Araghchi : Iran a shirye take don tattaunawa amma barazanar soji daga Amurka na dagula yanayin’
Published: 2nd, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu.
“Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba.
Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.”
Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD da dokokin kasa da kasa, hasali ma suna “rikitar” halin da ake ciki.
Araghchi ya yi gargadin cewa Iran za ta mayar da martani “cikin gaggwa” ga duk wani cin zarafi a kan iyakokinta, huruminta, da kuma muradun kasarta.
A halin da ake ciki kuma, ya soki kungiyar Tarayyar Turai kan gazawarta na daukar matsaya kan kalaman na jami’an Amurka, wadanda ya ce suna barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
A nasa bangaren, Veldkamp ya bayyana damuwarsa game da karuwar tashe-tashen hankula a yankin, yana mai jaddada bukatar hanyoyin diflomasiyya wajen warware takaddamar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar a karshen mako cewa zai iya ba da umarnin kai hare-haren soji kan Iran idan Tehran ta ki shiga tattaunawa don “saka sabuwar yarjejeniya” kan shirinta na nukiliya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD: Adadin ‘Yan Gudun Hijira A Duniya Ya Kai Miliyan 122
Hukumar dake kula da ‘yan hijira dake karkashin MDD ta sanar da cewa, mutanen yake-yake da rikice-su ka tilastawa yin hijira a duniya ya kai miliyan 122.
A yau Alhamis ne dai hukumar dake kula da ‘yan hijirar ta bayyana haka, tana kai kara da cewa; gajiyawar da aka yi na warware fadace-fadace da rikicen da suke faruwa a duniya ne su ka kara yawan ‘yan hijirar, daga ciki har da kasashen Sudan da kuma Ukiraniya.
Haka nan kuma ta ce; Tun daga 2015 ne ake samun koma baya na kudaden da ya kamata a rika bayarwa domin taimakawa ‘yan hijira.
Shugaban hukumar ‘yan hijirar ta MDD Filippo Grandi wanda ya gabatar da rahoto akan halin da ake ciki, ya yi ishara da cewa, tun daga watan Aprilu na wannan shekara ta 2025 da ake ciki an sami karuwar mutane miliyan biyu da su ka zama ‘yan hijira, duk da cewa wani adadin da ya kai mutane miliyan biyu ‘yan kasar Syria sun koma kasarsu bayan faduwar gwamnatin Basshar Asad.
Filippo Grandi ya ce rikice-rikicen kasar Myanmar, da yakin Ukiraniya da Sudan su ne ummul-haba’isin karuwar ‘yan hijirar da kuma gajiyawa wajen kawo karshen hakan.
Kasar Amurka tana cikin wadanda su ka rage yawan taimakon kudaden da suke bayarwa a harkar agaji, yayin da kasashe kamar Birtaniya da wasu kasashen turai suke bayar da kadan.