Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno
Published: 24th, July 2025 GMT
Dakarun Sojin Operation Hadin Kai, sun daƙile hare-haren Boko Haram a garuruwan Monguno da Bitta da ke Jihar Borno, tare da wani kashe babban Kwamandan Boko Haram mai suna Ibn Khalid.
Sun kuma kashe ’yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan ƙungiyar.
NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum Tinubu ya sake miƙa buƙatar karɓo bashin Dala miliyan 347 daga ƙetareMataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Kapten Reuben Kovangiya, ya ce sojojin sun yi jarumta wajen hana ’yan ta’addan shiga Monguno.
Ya ce sojojin sun yi amfani da manyan makamai wajen mayar da martani, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Ibn Khalid.
Yayin da sojojin ke bin sahun ’yan ta’addan da suka tsere, sun ga jini a hanya, alamar cewa wasu daga cikinsu sun jikkata.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama daga hannun ’yan ta’addan, ciki har da harsasai, PKT, ma’ajin bindiga AK-47, bam ɗin roka (RPG) da wasu kayayyaki.
Haka kuma, sun samu na’urar ɗaukar bidiyo da ’yan ta’addan ke amfani da ita.
A wasu hare-haren daban da suka gudana a wannan lokaci, sojojin sun kashe ƙarin mayaƙan Boko Haram 17 a dazukan Sambisa, Madagali da Kaga.
Haka kuma sun ƙwato babura da wasu kayan amfani daga hannunsu.
Shugabannin dakarun sun yaba da jarumtar sojojin, kuma sun buƙace su da su ci gaba da yaƙar ’yan ta’addan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Boko Haram kwamanda yan ta addan
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Tawayen Sudan Ta Kungiyar Rapid Support Forces Sun Kashe Mutane 27 A Yammacin Jihar Kordofan Ta Kasar Sudan
Mutane akalla 27 ne aka kashe a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai a yammacin Kordofan na kasar Sudan
Kafofin yada labaran kasar Sudan sun rawaito cewa: Mutane 27 ne suka mutu kana wasu 43 suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan wasu kauyukan arewacin garin Nahud na jihar Kordofan ta yamma.
Kungiyar likitocin Sudan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jaridar Sudan Tribune ta buga, inda ta bukaci daukar matakin kasa da kasa na dakatar da abin da ta bayyana a matsayin “cin zarafin fararen hula da bude hanyoyin jin kai don ceto wadanda aka tilastawa gudun hijira daga yankunansu.”
A cewar jaridar, dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces ne ke rike da mafi yawan yammacin Kordofan, ciki har da babban birnin jihar, Al-Fula, yayin da sojoji ke iko da Babanusa da wasu gidajen mai a Heglig.