Arakci: Babu Wanda Zai Yi Tunanin Kawo Wa Iran Hari
Published: 24th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana cikin shirin ko-ta-kwana akan duk wani abu da zai iya bijirowa, kuma a halin yanzu ba batun yaki ake yi ba.
A wata ganawa da ministan harkokin wajen na Iran ya yi da tawagar kungiyar agaji ta “Red Cross” a karkashin jagorancin shugabanta Koliband, ministan harkokin wajen na Iran ya yabawa aikin nasu, tare da cewa; Duk da cewa ana cikin lokacin hutu, amma su a kodayaushe suna cikin shirin ko-ta-kwana domin gabatar da ayyukan agaji da hakan yake nuni da yi wa al’umma hidima ta koli.
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kuma ce: Su ma sojoji da jami’an tsaro kamar ku suke aiki, ba su da lokacin hutu,kodayaushe suna cikin shirin ko-ta-kwana.
Haka nan kuma ya kara da cewa; Kowane bangare na gwamnati yana cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar kowane irin yanayi.
Har ila yau, babban jami’in diflomasiyyar ta Iran ya ce; Ina da tabbacin cewa babu wani mahaluki da yake tunanin kawo wa Iran hari, domin suna sane da sakamakon da take tattare da yin hakan, sun kuma san cewa kowane bangare na gwamnati yana cikin shiri.
Abbas Arakci ya kuma bayyana cewa baya ga ayyukan agaji da kungiyar take yi a cikin gida, tana kuma gabatar da wasu ayyukan na taimako a kasashen waje. Ya kuma yi ishara da lokacin girgizar kasar Japan, da hukumar agaji ta Iran ta kai dauki, wanda ya taka rawa wajen kara bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Tattaunawar Nukiliya Wani Zabi Ne Mai Muhaimmanci Wanda Ya Karfafa Matsayin Iran A Duniya
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan.
Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar Iran da ma matakan da aka dauka na yin shawarwari da kasashen yammacin duniya. Ya yi bayanin cewa, manufar yarjejeniyar makamashin nukiliyar ta ginu ce bisa ka’ida mai ma’ana, ta yadda Iran za ta dauki matakai na karfafa kwarin gwiwa domin dage takunkumin kanta.
Jami’in na Iran ya yi nuni da cewa, a lokacin da gwamnatin Trump ta Amurka ta bayyana burinta na yin shawarwari kan batun makamashin nukiliyar, Iran ta bayyana shirinta na shiga tattaunawa bisa wannan manufa, tare da jaddada cewa, ba za ta amince da duk wani sharadi da zai kawo cikas ga shirinta na nukiliya ko kuma dakatar da ayyukan inganta sinadarin Uranium ba.