Iran Ta Zargi Amurka Da HKI Da Wargaza Dokokin Kasa Da Kasa Da Kuma Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa
Published: 24th, July 2025 GMT
Wani babban Jami’in diblomasiyyar kasar Iran ya zargi Amurka da kuam HKI da laifin Zagon kasa ga dokokin kasa da kasa da kuma sabawa yarjeniyoyi da dokokin MDD.
Kazen Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran sharia na kasa da kasa yana fadar haka a jiya Laraba a majalisar dinkin duniya a birnin NewYork na kasar Amurka, a lokacinda yake jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD dangane da kasar Falasdinu.
Gharibabadi ya bayyana cewa, Amurka da HKI sune manya-manyan masu haddasa rashin tsaro a kasashen yankin Asiya ta yamma.
Jami’in diblomasiyyar ya bayyana cewa Amurka da HKI ne suke haddasa halin da ake ciki a Gaza, na yuwan da kuma kisan kiyashi a Gaza da kashesu hanyar daukar yunwa a matsayin makami. Hakama tashe-tashen hankula a kasashen Yemen, Siriya da kuam Lebanon.
Banda haka wadanan kasashen biyu ne suka haddasa yakin kwanaki 12 a kan kasar Iran a cikin watan Yunin da ya gabata.
Yace wadan nan kasashe ne suke haddasa matsaloli da ruda gidajen falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan, Yace HKI ta kori miliyoyin Falasdinawa daga gidajensu ta maidasu yan gudun hijira a kasashe makobta da kuma da sauran kasashen duniya,
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu
Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A yayin ganawarsa da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a jiya Laraba a birnin Qom mai alfarma Ayatullah Makarem Shirazi ya yi ishara da yakin tunani da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka yi kan Iran yana mai cewa: Wadannan makiya sun yi zaton za su haifar da rudani ta hanyar kai wa Iran hari, amma alhamdulillahi ba wai kawai hakan ya faru ba, amma hadin kan al’ummar kasar ya kara karfafa. A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana wasu manyan matsaloli guda uku da al’umma ke fuskanta: hauhawar farashin kayayyaki, gidajen haya, da samar da ayyukan yi ga matasa. Ya ce, “Dole ne a yi kokarin magance wadannan matsalolin, kuma in Allah idan ya yarda za a yi nasara.”