne kwarai da gaske cewa za a gudanar da taron G20 a Afirka ta Kudu, kasar da ta kasance tana cin zalin wasu...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar,  inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba. Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban. Hukumar kula da makamashin nukiliya...
    Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka. Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi. Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya “Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaron Nijeriya daga duk wata barazana da zata kawo ruɗani, da kuma gyara duk wani tarnaki a dangantakar mu da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa, don haka, ƴan Nijeriya su samu nutsuwa,” in ji Idris. Ministan ya ziyarci...
    Bisa goron gayyatar da gwamnatocin kasashen Guinea da Saliyo suka ba shi, Liu Guozhong, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda kuma shi ne mataimakin firaministan gwamnatin kasar, zai kai ziyara kasashen Guinea da Saliyo daga yau Litinin 10 zuwa 16 ga watan da muke ciki.   Sannan, bisa gayyatar shugaban kasar Guinea Mamady Doumbouya, Mr. Liu Guozhong zai kuma halarci bikin kaddamar da mahakar karafa ta Simandou a kasar ta Guinea, a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping. (Lubabatu Lei)   ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Ya Taya Ouattara Murnar Sake Lashe Zaben Shugaban Cote D’Ivoire November 10, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Halarci Bikin Bude...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia. An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP ’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan...
    Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta birnin tarayya (FCT) ta saka ranar 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe da za a biya kuɗin Hajji na shekarar 2026, wanda aka tsara a N7,696,769.76. Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin hukumar a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda jami’in hulɗa da jama’a, Muhammad Lawal Aliyu, ya buƙaci duk masu niyyar zuwa Hajji daga Abuja su bi ƙa’idojin da aka shimfida. An bayyana cewa tabbataccen kuɗin Hajjin ya samu ne bisa ƙayyadadden tsari daga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), sannan duk biyan kuɗin za a yi ne ta hanyar Banki, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, ba tare da karɓar kuɗi a hannu...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanya da kudinta ya kai Naira Biliyan 14 a Karamar Hukumar Malam Madori, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa1 karkashin shirin sabunta kudurori na gwamnatin tarayya wato “Renewed Hope Agenda.” A yayin taron kaddamarwar, an kuma gabatar da sabbin motoci ga shugabannin jam’iyyar APC guda takwas da masu tallata jam’iyyar a mazabar Arewa maso gabashin jihar, wanda Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya dauki nauyi. Wannan mataki na da nufin karfafa hadin kai a jam’iyyar da kuma tallata hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadin jihar. A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar Sanata Ahmed Malam Madori...
      Gasar ta kasa ita ce irinta mafi girma da ta kunshi wasanni daban-daban, kuma an fara ta ne a shekarar 1959. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar  November 9, 2025 Daga Birnin Sin An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa November 9, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025 Manyan Labarai Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya November 8, 2025 Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025
    Maiyaki ya ce, “Gwamna Uba Sani kwanan nan ya ba da izinin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a karkashin rukunoni daban-daban.   “Za a ci gaba da yin hakan a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin inganta harkar lafiya a jihar.”   Maiyaki ya ci gaba da cewa, Gwamna Sani ya fifita harkar kiwon lafiya a gwamnatinsa, inda take gaba-gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5 November 10, 2025 Labarai Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta  November 10, 2025 Labarai Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC November 10,...
    ‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a kauyen ‘Yan Kwada da ke cikin garin Farun Ruwa a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata biyar, ciki har da masu shayarwa. Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ne a yankin a ranar Lahadi da yamma, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi sannan suka afka cikin gidaje da dama, sannan suka tafi da matan. Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno “Na samu labarin cewa, an sace mata biyar, wasu daga cikinsu, masu shayarwa ne...
      Mazauna Millennium City a Jihar Kaduna sun zargi kamfanin wutar lantarki na Kaduna Electric da tilasta musu sanya mita da kuma ƙara farashin wuta ba tare da tuntuba ba. Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da MPH Estate, TUC Estate, Urban Shelter Estate, Yardan Allah Estate, Highfield Estate, Rahusa Estate, Danbushiya, Sabon Gari, Keke da Doka. Mazauna sun bayyana cewa an katse musu wuta na makonni saboda ƙin karɓar mitocin da kamfanin ya kawo. Sun ce matakin Kaduna Electric ya saba da umarnin Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC), wadda ta tanadi cewa dole a tattauna da al’umma kafin a yi canjin mita ko a sauya tsarin biyan kuɗin wuta. Mazauna sun kuma yi ƙorafi cewa kamfanin...
    Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana  mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira       ” Nuna wariya ta kabilanci.” Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.” A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%. Shi dai...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinawa ta sanar da cewa; sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 44 da suke a cikin sansanonin ‘yan hijira mabanbanta a yankin Gaza. Sanarwar ta ce, wannan adadin, yana a karkashin jumillar ‘yan jarida 254 da su ka yi shahada a tsawon lokacin yakin da ya fara daga watan Oktoba na 2023, zuwa watan Oktobar wannan shekarar ta 2025. Kwamitin dake kare ‘yancin aikin jaridar dake karkashin kungiyar ‘yan jaridar ta Falasdinawa, ya ce; Kashe ‘yan jarida da HKI take yi wani shiryayyen tsari ne da ya hada kai hare-hare akan sansanon ‘yan hijira da suke a kusa da asibitoci da sauran cibiyoyin da hukumar ‘yan hijirar Falasdinawa ta MDD, Unrwa take kula da su....
    Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa,  Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar. Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan motar da hakan ya yi sanadiyyar konewarta baki daya. Dama dai ma’aikatar lafiya ta Lebanon din ta sanar da shahadar wasu mutane biyu sanadiyyar hare-hare biyu da Isra’ilan ta kai a kudancin kasar, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Tun da aka tsagaita wutar yaki a watan Nuwamba 2024, HKI take ci gaba da keta ta, ya kai dubbai. A wani labarin daga...
    Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum. Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro. Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe. Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya. Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin”...
    An fara matakin karshe na Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Duniya karo na 26 a Hadaddiyar Daular Larabawa. A cikin yanayi mai cike da ruhi da daukaka, cike da ruhin gasar Alqur’ani, matakin karshe na Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Duniya karo na 26 ta Sheikha Hind Bint Maktoum ta fara, a cewar Al Ittihad.Gasar, wacce Kyautar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Duniya ta Dubai ta shirya, ta fara ne a rana ta farko a hedikwatar kyautar tare da halartar mahalarta maza 11 daga Hadaddiyar Daular Larabawa.Gasar ta kwanaki biyar ta kunshi nau’ikan haddace-rubuce daban-daban, ciki har da 30, 20, 10, 5, 3 da Juz’ 30 na Alqur’ani.Mahalarta sun fito ne daga Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Iran, Mauritania...
    Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.   “A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025...
    ’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa. Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane. “Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar. Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2...
    Pars Today – Kimanin masu jefa ƙuri’a miliyan 1.3 na Iraki sun je rumfunan zaɓe jiya, Lahadi (9 ga Nuwamba). An gudanar da wannan zaɓen na musamman kwanaki biyu kafin babban zaɓen ‘yan majalisar dokoki na Iraki, wanda za a gudanar a ranar Talata ta wannan makon (11 ga Nuwamba). An ci gaba da gudanar da zaɓen har zuwa ƙarfe 6 na yamma agogon ƙasar, bayan haka aka rufe akwatunan zaɓe ta hanyar lantarki. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar da cewa an shirya cibiyoyin zaɓe 809, ciki har da akwatunan zaɓe 4,501, a faɗin ƙasar don ranar zaɓen musamman. A wannan zagayen zaɓen, ‘yan takara sama da 7,744 daga ƙungiyoyin zaɓe 31 sun tsaya takarar kujeru...
    Pars Today – Jakadan Iran a Rasha ya sanar da cewa Tehran da Moscow sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Kazem Jalali, jakadan Iran a Rasha, ya rubuta a ranar Lahadi a dandalin sada zumunta na X cewa an cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Rasha don kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Ya kara da cewa wannan yarjejeniya ta samo asali ne daga tarurrukan da aka gudanar a ranakun 6-7 ga Nuwamba a Makhachkala tsakanin shugabannin tashoshin jiragen ruwa da na ruwa, manyan jami’an gwamnati, da daraktocin manyan kamfanonin kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen biyu. A cewar Pars Today, ya kara da cewa a lokacin wannan taron, an amince da tsarin da tsarin hadin...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi. A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a zaɓen 2027. Abdulmumin Jibrin ya sanar ta shafinsa cewa sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa. “Na samu kyakkyawar tarba daga dubban al’ummar mazaɓata ta Kofa, Bebeji, da ke Jihar Kano. “Taron ya yi ittifaƙin ficewa daga NNPP/Kwankwasiyya, mu koma APC, tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi wa’adi na biyu. An ƙara rage kuɗin aikin Hajjin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi. Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud. Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama  a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko...
    Allah Ya yi wa Hajiya Ɗayyabatu, mahaifiyar Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abas, rasuwa tana da shekara 93. Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da jinya, a gidanta da ke unguwar Bambale da ke birnin Zariya. Ta rasu ta bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci Ana sa ran gudanar da Sallar jana’izarta a safiyar Litinin daina nan da misalin ƙarfe 11, a gidan nata da ke Bambale, Birnin Zariya.
    A taron CELAC na biyar tare da Tarayyar Turai a Colombia, shugabannin Latin Amurka sun yi Allah wadai da karuwar jibge  sojojin Amurka a yankin Caribbean, suna gargadi game da tsoma bakin kasashen waje da kuma yin kira da a hada karfi da karfe wajen kare ‘yancin kai da zaman lafiya. Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya aika wa kasashe mambobin CELAC wasika yana mai kira da su yi tir da abin da ya bayyana a matsayin tsokana da neman tyar da zaune tsaye da Amurka ke yi a yankin Caribbean. Da yake magana kan hare-haren da aka kai kwanan nan kan jiragen ruwa na kamun kifi da kuma tura sojojin Amurka kusa da iyakokin ruwa na Venezuela, Maduro ya bayyana...
    Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta,  yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.” A lokacin ziyararsa a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin Lebanon, Nasser Eddine ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi shahada ya karu daga 23 zuwa 28 a cikin watan da ya gabata, yana mai jaddada cewa waɗannan shahidai suna da iyalai da dangi da ‘yan uwa, kuma dole ne  ƙasa ta tsaya musu. Ya ƙara da cewa: “Dangane da wannan hari na  Isra’ila a kan ƙasarmu, sojojin Lebanon ba...
    Gwamnan yankin Darfur na Sudan, Bahreldin Adam Karamah, ya bayyana cewa shugabannin mayakan RSF sun aikata laifuka a El Fasher, yana mai jaddada cewa “ba za su iya ɓoye su ba.” A cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA), Karamah ya fayyace cewa shawarar da Majalisar Tsaro ta Sudan ta yanke, wacce shugabanninta suka goyi bayanta baki daya, ta tabbatar da cewa “babu wani sulhu da masu kisan gillar al’ummar Sudan.” Ya kara da cewa, “Ba za mu yi sulhu a kan wannan kasa ba, kuma ba za mu bari a sauke tutarta ko a lullube ta a cikin laka tare da ta wulakanta ta ba.” Gwamnan Darfur ya nuna cewa rikicin da ake...
    A yau Lahadi 9 ga wannan wata, an rufe taron koli na Wuzhen na ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya na shekarar 2025 mai taken “kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa mai bude kofa da hadin gwiwa da tsaro don kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo”, inda wakilai fiye da 1600 daga kasashe da yankuna fiye da 130 suka halarci taron da tattauna taswirar kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa.   Babban sakataren taron Ren Xianliang ya yi bayani a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, an zartas da rahoton aiki na taron yanar gizo na duniya na shekarar 2025 a gun taron koli a...
    Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics. Ya ce, gasar wasanni ta kasa ita ce babban bikin wasanni mafi girma a kasar Sin. Kuma yankunan Guangdong, Hong Kong da Macao ne suka hada hannu wajen shirya gasar wasannin ta kasa karo na 15. Ana kyautata zaton cewa, wannan gasar wasannin ta kasa ba wai kawai za ta bayyana sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu a sabon zamani ba ne, har...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji November 9, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba November 9, 2025
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
    ’Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari sansanin Hukumar Kwastam da ke Maje, a Ƙaramar Hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka kashe wani jami’i guda ɗaya. Wani mazaunin yankin ya ce ’yan ta’addan sun zo da yawa, inda suka fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, sannan suka ƙone sansanin jami’an kwastam. Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Ya ce, “Lakurawa sun zo da yawa, suna harbe-harbe ta ko ina. Sun ƙone sansanin kwastam tare da kashe wani jami’i.” Mai magana da yawun hukumar Kwastam a Jihar Kebbi, Muhammad Tajudeen, ya tabbatar da faruwar harin. Ya ce jami’an hukumar suna asibiti suna...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ayyana bude gasar wasanni ta kasa karo na 15 a yau Lahadi. Xi ya halarci bikin bude gasar a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba November 9, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki November 8, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa  November 8, 2025
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu. Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa. Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga “Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi. Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin,...
    Dong ta danganta raguwar farashin na PPI da aka samu a mizanin shekara-shekara bisa karuwar yawan sarrafa kaya a manyan masana’antu, da hanzarta kokarin kafa masana’antu na zamani, da kuma bude hanyoyin sayayyar kayayyaki. A watan Oktoba, ci gaban da aka samu na karuwar hada-hadar kaya da bukatarsu ya haifar da hauhawar farashi a wasu sassa kamar masana’antar hakar kwal da sarrafa shi, kamar yadda Dong ta bayyana, yana mai nuni da cewa su ma sauye-sauyen farashi a kasashen duniya sun shafi farashin wasu kayan masana’antun cikin gida. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki November 8, 2025 Daga Birnin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025 Wasanni Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax November 6, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran ’yan Najeriya da su haɗa kai don kare ƙasar. Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Oyintiloye, ya ce matsalar tsaro ba a zamanin Tinubu ta samo asali ba, kuma a cewarsa matsalar na shafar addinai daban-daban a ƙasar. “Dole ne mu tsaya tare da Shugaba Tinubu. Wannan ba lokacin rabuwar addini ko...
    Daga Usman Mohammed Zaria Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Abba Zari Malamawa a matsayin sabon shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Dutse. A jawabinsa yayin kaddamarwar shugaban kungiyar na jihar, Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci sabon shugaban da ya kasance mai gaskiya da rikon amana wajen hulda da ya’yan kungiyar tare da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki domin cimma nasarar da ake bukata. Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci masu sana’ar dako a karamar hukumar Dutse da su nuna cikakken goyon baya ga sabon shugaban, tare da mutunta ‘yan kasuwa a matsayin su na jigo wajen ciniki da kasuwanci wanda ke bude kofar samu ga ‘yan dako. Ya kuma yi...
    Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, yau Lahadi, inda suka tattauna dangantakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Mista Araghchi ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yanzu tsakanin Afghanistan da Pakistan, yana mai jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tare da taimakon kasashen yankin masu tasiri, don sasanta takaddamar da rage tashin hankali. A watan da ya...
    Ministocin tsaro na kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun yunkuri anniyar kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa, wacce zata tunkari magance barazanar ta’addanci mai nasaba da kungiyoyin JNIM da ISIS a yankin Sahel. Kasashen sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a Niamey karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani da ministocin tsaron kasashen da ke kungiyar kawacen sahel ta (AES). Ministocin tsaro na Mali, Sadio Camara; Burkina Faso, Célestin Simporé; da Nijar, Salifou Mody, sun sanar da shawararsu ta hanzarta aiwatar da aikin rundunar hadin gwiwa ta AES. Shawarwarin da aka amince da su sun tanadi musayar bayanan sirri, da kuma hadin guiwa ta fanin ayyukan soji. Kasashen na fuskantar barazanar kungiyoyin ta’addanci da suka...
    A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa zargin gwamnatin kasar da kauda kai kan kisan da ake wa kiristoci a kasar. Masu zanga-zanga a Kano, dake arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai da barazanar da kuma yin watsi da ikirarin na Trump na “kisan kiyashin Kiristoci.” Masu zanga-zangar sun zargi Washington da amfani da addini domin tsoma baki da a cikin harkokin cikin gidan Najeriya, suna gargadin cewa duk wani matakin soja na Amurka zai keta hurumin Najeriya. A ranar 1 ga Nuwamba, ne Trump ya ce ya umarci Pentagon da ta shirya daukar matakin soji a Najeriya, yana mai ikirarin cewa...
    Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da mummunan ta’addancin da aka aikata kan fararen hula a yankin El-Fasher na Sudan. Ofishin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ya yi gargadin cewa El-Fasher ya zama birnin makoki a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare masu muni, wanda hakan ya haddasa wahalhalu marasa misaltuwa. A cikin wani bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X, Li Fung, Wakiliyar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ta ce: “A cikin kwanaki goma da suka gabata, yankin El-Fasher ya kasance wurin da ake samun karuwar hare-haren ta’addanci. A cewarta, “an kashe daruruwan mutane, ciki har da mata, yara, da wadanda suka...
    A Labanon akalla mutane uku ne suka mutu sannan goma sha daya suka jikkata a hare-haren jiragen sama marasa matuka na Isra’ila a kudancin Lebanon, wanda ya sake nuna yadda Isra’ilar ke keta yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin suka cimma.   A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa na Lebanon (NNA), an kashe ‘yan’uwa biyu lokacin da wani jirgin saman Isra’ila mara matuki ya kai hari kan motarsu kusa da garin Shebaa. Harin ya faru ne a kan wata hanya da ta hada Ain Ata da Shebaa, a kan gangaren yammacin Dutsen Jabal al-Sheikh, wanda ya sa motar ta kama da wuta, kamar yadda NNA ta ruwaito. Wani hari na danban ya afka wa wata mota a Barashit, inda ya...
      Shugaban reshen Akure na NBA, Mr. Friday Umar, wanda ya yi wannan kira, ya lura cewa “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi.   Ya ƙara da gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa shigar da ƙara a inda aka yi laifi don kiyaye mutuncin shari’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Labarai Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9,...
    Daga Usman Mohammed Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta sake jaddada kudirinta na cigaba da horas da matasa maza da mata sana’o’in hannu domin su kasance masu dogaro da kai. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan lokacin bikin yaye matasa 160 da suka sami horo akan sana’o’in dogaro da kai, wanda kungiyar hadin kai ta kafin Hausa ta gudanar. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta bullo da shirye-shirye da nufin mayar da matasan jihar masu dogaro da kawunansu. A don haka, Gwamnan ya godewa Kungiyar bisa bada horan, tare da yin kira ga matasan da suka amfana da shirin su yi amfani da ilmin da suka samu domin zama masu dogaro da kai. A jawabinsa na marhabun...
      Ana sa ran Mataimakin Shugaban Majalisar zai gana da gwamnan Jihar, Dr. Nasir Idris, a safiyar yau Lahadi.   Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomi kan yadda Mataimakin Shugaban Majalisar ya kuɓuta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra November 9, 2025 Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9, 2025
    A wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a nan birnin Tehran an kafe Mutum-mutumin   tarihi na sarkin daular Roma Velarian wanda aka kamo shi a matsayin fursunan yaki a zamanin Daular Sasaniyawa, ya kuma durkusa a gaban sarki Shahpur 1. Kafe Mutum-mutumin  da aka yi, yana a karkashin jaddada matsayar Iran na cewa, al’ummarta ba ta rusunawa a gaban abokan gaba sai dai su rusuna a gabanta. A shekarar miladiyya ta 260 bayan haihuwar Annabi Isa ( a.s) ne aka yi yaki a tsakanin tsohuwar daular farisa ta Sasaniyawa da kuma daukar Roma ta gabasa, a Edessa, wanda ya kare da murkushe sojojin Romawa 70,000 sannan kuma aka kama sarkinsu Velarian aka kawo shi Iran a matsayin furusunan yaki. Har...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su karbi albashi ba, idan su ka yi aiki alhali ayyukan gwamnati suna a rufe. Hukumar filayen jiragen sama ta tarayyar Amurka ce ta sanar da cewa masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama a hasumiyoyin dake cikin filayane jiragen sama 25 sun dakatar da aiki. Daga cikin garuruwan da tsaikon aikin ya shafa da akwai Chicago, Sanfarancisco, New York, New Rock da kuma Atalanta. Tashar...
    Wasu Karin kasashe takwas sun yi kira da a kama Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila  Benjamine Netanyahu saboda laifukan yakin da ya aikata.  Kasashen Turkiya, Norway, Italiya, Canada, Slovenia da Lithuania, sun bayyana cewa a shriye suke su kama fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila. A kasar Turkiya mai shiga da kara na birnin Istanbul ya fitar da sammacin kamo mutane 37 masu hannu a kisan kiyashin Gaza daga cikinsu da akwai Netanyahu, ministansa na yaki, Kats, da babban hafsan hafsoshin sojan ‘yan sahayoniya Iyal Zamir. A ranar 21 ga watan Nuwamba 2024 ne kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kamo Fira minista Netanyahu da tsohon ministansa na yaki Yoav Gallant saboda amfani da yunwa...
    Shirin Majalisar Dinkin Duniya Na Samar Da Abinci ( WFP) ya fitar da gargadi akan cewa, yankin gabashin DRC yana fama da matsananciyar yunwa.  Daraktar cibiyar ta WFP a kasar ta DRC Cynthia Jones ce ta yi wannan gargadin yana mai kara da cewa; Da akwai iyalan da suke tsallaken cin abinci, bayan da su ka sayar da kayan gidansu da kuma dabbobin da su ka mallaka.” Hukumar da yake kula da wadatar abinci ( IPC) ta ce da akwai mutanen da adadinsu ya kai miliyan 25 da suke cikin matakin karshe na yunwa, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3 da suke cikin hatsari. Hukumar ta MDD ta kuma ce, a halin yanzu mutane suna ta mutuwa saboda babu...
    Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi. Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo. ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar. Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya...
    Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka.   Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9, 2025 Labarai Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza November 8, 2025
    Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi. Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445. George Moghalu na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401. Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban...
    Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana. Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu. Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma  zai share fagen...
    ‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata. Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi na kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam da dama sun yi ikirarin cewa, jami’an tsaro sun kashe mutane sama da 1,000 yayin da suke tarwatsa zanga-zangar, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su a matsayin marasa tushe, amma kuma gwamnatin ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba. ‘Yan sanda sun sanya Gologowa da wasu mutane tara a cikin jerin...
    Hare-haren daukan fansa da Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar janyo hasarar dala miliyan 200 Harin da aka kai wa matatun mai na Haifa na ɗaya daga cikin ayyukan da Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya ga harin da Isra’ila ta kai a lokacin yaƙin kwanaki 12. Shirin “Lambar” a cikin ɓangarensa na “Sa ido”, ya magance wannan aikin. Waɗannan matatun mai suna daga cikin muhimman wurare na dabaru a Isra’ila, waɗanda ke cikin ɗaya daga cikin muhimman tashoshin jiragen ruwa kuma suna aiki a matsayin babbar cibiyar jiragen ruwa da ke jigilar mai zuwa ƙasar. A cewar ƙididdiga da ƙayyadaddun fasaha, matatun mai na Haifa suna da ƙarfin samar da tan miliyan 9.8 a...
    Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne  har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya ga Fadar White House ba ce, har ma ga dimokuradiyyar Amurka. CNN ta ambato Biden yana cewa: A lokacin wani taron Jam’iyyar Democrat a Nebraska a yammacin Juma’a a Omaha: “Biden na cewa, ya san Trump zai kawo wani abin kunya a kasar, amma bai sani ba shin dole ne ya amince cewa akwai wani abin kunya da ya riga ya faru.” Biden yana magana...
    Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka zayyana sun haɗa cewa, ya danganta halittar Annabi SAW da ƙasƙantun halittu (‘Ya’yan Tumkiya, da Karya, da Ƙwarƙwata), sannan kuma ya taɓa alfarmar iyayen Annabi SAW wanda a cewarsu, hakan bai dace ba a alfarmarsa fiyayyen halitta.   Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba tare da ɓata lokaci ba, ta miƙa koken ga Majalisar Shura ta jihar domin fayyace gaskiyar lamari.   Majalisar Shura, ta bakin Sakatarenta, Shehu Wada Sagagi, a wani taron manema labarai da ta gudanar, ta tabbatar da cewa, za ta gudanar da cikakken bincike akan zargin da aka yi wa Malamin (Abubakar Triumph). Sannan kuma, za ta gayyaci masu ƙorafe-ƙorafe da kuma Malamin domin sauraron bayanansu....
    Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin ƙasar nan. Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma ‘yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta. Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace. Haka kuma,...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun  tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar a ranar Asabar, Abdelatty ya yi nazari kan ci gaba da kokarin da Masar ke yi na karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa. Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya zuwa mataki na biyu na shirin tsagaita wuta, wanda zai  magance matsalolin siyasa da ayyukan  jin kai domin samun...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa  November 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025
    Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya taɓa zargin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ƙirƙiro Boko Haram. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanata Sheriff ya bayyana labarin a matsayin ƙarya mara tushe. Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Ya ce bai taɓa yin wata hira ko yi wa wani bayani da ya shafi Shettima game da kafa Boko Haram ba. “Wannan labari ƙarya ne gaba ɗaya, kuma an shirya shi ne domin rikita jama’a da kawo rabuwar kai,” in ji sanarwar. Sheriff, wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya ce waɗanda...
    Fidan ya ci gaba da cewa akwai bukatar fara aiwatar da kudirin da aka cimma yayin taron kasashen Musulmi na OIC da kuma Arab League dangane sake gina Gaza don karfafa da kuma tallafar rayuwar dimbin Falasdinawan da Isra’ila ta tagayyara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga November 8, 2025 Manyan Labarai Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya November 8, 2025 Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025
      Kazalika, duk dai a jiya Jumma’ar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da taron, Chen Binhua, mai magana da yawun Ofishin Harkokin Taiwan na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ya ce taron wanda ya gudana shekaru goma da suka gabata ya karfafa muhimmiyar rawar da Yarjejeniyar 1992 ta taka a matsayin ginshikin siyasa ta bunkasa zaman lumana a dangantakar bangarori biyu na mashigin tekun, kana matukar an ci gaba da amincewa da Yarjejeniyar 1992 kuma aka nuna adawa da batun “‘yancin kai na Taiwan”, to dangantakar bangarorin biyu za ta iya bunkasa cikin lumana kuma za a iya kara inganta muradun ‘yan kasa da ke bangarorin biyu na mashigin tekun. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga...
    Wasu ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta sun kai hari ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato da safiyar ranar Asabar. Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mutum biyar, tare da jikkata wani ɗan sa-kai, sannan suka sace wasu mutum tara waɗanda mafi yawansu mata ne. Ban ɓata zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Kafin faruwar harin, wani mai ɗan gwagwarmaya a yankin mai suna Basharu Altine Guyawa, ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ya yi gargaɗin cewa Bello Turji da tawagarsa suna shawagi a yankin Fadanar Tursa da Dorawar Madugu zuwa Dan Huntuwa ta gadar...
    BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”.   Somalia (1992–1994) Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s. A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya. Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida. Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025
    Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi  ya zo na daya a duniya  da maki 170.80  kuma yana mataki na 4  a bangaren Olympic, A gefe...
    Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya taɓa zargin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da ƙirƙiro Boko Haram. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanata Sheriff ya bayyana labarin a matsayin ƙarya mara tushe. Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Ya ce bai taɓa yin wata hira ko yi wa wani bayani da ya shafi Shettima game da kafa Boko Haram ba. “Wannan labari ƙarya ne gaba ɗaya, kuma an shirya shi ne domin rikita jama’a da kawo rabuwar kai,” in ji sanarwar. Sheriff, wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya ce waɗanda...
    Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa. Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025
    Prime ministan kasar Iraki shiya Al-sudani ya sanar a birnin bagadaza cewa sun fara shirin kula wata yarjejeniya a hukumace da kasar Amurka, da zai kai ga ficewar sojojin kasashen waje daka kasar, daga nan zuwa wata satumbar shekara ta 2026, wanda wannan wata ishara ce ta bude wani sabon shafi a kasar na zaman tabbaci da tsaro mai dorewa. Kasar iraki na kokari wajen ganin an kawo karshen zaman sojojin mamayar Amurka dake kasar fiye da shekaru 20 da kuma tsoma bakin kasashen wajen, da ya fara daga lokacin da Washington ta shiga kasar a shekara ta 2003 domin kaddamar da hare-hare da dukkan duniya ta yi tir da shi da kuma bayyana shi a matsayin wanda ya sabama...
    Rahotanni sun bayyana cewa a kasar Turkiya an fitar da hukumci kama prime ministan Isra’ila banjamin Natanyaho da wasu jami’an Isra’ila guda 37 da laifin keta hakkin bil adama da kuma yin kisan kare dangi kan alummar Gaza a lokacin yaki, Wannan yana nuna irin mataki mai tsauri na doka da aka dauka kan jami’an Isra’ila a baya bayan nan, kan laifuka yaki da suka tafka kan bil adam a yakin Gaza, da kuma karfafa kasashen duniya daukar matakin da ya dace kan zargin da ake mata na kai hare-haren kan fararen hula. Sabanin tsakanin Ankara da tel aviv ya kara tsananta ne tun bayan da ta fara kai hare-haren kan fararen hula a yankin gaza a shekara ta 2023...