HausaTv:
2025-09-17@22:08:09 GMT

Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza

Published: 24th, July 2025 GMT

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin.

Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.

” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar.

 A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yankin yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako.

 An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar Gaza, da hana shigar da madarar jarirai da dukkanin kayan agaji.

Bugu da kari ofishin gwamnatin Gaza din ya kuma kara da cewa; Da akwai wasu kafofi da suke watsa jita-jita da karairayi akan shigar da kayan abinci zuwa cikin yankin na Gaza, yana mai cewa babu kamshin gaskiya a ciki.

Haka nan kuma ya yi kira ga mutanen Gaza da kar su yarda da wadannan irin karairayin, wacce manufarta rufe hakikanin laifukan da ‘yan sahayoniya suke aikatawa.

Har ila yau, ofishin na gwamnatin Gaza ya bukaci ganin dukkanin kasashen duniya ba tare da togiya ba, da su yunkura domin karya killace Gaza da aka yi, da kuma bude kan iyakoki saboda a shigar da madarar da kananan yara za su sha, da kuma abincin da mutane fiye da miliyan 2.4 za su ci.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq.

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano

Sun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi.

A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Saudiyya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da cikakken goyon baya wajen ganin an saki waɗanda aka kama.

Bincike ya gano cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, suka ƙwayoyin a jakunkuna waɗanda aka kama.

Mutanen uku da aka kama, sun tashi a jirgin Ethiopian Airlines a ranar 6 ga watan Agusta don yin Umara, amma aka kama su a Saudiyya.

Binciken NDLEA ya kai ga kama wani shugaban masu safarar miyagun ƙwayoyin, mai shekaru 55, Mohammed Ali Abubakar (wanda aka fi sani da Bello Karama).

Hakazalika, hukumar ta kama wasu mutum uku ciki har da ma’aikatan jirgi.

Mutanen da aka kama su ne suka shirya safarar ƙwayoyin a jakunkunan mutane da aka kama a Saudiyya.

NDLEA ta gabatar da shaidun da suka tabbatar da cewa mutanen da aka kama a Saudiyya ba su da laifi.

Sakamakon haka, hukumomin Saudiyya suka sako ɗaya daga cikinsu a ranar 14 ga watan Satumba, sannan suka sako sauran biyun a ranar 15 ga watan Satumba.

Babafemi, ya ce Marwa ya gode wa hukumomin Saudiyya saboda mutunta yarjejeniyar haɗin kai tsakaninsu da Najeriya.

Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Shari’a, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Mai Bai Wa Shugaba Shawara Kan Harkar Tsaro, saboda gudummuwarsu.

Ya ƙara da cewa wannan lamari ya nuna cewa Najeriya tana tsayawa wajen kare ‘yan ƙasarta a ƙasashen waje kuma ba za ta yadda wani ɗan Najeriya ya sha wahala saboda laifin da bai aikata ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  •  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza.
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza
  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000