Aminiya:
2025-04-30@19:16:41 GMT

Rikici ya ɓarke bayan wata mata ta mari ɗan sanda a Saudiyya

Published: 29th, March 2025 GMT

Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.

Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo

Bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Juma’a, ya nuna matar tare da wata ƙawarta suna tunkarar wajen da aka kange, inda jami’an tsaro suka hana su wucewa.

Sai dai matar ta fusata, tare da marin ɗan sandan, shi ma daga bisani ya rama kafin wasu su shiga tsakani.

Lamarin ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke ganin matar ta ci zarafin jami’in tsaron yayin da yake bakin aikinsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: askar Ɗan Sanda mari Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴansanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A Jigawa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Da Alamu Amurka Ta Fara Dandana Kudarta
  • Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47
  • Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
  • Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka Game Da Batun Haraji
  • Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
  • Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku
  • Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
  • Ƴansanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A Jigawa
  • Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare