Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
Published: 25th, July 2025 GMT
Da yammacin yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 25, tare da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen a nan birnin Beijing.
A yayin taron, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da EU suna da moriya iri daya wadda babu rikici a cikinta.
Li Qiang ya ce, kamata ya yi bangarorin biyu su kara yin hadin gwiwa, da tabbatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da gudanar da ciniki cikin ‘yanci, don tabbatar da adalci da odar tattalin arziki, da cinikayya a duniya baki daya.
A nasu bangare, Antonio Costa da Ursula von der Leyen, sun bayyana cewa, bangaren EU yana fatan yin kokari wajen zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsa da kasar Sin a dogon lokaci, da kara yaukaka mu’amala da juna, da fahimtar juna, da mai da hankali ga batutuwan da suke mayar da hankali a kansu, da sa kaimi ga hadin gwiwarsu a fannonin cinikayya da zuba jari, da kokari tare wajen tinkarar kalubalen duniya, da nuna goyon baya ga hukumar WTO, ta yadda za ta taka muhimmiyar rawar raya dangantakar tattalin arziki, da cinikayya a tsakanin sassan kasa da kasa, da kuma tabbatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya bayyana cewa Gwamnonin APC sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar gwamnati da ke Abuja.
Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana ganawar da cewa “tattaunawa ce mai muhimmanci da Shugaban Ƙasa domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma inganta ikon ta na samar da nagartaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya”.
Ya ƙara da cewa, a matsayin su na gwamnoni, sun haɗu da Shugaban Ƙasa domin daidaita matsayin al’amuran jam’iyya da kuma muhimman abubuwan da suka shafi shugabanci.
Da aka tambaye shi ko ana sa ran yanke wasu manyan shawarwari ko takaddama a yayin Taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC da za a gudanar a gobe Alhamis, gwamnan ya ce, “Ba za mu iya cewa komai yanzu ba har sai mun isa wurin taron gobe.”
Ana sa ran taron na gobe Alhamis 24 ga watan Yulin 2025 zai tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jam’iyyar da kuma tsara hanyoyin ci gaba da haɗin kai da inganci a harkokin ta.
Bello Wakili