Shima da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan harkokin mata, yara da nakasassu na jihar Kano, wanda daraktan gudanarwa, Alhaji Mohammed Sambo Iliyasu ya wakilta, ya jaddada goyon bayan jihar kan ci gaban harkokin inganta zamantakewa da walwalar al’umma.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.

Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya Ta Cimma Sabon Tsarin Hadin Gwiwa Kan Sha’anin Tsaro da Amurka

Daga Bello Wakili

Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawa da tawagarta ta yi da jami’an Amurka ta kara karfafa huldar tsaro tsakanin kasashen biyu tare da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa domin kara kare ‘yan Najeriya.

Tawagar, karkashin jagorancin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ta  gana da manyan jami’an Majalisar Dokokin Amurka, Ofishin Bangaren Addini na Fadar White House, Ma’aikatar Harkokin Waje, Majalisar Tsaro ta Kasa da Ma’aikatar Yaki a birnin Washington DC

A yayin tattaunawar, tawagar ta musanta zargin kisan kare dangi a Najeriya, tana mai jaddada cewa hare-haren da ake samu na shafar al’umma ne daga bangarori daban-daban na kabilu da addinai. Ta ce irin wannan kuskuren fassarar halin da ake ciki na haifar da rarrabuwar kai da kuma karkatar da gaskiyar abin da ke faruwa.

Bayan ganawar, Gwamnatin Amurka ta tabbatar da kudirinta na karfafa huldar tsaro da Najeriya ta hanyar inganta musayar bayanan sirri, hanzarta aiwatar da bukatun kayan aikin tsaro, tare da yiwuwar bayar da karin kayan tsaro na musamman idan sun samu, domin tallafa wa yakin da ake yi da ‘yan ta’adda da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.

Amurka ta kuma nuna shirinta na bada tallafin jin kai ga al’ummomin da rikici ya shafa a yankin Arewa ta tsakiya, da kuma taimakawa wajen karfafa tsarin ankararwa da wuri, tare da daukar mataki cikin gaggawa.

Kasashen biyu sun amince da fara aiki kai tsaye da wata yarjejeniyar hadin gwiwa da kafa Kwamitin Aiki na Hada-hadar Tsaro domin tabbatar da tsari guda wajen aiwatar da abin da aka cimma.

A nata bangaren, Najeriya ta sake nanata kudirinta na inganta tsarin kare fararen hula a fadin kasar.

Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawar ta bayar da dama wajen gyara kuskuren fahimta game da halin da ake ciki, ta karfafa amincewar juna, tare da inganta dabarun hadin gwiwa domin kare al’ummomi masu rauni musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.

Mambobin tawagar sun hada da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi; Shugaban Hafsoshin Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Daraktan Leken Asiri na Soji, Laftanar Janar Emmanuel Parker Undiandeye; Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun; Daraktan Harkokin Ketare a Ofishin mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro NSA, Ambasada Ibrahim Babani; da Mai Baiwa NSA Shawara ta Musamman, Ms. Idayat Hassan.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi saboda matsalar tsaro
  • Najeriya Ta Cimma Sabon Tsarin Hadin Gwiwa Kan Sha’anin Tsaro da Amurka
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kwara Ta Sanar da Wa’adin Biyan Kudin Aikin Hajjin 2026
  • Matsalar tsaro: Gwamnatin Yobe ta rufe duk makarantun sakandaren kwana
  • An rufe duk makarantu a Jihar Bauchi na saboda matsalar tsaro
  • Najeriya: Kungiyar Yan Ta’adda Ta ISWAP Ta Sace Yan Mata 13 A Jihar Borno
  • Gwamnatin Kebbi Ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantu a Jihar
  • Antonio Guterres Ya Kira Yi Kungiyar G 20 Da Su Warware Matsalar Rashin Adalci A Harkokin Kasuwanci
  • Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya