Aminiya:
2025-07-31@17:28:00 GMT

Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas

Published: 24th, March 2025 GMT

Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun maka Shugaba Bola Tinubu a Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas, Similanayi Fubara.

Gwamnonin sun garzaya kotun ne domin neman fatawa game da abin da sashe na 305 na kundin mulkin ƙasar ke nufi.

Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha Juventus za ta sallami kocinta Thiago Motta

Gwamnonin da ke kan gaba a shigar da ƙarar sun haɗa da na jihohin Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato, Zamfara.

Daga cikin abubuwan da suke nema akwai neman kotun ta ɗauki matsaya kan ko sashen na 305 na kudin mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa shugaban ƙasa dama ya dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da mataimakiyarsa da majalisar dokoki ta jiha, kuma ya naɗa wani gwamnan riƙo a ƙarƙashin dokar ta-ɓaci.

A ƙunshin takardun da suka gabatar wa kotun, gwamnonin sun ce dakatar da zaɓaɓɓun shugabanni da Shugaba Tinubu ya yi na cin karo da sassa na 1(2) da na 5(2) da kuma na 305 da ke ƙunshe a Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Matakin na zuwa bayan huɗu cikin shida na gwamnonin yankin kudu maso kudu sun yi tir da dokar da Tinubu ya ayyana a Ribas.

Gwamnan Bayelsa Duoye Diri, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin, ya ce, “rikicin siyasar na Ribas bai kai abin da za a ayyana dokar ta-ɓaci a kai ba kamar yadda sashe na 305(3) ya tanada.”

Sai dai kuma, gwamnonin Edo da na Kuros Riba sun goyi bayan matakin na Shugaba Tinubu.

A gefe guda kuma, ƙungiyar neman shugabanci na gari ta Socio-Economic Rights and Accountability Project (Serap) ta ce ta shigar da Tinubu ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja game da dakatar da gwamnan Ribas da mataimakiyarsa da majalisar dokoki “wanda ya saɓa wa doka”.

Ana iya tuna cewa, a ranar 18 ga wannan wata na Maris ne Tinubu ya dakatar da Gwamna Similanayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu da duk ’yan majalisar dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida tare da ɗora tsohon Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas a matsayin kamtoman jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnoni Siminalayi Fubara

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.

A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki.

Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin Hamas sun fahimci bukatar neman cimma muradun al’ummar Gaza da ake zalunta ta hanyar da ta dace, kuma ba sa bukatar shiga tsakani na bangarori na uku dangane da hakan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya yi la’akari da katsalandan din Iran a cikin shawarwarin da suka dace da cewa ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa irin wadannan zarge-zarge wani nau’i ne na neman tauyaye hakki da gujewa hakkin da ya rataya a wuyar mutum da kokarin Amurka na gujewa duk wani mugun aiki da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aikita kan al’ummar Falasdinu, da suka hada da kisan fararen hula 60,000 da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara da kuma killace Zirin Gaza tsawon watanni. Da hana shigar agajin jin kai da kuma kashe fararen hula da ke fama da yunwa da kishirwa a tarkon kisa a wuraren da ake kira cibiyoyin rarraba kayan agaji da wata cibiyar Amurka ta kafa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
  • Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC
  • Gwamnan Kaduna Ya Sauke Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ya Maye Gurbinsa Da Maiyaki
  • EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza
  • Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
  • Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
  • Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci
  • Kungiyar Gwamnonin Jihohi Ta Jajintawa Jihar Adamawa Bisa Ambaliyar Ruwa A Yola