HausaTv:
2025-07-25@21:32:41 GMT

Majalisar Dokokin Isra’ila Ta Kada Kuri’ar Sake Mamaye Yankunan Flasdinawa

Published: 24th, July 2025 GMT

Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da karya dokokin kasa da kasa, inda ta fara mamaye yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kwarin Jordan!

Majalisar Dokokin yahudawan sahayoniyya ta Knesset ta kada kuri’a kan wani kudirin doka da ba shi da tushe don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila cikakken ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan.

Kuri’ar dai ta samu amincewar ‘yan majalisu 71, yayin da 13 suka nuna adawa da shi. Kungiyar Hamas ta dauki matakin a matsayin maras halacci a doka.

A wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida da na waje, Majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da wani kudirin doka da bai taka kara ya karya ba na tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan, matakin da ya bullo da wani fanni na shari’a da siyasa da ba a taba gani ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Da Karamar Hukumar Dutse Za Su Shirya Taron Bita Ga Kansiloli

Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana cewa gudanar da ayyukan raya kasa sosai a yankunan karkara zai kara daga martabar jihar a idon sauran jihohin kasar nan.

Ya yi wannan tsokaci ne yayin ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Dutse, inda ya ja hankalin shugaban karamar hukumar game da bukatar bada fifiko ga bangaren ayyukan raya kasa fiye da harkokin yau da kullum domin karfafa matakin cigaban karamar hukumar.

A cewar sa, kwamatin na rangadin kananan hukumomin jihar 27 ne domin bibiyar yadda ake aiwatar da tanade tanaden kasafin kudi domin tabbatar da kashe kudaden gwamnati ta hanyar da ta dace, Inda Kwamatin ke duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin Kudi da nufin cusa dabi’ar aiki da tanade tanaden aikin gwamnatin da ka’idojin kashe kudade.

Kazalika, Alhaji Aminu Zakari yace an kafa kananan kwamitoci guda 2 domin ziyarar gani da ido kan ayyukan raya kasa da karamar hukumar Dutse ta gudanar ga jama’ar yankin.

Karamin Kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar
Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashim Kanya, ya duba aikin ginin Masallacin khamsissalawati na garin Barangu da rumfunan kasuwa a garin ‘Yar Gaba da Masallacin khamsissalawati na Gidan Gawo da aikin ginin karamin asibitin garin Charka da aikin karamin asibitin Zangon Buji, da aikin gyaran Masallacin Juma’a na garuruwan Kacha da Barandau.

Shi kuwa karamin kwamati na 2 bisa jagorancin wakilin mazabar Buji, Alhaji Sale Baba Buji ya duba aikin hanyar Burji daga Bolari ta wuce Bakin Jeji zuwa Katangar lafiya, akan naira milyan 129 wadda wani kamfani ya yi, sai kuma rumfar kasuwa a garin Hammayayi da sanya fitilu masu amfani da hasken rana makaranta sikandire ta garin Madobi da Masallacin Juma’a na garin Baranda.

A jawabin sa na maraba, shugaban karamar hukumar Dutse Malam Sibu Abdullahi, ya bayyana ayyukan Kwamatin a matsayin ginshikin samun nasarar gudanar da mulkin kananan hukumomi.

Ya bayyana kudurin sa na karbar gyare-gyare da shawarwarin Kwamatin domin cigaban karamar hukumar sa.

Malam Sibu Abdullahi ya bayyana kudurinsa na hada Kai da majalisar Dokokin jihar Jigawa domin shiryawa kansiloli da Akawun majalisar kamsilolin bita game da tsare tsaren zaman majalisa kamar yadda mataimakin sakataren Kwamatin Malam Sadiq Muhammad ya kawo shawara.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wasu Mahara Sun Sake Kashe Mutum 14 A Wani Kauyen Jihar Filato
  • Amurka: An gabatar da daftarin kudirin sake duba alaka da Afirka ta kudu
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Da Karamar Hukumar Dutse Za Su Shirya Taron Bita Ga Kansiloli
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Tattaunawa kan Masifar Zirin Gaza Na Falasdinu
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
  • Yahudawan Sahayoniyya Sun Bullo Da Dabarar Kisa Kan Falasdinawa Musamman ‘Yan Gudun Hijira
  • Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa