An Bada Umarnin Sake Tsugunar Da Wadanda Harin ‘Yan Bindiga Ya Rutsa Da Su A Kebbi
Published: 13th, March 2025 GMT
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa.
Gwamnan, ya ba da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kangiwa da Lakurawa suka kai musu hari tare da raba su da muhallansu a kauyukan Birnin Debe, Dan Marke da Tambo.
Gwamnan ya ce, ya kai ziyarar ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da ba shi damar samun rahoton halin da ake ciki a kan wannan mummunan lamari don jagorantar gwamnatin jihar ta dauki matakin da ake bukata tare da tantance halin da ake ciki da kuma tabbatar da matakan da suka dace da za a dauka cikin gaggawa domin kai daukin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.
A yayin da yake koka da cewa, ana kai hare-haren ne daga jihar Sokoto da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi, ya kuma yaba wa jami’an tsaro da suka yi iya kokarinsu wajen ganin an shawo kan lamarin, ya kuma bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi da suka samu ga hukuma domin daukar matakin da ya dace.
Tun da farko Shugaban Karamar Hukumar Arewa Alhaji Sani Aliyu ya godewa Gwamnan bisa daukar matakin gaggawa don ganin an shawo kan wannan mummunan lamari.
Shugaban ya kuma bayyana cewa an bayar da agajin ga wadanda abin ya shafa, inda ya ce iyalan kowannen wadanda suka rasa rayukansu sun samu Naira 500,000 yayin da kowanne daga cikin wadanda suka jikkata kuma ya samu N500,000.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan bindigar Lakurawa suka kai hari kauyuka 7 a karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi inda suka kashe sama da mutane 10 tare da kona gidaje da dama wanda hakan ya kasance harin ramuwar gayya biyo bayan kashe wani shugabansu mai suna Maigemu da jami’an tsaro suka yi.
Abdullahi Tukur
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Bai Taɓa Ba Ni Umarnin Yin Ƙarya Ko Cin Zarafin ’Yan Jarida Ba – Minista
Ya ƙara da cewa, Tinubu na mutunta dimokuraɗiyya da doka.
Haka kuma, gwamnati ta san cewa ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.
Idris ya ce a baya, wasu jami’an gwamnati suna sukar gwamnati, amma shi kullum yana tattaunawa da ƙungiyar ’yan jarida da masu wallafa jaridu domin warware matsaloli cikin lumana.
“Idan muna yin daidai, ku yabe mu,” in ji shi.
“Idan kuma muna kuskure, ku faɗa mana cikin lumana domin mu inganta ayyukanmu.”
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar mu’amala da kafafen labarai kuma hakan zai ci gaba.
Ya roƙi ’yan jarida ka da su ɗauki wasu ƙananan matsaloli su yi wa gwamnati hukunci a kai gaba ɗaya.
Ya kuma bayyana wani babban ci gaba da aka samu a Nijeriya na dab da samuwa domin za a karɓi baƙuncin Cibiyar Wayar da Kan Jama’a kan Hanyoyin Yaɗa Labarai (MIL) a Jami’ar Open University da haɗin gwiwar UNESCO.
Wannan cibiyar za ta taimaka wajen ilimantar da mutane kan labaran ƙarya da yaɗa jita-jita.
“Da zarar an amince, mutane daga sassa daban-daban na duniya za su riƙa zuwa Nijeriya domin koyon dabarun kafafen yaɗa labarai,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp