Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Published: 2nd, April 2025 GMT
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya.
Jaridar Tehran time ta nakalto Dr Larijani ya kara da cewa idan Amurka ko HKI ko duka biyu suka kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar, to kuwa zata kera makaman nukliya.
A ranar Lahadin da ta gabata ce, Dr Larijani ya bayyana haka. Sai dai a daren Litinin ne Dr Larijani ta kara jaddada wannan matakin.
Sai dai kafin haka shugaban ma’aikatar leken asiri na Amurka ta tabbatarwa tashar talabijin ta NBC kan cewa Iran bata da shirin samar da makaman Nukliya.
Amma Trump ya sha nanatawa cewa iran Iran bata zo suka tattauna batun shirinta na makamashin nukliya ba sai ya kai hare-hare kan ciboyoyin makamashin nukliya na kasar Iran.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makaman nukliya
এছাড়াও পড়ুন:
Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin isra’ila na fuskantar suka game da matakin da ta dauka na kai hari kan kungiyar unicef ta majalisar dinkin duniya a gaza, matakin da falasdinawa da masu sa ido ke gani a matsayin wata dabara ta murukushe kungiyoyin agaji da kuma fitar da kungiyoyin majalisar dinkin duniya daga yankin gaza
Rahoton da wani jami’in majalisar dinkin duniya ya fitar a jiya jumaa ya nuna cewa sojojin isra’ila sun kama wani ma’aikacin UNICEF mai suna Raed Afif mai shekaru 45 da haihuwa a kerem shalom alokacin da yake gudanar da ayyukansa.
Yazu wa yanzu isra’ila bata bayyana dalilan da suka sanya ta kama shi ba kuma take ci gaba da tsare shi.
Kwana daya kafin tayi kamun isra’ila ta bukaci kungiyar ta Unicef da ta kwashe dukkan kayayyakin agajinta daga yankin , kawai sai ta rufe dukkan kofofin shiga da magunguna zuwa asibitocin dake arewacin yankin Gaza. Kungiyoyin bada agaji na duniya sun yi gargadin cewa wannan matakin an dauke shi ne domin yanke duk wasu ayyukan jinkai da ake yi da kuma korar dukkan kungiyoyin agaji da hakan zai kara sanyawa yanayi ya kara tazzar a yankin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci Daga Yanzu November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci