Babban daraktan hukumar IAEA, Rafael Grossi, zai ziyarci Iran cikin makwanni masu zuwa
Published: 2nd, April 2025 GMT
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin.
Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT).
Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai.
Da yake amsa tambaya daga wakilin TASS, Grossi ya tabbatar da cewa ana tattaunawa don tsara ziyararsa a makonni masu zuwa.
Wannan bai ta ce ziyarar Rafael Grossi, t afarko a Iran ba, don kuwa ko a kasrhen watan Nuwamban bara ya gana da shugaban Iran Masoud Pezeshkian da ziyarce-ziyarcen cibiyoyin nukiliya na Fordow da Natanz.
Ziyarar Grossi ta zo ne a daidai lokacin da Iran ke ci gaba da tabbatar da hakkinta na samar da makamashin nukiliya cikin lumana karkashin dokokin kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 2, 2025
Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025
Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025