Neman “’Yancin Kan Taiwan” Da Jam’iyyar DPP Ke Yi Zai Ci Tura
Published: 2nd, April 2025 GMT
Tun daga ranar 1 ga watan Afrilu, dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar ta kaddamar da atisayen hadin gwiwar rukunoni masu kunshe da sojojin kasa, da na ruwa, da na sama da dai sauransu a kewayen tsibirin Taiwan. Atisayen da ya kasance wani salo na jan kunne mai karfi ga mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te dake rajin “’yancin kan Taiwan”, kana mataki mai karfi da ya wajaba na kare ikon mulkin kai da cikakkun yankunan kasar Sin.
Kamar yadda aka sani, Taiwan wani sashe ne na kasar Sin, wanda ba ta taba zama kasa ba, kuma ba zai taba zama ba a nan gaba. Sunan yankin Taiwa a MDD shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Duk yunkurin Lai Ching-te ba zai iya canza gaskiyar ba.
A daya hannun, matakin da babban yankin kasar Sin ya dauka ya nunawa kasashen duniya tsayayyiyar niyyar kasar ta tabbatar da nasarar warware batun Taiwan, da cimma manufar dinke dukkanin sassan kasar yadda ya kamata, kana ba za ta taba amincewa da duk wasu rukunoni ko mutanen dake neman balle Taiwan daga kasar Sin ba. Kowane karin girman kai da mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te dake rajin “’yancin kan Taiwan” suka yi, za a bi shi da hukunci mai karfi daga babban yankin kasar Sin, kuma karshensu zai zo da wuri. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp