Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar
Published: 24th, July 2025 GMT
A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin jirgin saman fasinja da ya auku a kasar, wanda ya haddasa rasa rayuka da dama.
Kafar dillancin labarai ta “The Russia Today”, ta hakaito kwamitin binciken hadarin na cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin saman mai lamba An-24 da ya yi hadari a yau Alhamis a yankin Amur na kasar Rasha sun rasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar “Human Right Watch” Ta Yi Kira Da A Saki Tsohon Shugaban Kasar Nijar Muammad Bazoum
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta yi kira ga gwamnatin sojan jamhuriyar Nijar da ta saki tsohon shugaban kasar Muhamad Bazum, wanda ake tsare da shi tun lokacin juyin mulkin watan Yuli na 2023.
Kungiyar ta kuma ce, ci gaba da tsare Muhammad Bazum da ake yi ba tare da yi masa shari’a ba, ya sabawa doka da kuma take dokokin kasa da kasa na sharia.
Bayan juyin mulkin na 2023, shugabannin soja sun yi alkawalin gabatar da Bazum a gaban kotu domin yi masa shari’a bisa zargin cin amanar aksa.
A 2024, kotun musamman da aka kafa ta cirewa tsohon shugaban kasar rigar kariya, da hakan ya zama tamkar share fage domin yi masa sharia,sai dai har yanzu hakna ba ta faru ba.
Lauyoyin da suke bai wa Bazzoum kariya sun nemi taimakon kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada MDD da kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ( ECOWAS).
Dukkanin kungiyoyin na kasa da kasa da kuma na yammacin Afirka sun sha yin kira da a saki Bazzum ba tare da wani sharadi ba.