Gidauniyar Bafarawa Ta Rabawa Kananan ‘Yan Kasuwa Naira Milliyan 13 a Sokoto
Published: 13th, March 2025 GMT
Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu.
Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar.
Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai karbi naira dubu hamsin tare da tallafin sufurin daga naira 3,000 zuwa naira 5,000, ya danganta da nisan su da wuraren rabon kayayyakin.
Maidoki ya jaddada cewa shirin na da nufin wadata wadanda suka samu tallafin jarin da ake bukata domin biyan bukatunsu na yau da kullum da kuma samar da kudaden shiga, da karfafa tattalin arzikin kasa.
Da yake jawabi a wajen taron, Sarkin Malaman Sokoto, Malam Yahaya Boyi, ya yabawa tsohon Gwamna, Alhaji Attahiru Bafarawa bisa wannan karamci da ya nuna.
Ya mika godiyar wadanda suka amfana, sannan ya bukace su da su yi addu’a ga masu hannu da shuni, Jihar Sakkwato, da Nijeriya, musamman a wannan wata na Ramadan mai albarka.
Boyi ya kuma ja hankalin wadanda suka karba da su yi amfani da kudaden da suka dace ta hanyar yin sana’o’i masu inganci maimakon yin bara.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, Shehu Gwiwa, ya bayyana godiya a madadin sauran jama’a, inda ya gode wa wannan gidauniya bisa tallafin da ta bayar, ya kuma yi addu’ar Allah ya sakawa duk masu hannu a wannan shirin.
Nasir Malali
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Bafarawa Rabo Sakkwato wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.
Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi.
Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba.
Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati?
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan